Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • rq darasi na 14 pp. 28-29
  • Yadda Ake Shirya Shaidun Jehovah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Ake Shirya Shaidun Jehovah
  • Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Allah Yake da Ƙungiya?
    Albishiri Daga Allah!
  • Me Ya Sa Allah Yake da Ƙungiya?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ƙungiyarsu ta Dukan Duniya da Kuma Aikinsu
    Shaidun Jehovah Su Wanene ne Su
  • Bari Ikilisiya Ta Ingantu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Dubi Ƙari
Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
rq darasi na 14 pp. 28-29

Darasi na 14

Yadda Ake Shirya Shaidun Jehovah

Yaushe ne Shaidun Jehovah na zamani suka soma? (1)

Ina yadda ake tafiyadda taruwai na Shaidun Jehovah? (2)

Ina yadda ake biyan bukatun? (3)

Waɗannene suke jagabanci cikin kowane ikklisiya? (4)

Waɗanne manyan taruwai ne ake yi kowace shekara? (5)

Waɗanne aikace-aikace ne ake yi a hedkwatoci da kuma ofisoshin rassa nasu? (6)

1. Shaidun Jehovah na zamani sun soma cikin shekarun 1870 ne. A farko, ana kiransu Daliɓan Littafi Mai-Tsarki. Amma cikin 1931 sun talafa suna na Nassin nan Shaidun Jehovah. (Ishaya 43:10) Daga ƙaramin somawa ƙungiyar ta yi girma zuwa miliyoyin Shaidu, waɗanda sun taƙure cikin ­aikin wa’azi cikin ƙasashe sama da 230.

2. Yawancin ikklisiyai na Shaidun Jehovah suna da taruwai sau uku kowace mako. Ana gayyace ka ka hallarce su. (Ibraniyawa 10:​24, 25) Littafi Mai-Tsarki shine tushin abinda ake koyaswa. Ana soma kuma rufe taruwai nan da addu’a. Ana raira “waƙoƙi masu-ruhaniya” daga zuci a yawancin taruwai nan. (Afisawa 5:​18, 19) Ana hallarta kyauta, ba a kar­ɓan kuɗi.​—Matta 10:8.

3. Yawancin ikklisiyai suna riƙe taruwai a cikin Majami’ar Mulki. Waɗannan dai gidaje ne masu-sauƙi da Shaidu masu-bada kai suka gina. Ba zaka ga sifofi, giciye, ko kuwa abubuwa makamancin waɗannan cikin Majami’ar Mulkin ba. Ana biyan bukatan kuɗi ta wurin kyautai na son rai. Ga waɗanda suke son su bada kyautai fa, da akwai akwatin baye-baye.​—2 Korinthiyawa 9:7.

4. Cikin kowane ikklisiya, da akwai dattiɓai, ko kuwa masu-luraswa. Suna ja-gora cikin koyaswa cikin ikklisiyar. (1 Timothawus 3:​1-7; 5:17) Bayi masu-hidima suna taimake su. (1 Timothawus 3:​8-10, 12, 13) Ba a ɗaukaka waɗannan mazaje sama da saura cikin ikklisiyar ba. (2 Korinthiyawa 1:24) Ba a basu wasu lakabi na musamman. (Matta 23:​8-10) Basu ado dabam daga wasu. Ba kuwa ana biyansu sabili da aikinsu ba. Da son rai dattiɓan suna kula da bukatun ruhaniya na ikklisiyar. Suna iya tanadar da ta’aziya da jagabanci a lokuttan damuwa.​—Yaƙub 5:​14-16; 1 Bitrus 5:​2, 3.

5. Shaidun Jehovah ma suna riƙe manya ko kuwa taruwai na gunduma kowace shekara. A waɗannan lokutta akan haɗa ikklisiyai dayawa don ­tsarin koyaswa na musamman daga Littafi Mai-Tsarki. Baftismar sabobbin almajirai sashen tsarin kowace babba ko kuwa taron gunduma ne.​—Matta 3:​13-17; 28:​19, 20.

6. Hedkwatocin Shaidun Jehovah na duk duniya yana New York ne. Da akwai Hukumar Mulki, rukunin gogaggun dattiɓai waɗanda suke lura da ikklisiyai na dukan duniya. Da akwai ofisoshin rassa sama da 100 a kewaye da duniya. A waɗannan wurarre, waɗanda suka bada kansu suna buga kuma rarraba littattafai masu-tushi cikin Littafi Mai-Tsarki. Ana bada jagabanci ma game da yadda za a shirya aikin wa’azin. Don me ba zaka shirya ka ziyarci ofishin rassa da ke kusa da kai ba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba