Darasi na 13
Ina Yadda Zaka Sami Addini na Gaskiya?
Dukan addinai ne ke gamsad da Allah, ko kuwa ɗaya ne kaɗai? (1)
Me yasa da akwai addinai dayawa da ke da’awar zaman Kirista? (2)
Ina yadda zaka sakankance Kiristoci na gaskiya? (3-7)
1. Yesu ya soma addinin Kirista na gaskiya ɗaya. Saboda haka a yau tilas ne a samu hukuma, ko kuwa rukunin, masu-sujadar Jehovah Allah ɗaya. (Yohanna 4:23, 24; Afisawa 4:4, 5) Littafi Mai-Tsarki ya koyas da cewa kalilan mutane ne ke bisa matsatsiyar hanyar zuwa rai.—Matta 7:13, 14.
2. Littafi Mai-Tsarki ya annabta cewa bayan mutuwar manzannin, koyaswan ƙarya da ayukan da ba na Kirista ba zasu shigo cikin ikklisiyar Kirista da sannu sannu. Mutane zasu jawo masu-bi garin binsu maimakon Kristi. (Matta 7:15, 21-23; Ayukan Manzanni 20:29, 30) Abinda yasa kenan muna ganin addinai dayawa da suke da’awar zaman Kirista. Ina yadda zamu sakankance Kiristoci na gaskiya?
3. Alamar Kiristoci na gaskiya na musamman shine cewa tilas ne su kasance da ƙauna na gaskiya ga junansu. (Yohanna 13:34, 35) Ba a koyad da su cewa sun fi mutane na wasu kabila ko fatan jiki ba. Ba kuwa an koyad da su su ƙi mutane na wasu ƙasashe ba. (Ayukan Manzanni 10:34, 35) Saboda haka basu rabo cikin yaƙoƙi. Kiristoci na gaskiya suna sha’ani da juna kamar yan’uwa maza da mata.—1 Yohanna 4:20, 21.
4. Wata alamar addini na gaskiya ita ce wai mambobinta suna da ladabi mai-zurfi ga Littafi Mai-Tsarki. Suna ɗaukansa kamar Kalmar Allah kuma gaskata da abinda ya ke faɗi. (Yohanna 17:17; 2 Timothawus 3:16, 17) Suna ɗaukan Kalmar Allah kamar abinda ya fi muhimmanci da ra’ayoyi ko kuwa al’adun yan-Adam. (Matta 15:1-3, 7-9) Suna ƙoƙarin zama cikin jituwa da Littafi Mai-Tsarki cikin rayuwarsu na kullayaumi. Basu yin wa’azin wani abu dabam sa’annan kuma aika wani dabam ba.—Titus 1:15, 16.
5. Addini na gaskiya ma tilas ne ya daraja sunan Allah. (Matta 6:9) Yesu ya sanas da sunan Allah, Jehovah, ga wasu. Tilas ne Kiristoci na gaskiya su aika bai ɗaya. (Yohanna 17:6, 26; Romawa 10:13, 14) Waɗanne mutane ne cikin yankinka da suke yin magana da wasu game da sunan Allah?
6. Tilas ne Kiristoci na gaskiya su yi wa’azi game da Mulkin Allah. Yesu ya yi haka. Kullum yana magana game da Mulkin. (Luka 8:1) Ya umurce almajiransa su yi wa’azin wannan saƙon a dukan duniya. (Matta 24:14; 28:19, 20) Kiristoci na gaskiya sun gaskata cewa sai Mulkin Allah ne zai kawo salama da kwanciyar rai ga wannan duniya.—Zabura 146:3-5.
7. Tilas ne almajiran Yesu su zama ba na wannan miyagun duniya ba. (Yohanna 17:16) Basu shaƙuwa cikin harƙoƙin siyasa da kuma jayayya na zaman jama’a. Suna guje ma halaye, ayuka, da kuma hali mai-ɓarna da ke ko’ina cikin duniya. (Yaƙub 1:27; 4:4) Zaka iya sakankance wani rukunin addini cikin yankinka da ke da alamun Kiristanci na gaskiyar nan?
[Hotuna a shafi na 26 da 27]
Kiristoci na gaskiya suna ƙaunar juna, nuna ladabi ga Littafi Mai-Tsarki, kuma suna wa’azi game da Mulkin Allah