Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • rq darasi na 11 pp. 22-23
  • Imani da Al’adu da ke Ɓata ma Allah Rai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Imani da Al’adu da ke Ɓata ma Allah Rai
  • Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yanke Shawarar Bauta wa Allah
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Me Ya Sa Ba Ku Yin Bikin Ista?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Dukan Bukukuwa Ne Allah Yake So?
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Bukukuwan da Allah ba ya So
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
Dubi Ƙari
Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
rq darasi na 11 pp. 22-23

Darasi na 11

Imani da Al’adu da ke Ɓata ma Allah Rai

Waɗanne imani da al’adu ne basu da kyau? (1)

Ya kamata Kiristoci su gaskata cewa Allah Dunƙulin-Alloli-Uku ne? (2)

Don me Kiristoci basu yin bikin Kirsimati, Easter, ko kuwa bikin ranar haihuwa? (3, 4)

Shin matattu suna ɓarna ga masu-rai? (5) Anya Yesu ya mutu bisa giciye? (6) Ina muhimmancin faranta ma Allah rai? (7)

1. Ba dukan imani da al’adu ne ba kyau ba. Amma Allah baya amince da su idan daga addinin ƙarya ne ko kuwa suna gāba da koyaswan Littafi Mai-Tsarki.​—Matta 15:6.

2. Dunƙulin-Alloli-Uku: Anya Jehovah Dunƙulin-Alloli-Uku ne​—mutane uku cikin Allah ɗaya? A’a! Jehovah, Uba, shine “Allah makaɗaici mai-gaskiya.” (Yohanna 17:3; Markus 12:29) Yesu shine Ɗansa na fari, kuma yana biyyaya ga Allah. (1 Korinthiyawa 11:3) Uban ya fi Ɗan girma. (Yohanna 14:28) Ruhu mai-tsarki ba mutum ba ne; ikon aikin Allah ne.​—Farawa 1:2; Ayukan Manzanni 2:18.

3. Kirsimati da Easter: Ba a haifi Yesu a 25 ga Disamba ba. An haife shi tsakanin 1 ga Oktoba, a lokacinda makiyaya ke barin garken a waje da dare. (Luka 2:​8-12) Yesu bai taba umurce Kiristoci su yi bukin haihuwarsa ba. Maimako fa, ya umurce almajiransa su yi bukin, ko kuwa tuna da, mutuwarsa. (Luka 22:​19, 20) Kirsimati da al’adunta sun fito ne daga addinan ƙarya na dā. Haka ma ya ke da al’adun Easter, irinsu amfani da ƙwai da zomaye. Kiristoci na farko basu taba yin bukin Kirsimati ko Easter ba, ba kuwa ma Kiristoci na yau.

4. Ranakun Haihuwa: Bukukkuwan ranar haifuwa biyu kaɗai da aka ambata cikin Littafi Mai-Tsarki ba masu bauta ma Jehovah ne suka yi ba. (Farawa 40:​20-22; Markus 6:​21, 22, 24-27) Kiristoci na farko basu yi bukin ranakun haihuwa ba. An samo al’adun yin bukin ranakun haihuwa daga addinan ƙarya na dā ne. Kiristoci na gaske suna bada kyautai kuma holewa tare a wasu lokutta a cikin shekara.

5. Tsoron Mattatu: Mattatu ba su iya yin kome ko kuwa ji kome ba. Ba mua iya taimake su, kuma ba zasu iya yi mana ɓarna ba. (Zabura 146:4; Mai-Wa’azi 9:​5, 10) Kurwa na mutuwa; ba shi rayuwa bayan mutuwa. (Ezekiel 18:4) Amma a wasu lokutta miyagun mala’iku, waɗanda ake kira aljannu, suna lamunin wai ruhun mattatu ne. Duk al’ada da ke tsoro ko kuwa bauta ma mattatu ba shi da kyau.​—Ishaya 8:19.

6. Giciye: Yesu bai mutu bisa giciye ba. Ya mutu akan miƙaƙƙen itace, ko gungume. Kalmar Hellenanci da aka juya “giciye” cikin Littafi Mai-Tsarki dayawa yana nufin babban katako ɗaya ne. Alamar giciye ya fito ne daga addinan ƙarya na dā. Kiristoci na farko ba su yi amfani da giciye ko kuwa bauta masa ba. Saboda haka fa, kana jin daidai ne a yi amfani da giciye cikin sujada?​—Kubawar Shari’a 7:26; 1 Korinthiyawa 10:14.

7. Zai iya zama da wuya yasad da wasu imani da al’adun nan. Mai-yiwuwa dangogi da abokai zasu yi ƙoƙarin rinjaye ka ka sake imaninka. Amma faranta ma Allah rai ya fi muhimmanci da faranta ma mutane.​—Misalai 29:25; Matta 10:​36, 37.

[Hoto a shafi na 22]

Allah ba Dunƙulin-Alloli-Uku ba ne

[Hoto a shafi na 23]

Kirsimati da Easter sun fito daga addinan ƙarya na dā

[Hoto a shafi na 23]

Babu wata dalilin bauta ko kuwa jin tsoron matattu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba