Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • jt pp. 22-24
  • Amfanin Gaske na Bisharar wa Yankinka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amfanin Gaske na Bisharar wa Yankinka
  • Shaidun Jehovah Su Wanene ne Su
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Ja-gorar Sawayenka Da Ƙa’idodin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Littafi Mai Tsarki Ya Haramta Auren Wani Kabila Ne?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Shaidun Jehovah Su Wanene ne Su
jt pp. 22-24

Amfanin Gaske na Bisharar wa Yankinka

A DUNIYA ta yau, sau da yawa muna jin ra’ayi da ake furtawa: “Ƙa’idodin Kiristanci ba sa amfani. Ba za su yi amfani ba a duniya mai girma ta yau.” Amma a rahoton da aka ba da na zance tsakanin shugaban Hindu Mohandas K. Gandhi da gwamnan Britaniya a Indiya dā, Lord Irwin, an furta ra’ayi da ke dabam. An ce wai Lord Irwin ya tambayi Gandhi abin da yake zato zai warware matsalolin da suke tsakanin Britaniya Babba da Indiya. Gandhi ya ɗauki Littafi Mai Tsarki ya buɗe sura ta biyar na Matta ya ce: “Lokacin da ƙasarku da tawa za mu bi koyarwa da Kristi ya yi a wannan Huɗuba Bisa Dutse, za mu warware matsaloli ba na ƙasashenmu kaɗai ba amma na duka duniya.”

Wannan huɗuba ce ta yi zance a kan neman ruhaniya da zama masu tawali’u, zaman lafiya, nuna juyayi, da ƙaunar adalci. Ya haramta ba kisa kaɗai ba amma har yin fushi da mutane, haramta ba zina kawai ba amma sha’awarta. Ya hana kisan aure da ke raba gidaje kuma ya sa yara su sha wahala. Ya gaya mana: ‘Mu so waɗanda ba sa son mu, mu taimaka wa matalauta, mu daina shar’anta mutane da rashin jinƙai, mu yi wa wasu yadda za mu so su yi da mu.’ Duk waɗannan shawara, idan an bi za su kawo amfani mai girma. Idan mutane da suke yin haka a yankinka suna ƙaruwa, yankinka zai daɗa yin kyau!

Shaidun Jehovah sun yi tasiri a wannan hanyar. Littafi Mai Tsarki ya koya musu su daraja aure. Suna koyar da yaransu a ƙa’idodi da suke daidai. An nanata muhimmancin iyali. Iyalai da suke da haɗin kai albarka ce ga yankinka, har da ƙasarka ga baki ɗaya. Tarihi ya cika da misalan masu mulkin duniya da suke faɗiwa yayin da gamin iyali ya raunana kuma lalata ta ƙaru. Yayin da mutane da iyalai da Shaidun Jehovah suke rinjaye su su bi ƙa’idodin Kirista suna ƙaruwa, tawaye, lalata, da yin laifi za su ragu a yankinka.

Babbar matsala da ke damun yankuna da al’ummai ita ce wariyar ƙabila. Akasin haka, manzo Bitrus ya ce: “Hakika na gane Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.” Bulus ya rubuta kuma: “Ba daman cewa da Bayahude ko Bahelene, ba kuwa bawa ko ɗa, ba na miji ko ta mata: gama dukanku cikin Kristi Yesu ɗaya ne.” (Ayukan Manzanni 10:34, 35; Galatiyawa 3:28) Shaidun Jehovah sun yarda da wannan. Dukan ƙabilu da launin fata suna zama suna aiki tare a hedkwatarsu na duniya, a rassansu, da kuma a ikilisiyoyi.

A cikin Afirka wasu ƙabilu ba sa zama tare babu jayayya. Amma a taron Shaidun Jehovah da aka yi a wurin, mutane da yawa daga ƙabilu dabam dabam suka ci abinci tare, suka kwana tare, suka kuma yi bauta tare cikin haɗin kai da zumunci. Ma’aikatan gwamnati suna mamaki yayin da suka ga wannan. An yi maganar sakamakon wannan haɗin kai na gaskiya na Kiristanci a Amsterdam News na New York a ranar 2 ga Agusta, 1958. Don an lura da taro na dukan ƙasashe da aka ambata a dā inda Shaidun rubu’i miliyan suka taru a Birnin New York ne ya sa suka yi wannan maganar.

“Ko’ina baƙaƙe, turawa da mutanen Gabas, masu matsayi dabam dabam a rayuwa daga dukan ɓangarorin duniya suna cuɗanya da farin ciki . . . Shaidu da suke bauta a ƙasashe 120 sun zauna tare kuma sun yi bauta tare cikin salama, suna nuna wa ’yan Amirka yadda za a yi hakan da sauƙi . . . Taron misali mai kyau ne da ke nuna yadda mutane za su iya aiki kuma su zauna tare.”

Mutane da yawa suna iya ce ƙa’idodi na Kiristanci ba za su yi amfani ba ga duniya na zamani. Amma, menene ya yi amfani ko kuma zai amfana? Ƙa’idodi na Kirista zai zama abu mai aikawa sosai idan ka yi amfani da su a yankinka yanzu, kuma za su zama tushe na haɗa dukan ‘al’ummai, ƙabilu, da mutane’ na dukan duniya a ƙarƙashin Mulkin Allah bisa ’yan Adam.—Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10.

[Bayanin da ke shafi na 23]

Dukan ƙabilu da launin fata suna aiki tare

[Bayanin da ke shafi na 24]

Kiristanci tana da amfani. Menene kuma ya yi amfani?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba