Hanyoyi da Suke Amfani da Shi a Yaɗa Bisharar
AN UMURCI Kiristoci su “almajirantar da dukan al’ummai,” amma wannan ba ya nufin za su matsa wa mutane ko kuma juya su da dole. Umurnin Yesu shi ne a “yi shelar bishara ga matalauta,” a “warkarda masu-karyayen zuciya,” a “yi wa dukan masu-makoki ta’aziyya.” (Matta 28:19; Ishaya 61:1, 2; Luka 4:18, 19) Shaidun Jehovah suna yin haka ta yin shelar bisharar daga Littafi Mai Tsarki. Kamar annabi Ezekiel na dā, Shaidun Jehovah a yau suna ƙoƙari su sami waɗanda suke “ajiyar zuci, suna kuwa kuka saboda dukan ƙazanta da a ke yi.”—Ezekiel 9:4.
Hanya da aka fi sani da suke amfani da ita wajen neman waɗanda suke baƙin ciki don yanayin yanzu ita ce ta bi daga gida zuwa gida. Saboda haka suna yin ƙoƙari sosai su isa wurin mutane, yadda Yesu ya yi lokacin da “ya yi ta yawo a cikin birane da ƙauyuka, yana wa’azi yana kawo bishara ta mulkin Allah.” Almajiransa na farko ma sun yi haka. (Luka 8:1; 9:1-6; 10:1-9) A yau, idan ya yiwu, Shaidun Jehovah suna ƙoƙari su je kowane gida sau da yawa a shekara, suna yin zance da masu gidan cikin mintoci kaɗan a kan abubuwa da suke faruwa a yankinsu, ko na duniya da zai ta da marmarinsu ko game da damuwarsu. Za a karanta nassi ɗaya ko biyu, idan mai gidan ya nuna marmari, Mashaidin zai iya shiryawa ya sake dawowa a lokacin da ya fi kyau su ci gaba da zancensu. Akwai Littafi Mai Tsarki da littattafai da suke yin bayani a kan Littafi Mai Tsarki, idan mai gidan yana so ana iya yin nazarin Littafi Mai Tsarki na gida kyauta da shi. Ana tafiyar da waɗannan miliyoyin nazarori masu taimako na Littafi Mai Tsarki kullum a dukan duniya da mutane ɗaɗɗaya da kuma iyalai.
Wata hanya da ake amfani da ita a gaya wa wasu “bishara ta mulkin” ita ce ta wurin taro da ake yi a Majami’un Mulki. Shaidun suna yin taro a wurin kowane mako. Ɗaya cikin taron shi ne jawabi ga jama’a a kan darasi na kwanan nan, bayan haka sai a yi nazarin wani darasi na Littafi Mai Tsarki ko kuma annabci, suna amfani da jaridar Hasumiyar Tsaro. Wani taro shi ne makaranta ta koya wa Shaidu su zama masu shelar bisharar da kyau, bayan haka sai sashen tattauna aikin wa’azi a yankin. Kuma kowane mako Shaidu suna taruwa a gidaje a ƙananan rukuni don nazarin Littafi Mai Tsarki.
Ko waye yana iya halartar waɗannan taron. Ba a biyan kuɗi. Irin waɗannan taron suna da amfani ga duka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya kamata mu lura yadda kowanne cikinmu zai fi mu tada juna zuwa ƙauna da ayyuka masu kyau, kada mu fasa taronmu, yadda wasu suke yi, amma mu ƙarfafa juna, balle fa domin kuna ganin Ranan tana kusatowa.” Nazari na kai da yin bincike suna da muhimmanci, amma haɗuwa da wasu yana motsawa: “Ƙarfe ya kan wasa ƙarfe, hakanan kuma mutum ya kan wasa ilimin abokinsa.”—Ibraniyawa 10:24, 25; Misalai 27:17, The New Englishi Bible.
Shaidun suna amfani da zarafi da suka samu da kyau wajen yin magana game da bishara yayin da sun sadu da mutane a rayuwarsu na yau da kullum. Zai iya zama ɗan magana da maƙwabci ko da abokin tafiya a mota ko a jirgin sama, dogon zance da aboki ko dangi, ko kuma tattaunawa da abokin aiki lokacin cin abincin rana. Yawan wa’azi da Yesu ya yi lokacin da yake duniya irin wannan ne—da yake tafiya a bakin teku, lokacin da yake zaune a kan dutse, da yake cin abinci a gidan wani, da ya je bikin aure, ko kuma yana tafiya a kwalekwalen kamun kifi a Tekun Galili. Ya koyar a majami’u da kuma a haikali a Urushalima. Duk inda yake, yana samun zarafin yin magana game da Mulkin Allah. Shaidun Jehovah suna ƙoƙari su bi sawunsa a wannan ma.—1 Bitrus 2:21.
YIN WA’AZI DA MISALI
Kowanne cikin hanyoyin nan na gaya maka bishara ba zai zama da muhimmanci ba a gare ka idan mai gaya maka ba ya amfani da abin da yake koyarwa shi kansa. Munafunci ne idan muna faɗin abu dabam kuma muna yin wani abu dabam, munafunci na addini ya juya miliyoyi daga bin Littafi Mai Tsarki. Bai kamata a ɗaura wa Littafi Mai Tsarki laifi haka ba. Marubuta da Farisawa suna da Nassosin Ibrananci, amma Yesu ya zarge su ya ce musu munafikai. Ya yi maganar karatu da suke yi daga Dokar Musa, ya ce ga almajiransa: “Dukan abu fa iyakar abin da suka umurce ku, sai ku yi, ku kiyaye kuma: amma kada ku aika bisa nasu ayyuka; gama su kan faɗi, ba su kuwa aikawa.” (Matta 23:3) Rayuwa ta Kirista da take da misali mai kyau ta fi huɗubantar da mutane fiye da sa’o’i na yin wa’azi. An yi wa mata Kirista da mazansu da ba masu bi ba wannan shawara: “Su rinjayu banda magana saboda halayen matansu; suna lura da halayenku masu-tsabta.”—1 Bitrus 3:1, 2.
Saboda haka, Shaidun Jehovah suna ƙoƙari su gaya wa wasu bishara: ta wurin zama abin koyi a halayen Kirista da suke gaya wa wasu. Suna ƙoƙari su ‘yi iyakar abin da suke so mutane su yi musu.’ (Matta 7:12) Suna ƙoƙari su yi haka ga dukan mutane, ba ga Shaidu ’yan’uwansu, abokane, maƙwabta, ko dangogi kawai ba. Tun da yake su ajizai ne, ba sa yin nasara koyaushe. Amma muradin zuciyarsu ne su yi kirki ga dukan mutane ba kawai a gaya musu bisharar Mulki ba amma kuma a taimake su idan bukata ta kama.—Yaƙub 2:14-17.
[Hoto a shafi na 19]
Hawaii
[Hoto a shafi na 19]
Venezuela
[Hoto a shafi na 19]
Yugoslavia
[Hotona a shafi na 20]
Majami’un Mulki, da suke da kyau, wuraren tattauna Littafi Mai Tsarki ne
[Hotona a shafi na 21]
A ta su rayuwar iyali, haɗe da mutane da suke saduwa da su, Shaidun da gaske suna ƙoƙari su yi abubuwa da suke faɗa