Ƙungiyarsu ta Dukan Duniya da Kuma Aikinsu
AKWAI hanyoyi da yawa da ake amfani da su wajen ja-gorar aikin wa’azi a sama da ƙasashe 230 da ake yin sa. Hukumar Mulki da ke hedkwata a Brooklyn ta New York ne suke ja-gorar duka aiki da ake yi a duniya. Hukumar Mulkin suna aika wakilai kowace shekara zuwa jihohi dabam dabam na duniya su yi shawara tare da wakilan reshe na jihohin. A ofisoshin rassa, akwai Kwamiti na Reshe da mutanen da suke ciki sun kai uku ko bakwai da suke kula da aiki da ake yi a ƙasashe da ke ƙarƙashinsu. Wasu cikin rassa suna da maɗaba’a, wasu kuma suna da maɗaba’o’i masu gudu sosai. An raba ƙasa ko wuri da kowane reshe ke aiki zuwa gundumomi, kuma gundumomin an raba su zuwa da’irori. Kowace da’ira tana da misalin ikilisiyoyi 20. Mai kula da gunduma yana ziyarar da’irori a gundumansa ta wurin zagawa. Kowace da’ira tana yin taro sau biyu a shekara. Akwai mai kula da da’irar kuma, yana ziyarar kowace ikilisiya a da’irarsa sau biyu a shekara, yana taimaka wa Shaidun su tsara kuma su yi aikin wa’azi a yankin da aka ba wa ikilisiyar.
Majami’ar Mulki ta ikilisiyar ita ce cibiyar faɗin bisharar a yankinka. An ba kowace ikilisiya ƙananan yankuna da ke ƙarƙashinta tana aiki. An ba Shaidu waɗanda suke ƙoƙari su yi ziyara kuma yi magana da mutane a gidajensu waɗannan yankuna. Kowace ikilisiya da take da Shaidu daga kaɗan har zuwa 200, tana da dattiɓai da suke kula da ayyuka dabam dabam. Kowane mai shelar bishara yana da muhimmanci a ƙungiyar Shaidun Jehovah. Kowanne cikin Shaidun, ko yana hidima a hedkwata na duniya, a reshe, ko cikin ikilisiyoyi, yana aikin nan na gaya wa wasu game da Mulkin Allah.
Rahotanni na wannan ayyuka suna kai hedkwata na duniya, a rubuta kuma buga Yearbook na kowace shekara. Ana buga rahoto a cikin Hasumiyar Tsaro fitar 1 ga Janairu ta kowace shekara. Waɗannan littattafai biyu suna ba da rahoto dalla-dalla na abin da aka cim ma kowace shekara a wajen yin shaida ga Jehovah da Mulkinsa a ƙarƙashin Kristi Yesu. A shekarun bayan nan misalin Shaidu da mutane waɗanda suke da marmari 14,000,000 ne suka halarci Bikin Tunawa da mutuwar Yesu da ake yi shekara shekara. Shaidun Jehovah sun ba da fiye da sa’o’i 1,000,000,000 a shekara wajen shelar bishara, kuma fiye da sababbi 300,000 ne suka yi baftisma. Littattafai da suka ba da sun kai ɗarurruwan miliyoyi.