Ka Koya Daga Kalmar Allah
Me ya Sa Za Ka Koya Daga Wurin Allah?
Wannan talifin ya ta da tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin su kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.
1. Me ya sa za ka koya daga wurin Allah?
Allah yana da bishara mai daɗi ga mutane. Ya gaya mana ita a cikin Littafi Mai Tsarki. Littafi Mai Tsarki yana kama ne da wasiƙa da Uba daga sama ya aiko mana.—Karanta Irmiya 29:11.
2. Mece ce bisharar?
’Yan Adam suna bukatar gwamnati mai kyau. Babu wani ɗan Adam da ke mulki da ya taɓa cire wa ’yan Adam mugunta, rashin adalci, cuta, ko mutuwa. Amma akwai albishir. Allah zai yi wa ’yan Adam tanadin gwamnati mai kyau wanda zai ’yanta mutane daga dukan abubuwan da suke jawo wahala.—Karanta Daniyel 2:44.
3. Me ya sa yake da muhimmanci mu koya daga Allah?
Ba da daɗewa ba, Allah zai halaka mutanen da suke haddasa shan wahala a duniya. A yanzu, yana koya wa miliyoyin mutane masu tawali’u su more rayuwa mai kyau, wadda take bisa ƙauna. Daga Kalmar Allah, mutane suna koyon yadda za su jimre da matsaloli na rayuwa, yadda za su samu farin ciki na ainihi, da kuma yadda za su faranta wa Allah rai.—Karanta Zafaniya 2:3.
4. Wane ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki?
Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ƙananan littattafai guda 66. Maza 40 ne suka rubuta su. Musa ne ya rubuta littattafai guda biyar na farko wajen shekaru 3,500 da suka shige. Manzo Yohanna ne ya rubuta littafi na ƙarshe fiye da shekaru 1,900 da suka shige. Amma marubutan Littafi Mai Tsarki sun rubuta abin da Allah ya ce ne, ba abin da ke zuciyarsu ba. Saboda haka, Allah ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki.—Karanta 2 Timotawus 3:16; 2 Bitrus 1:21.
Mun san cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce domin ya bayyana abubuwan da za su faru a nan gaba dalla-dalla, babu kuskure. Ba mutumin da zai iya yin haka. (Ishaya 46:9, 10) Kuma Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana halayen Allah. Yana da ikon kyautata rayuwar mutane. Waɗannan gaskiyan sun sa miliyoyin mutane sun gaskata cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ce.—Karanta Joshua 23:14; 1 Tasalonikawa 2:13.
5. Ta yaya za ka fahimci Littafi Mai Tsarki?
Yesu ya zama sannanen malamin Kalmar Allah. Ko da yake yawancin mutanen da ya tattauna da su sun san Nassosi, amma suna bukatar taimako don su fahimce shi. Don ya taimake su, Yesu ya ambata nassin Littafi Mai Tsarki ɗaya bayan ɗaya kuma ya bayyana su don su “fahimci littattafai.” Wannan talifin, “Ka Koya Daga Kalmar Allah,” zai yi amfani da irin wannan salon don ya taimake ka.—Luka 24:27, 45.
Koyon manufar rayuwa daga wurin Allah abu ne mai ban al’ajabi. Amma wasu mutane ba za su yi farin ciki ba cewa kana karanta Littafi Mai Tsarki. Kada ka yi sanyin gwiwa. Domin ka kasance da begen more rayuwa har abada kana bukatar ka san Allah.—Karanta Matta 5:10-12; Yohanna 17:3.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 2 na Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? shaidun Jehobah ne suka wallafa shi.