Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 4/1 pp. 7-8
  • Su Waye Ne Suke Wa’azin Bishara?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Su Waye Ne Suke Wa’azin Bishara?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Ku Tafi . . . , Ku Almajirtar da Dukan Al’ummai’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Su Wane ne Suke Wa’azin Labari Mai Dadi?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Hanyoyi da Suke Amfani da Shi a Yaɗa Bisharar
    Shaidun Jehovah Su Wanene ne Su
  • Dukan Kiristoci Na Gaskiya Masu Wa’azin Bishara Ne
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 4/1 pp. 7-8

Su Waye Ne Suke Wa’azin Bishara?

“ . . . za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya.”—MATTA 24:14.

SHAIDUN Jehobah ne suke yin wa’azin bishara a dukan duniya. Suna yin hakan a hanyoyi dabam-dabam. Hanya ɗaya ita ce  . . .

Ta Maganar Baki. Kamar Yesu da almajiransa, Shaidun Jehobah suna kai wa mutane bishara. (Luka 8:1; 10:1) Ba sa sa rai cewa mutane za su zo wurinsu. Yin wa’azi ga mutane game da Mulkin Allah wani abu ne da dukan Shaidu fiye da miliyan bakwai suke yi. Suna yin wa’azi daga gida zuwa gida, a kan hanya, ta hanyar tarho, da wasu hanyoyi dabam-dabam. A shekarar da ta shige, Shaidu sun yi amfani da awoyi fiye da biliyan ɗaya da rabi a wannan aikin.

Suna koya wa mutane game da Mulkin Allah da kuma ‘dukan iyakar abin da Yesu ya umurta.’ (Matta 28:20) Suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki na gida kyauta fiye da miliyan takwas a kai a kai.

Shaidu suna yin wa’azi a dukan duniya a ƙasashe 236. Suna yin wa’azi ga kowa. Suna yin wa’azi a birni da ƙauye, a kurmin Amazon da na Siberia, a hamadar Afirka da Duwatsun Himalaya. Ba a biyan su kuɗi domin wannan aikin, suna amfani ne da kuɗinsu da kuma lokacinsu, ƙaunar da suke yi wa Allah da kuma maƙwabtansu ne take motsa su. Suna kuma yin shelar bisharar ta hanyar  . . .

Littattafai. Ana buga wannan mujallar, wadda cikakken jigonta ita ce Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah, a harsuna 185 kuma ana rarraba fiye da miliyan 42 a kowace fitowa. Ana buga mujallar nan Awake!, wadda ita ma tana shelar Mulkin, a harsuna 83 kuma ana rarraba wajen miliyan 40 a kowace fitowa.

Akwai littattafai, mujallu, warƙoƙi, fayafayan CD/MP3, da DVD da suke bayyana koyarwar Littafi Mai Tsarki a harsuna 540. Shaidu sun buga kuma sun rarraba fiye da kofi biliyan 20 na waɗannan abubuwan a cikin shekaru goma da suka shige, hakan yana nufin cewa kowane mutum guda a duniya zai iya samun wajen guda uku na waɗannan abubuwan!

Shaidun Jehobah sun buga fassarar Littafi Mai Tsarki dabam-dabam ko kuma sun ba da aikin yin hakan ga wasu. A yanzu za a iya samun New World Translation of the Holy Scriptures, gabaki ɗayansa ko rabinsa wanda Shaidu ne suka fassara shi, suka buga shi kuma suka rarraba shi, a harsuna 96. An rarraba fiye da miliyan 166. Shaidu suna kuma yaɗa bisharar Mulkin . . .

A Taron Kirista. Taron da ake yi a kowane mako a Majami’un Mulki ba hidimar addini kawai ba ne; an tsara su ne don ilimantarwa. Ana ba da jawabai a kan batutuwa dabam-dabam daga cikin Littafi Mai Tsarki, ana kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki ta wajen yin amfani da Hasumiyar Tsaro da wasu littattafai. A waɗannan taron, Shaidu suna koyan yadda za su ƙara ƙwarewa a shelar bishara.

Shaidu suna nazarin abubuwa iri ɗaya a cikin ikilisiyoyi fiye da 107,000 a dukan duniya, kuma hakan yana ƙarfafa haɗin kansu. Kowa zai iya halartan waɗannan taron. Ba a yawo da tire don a karɓi kuɗi a taron sam. Hakika, dukan waɗannan abubuwan za su zama banza idan Shaidu suka ƙi aikata abin da suke yin wa’azinsa. Saboda haka, suna yin bisharar . . .

Ta Wurin Halayen Su. Suna ƙoƙartawa su kasance da hali mai kyau na Kirista, ta wajen bi da mutane a hanyar da za su so mutane su bi da su. (Matta 7:12) Ko da yake su ajizai ne kuma a wasu lokatai sukan kasa, suna son su nuna ƙauna ga dukan mutane ba kawai ta wajen yaɗa bishara ba amma ta wajen ba da taimako a duk lokacin da hakan ya yiwu.

Ba wai Shaidun Jehobah suna son su juya dukan duniya ta hanyar wa’azinsu ba ne. A maimakon haka, sa’ad da Jehobah ya gamsu da aikin, ƙarshen zai zo, kamar yadda Yesu ya annabta. Mene ne hakan yake nufi ga duniya da kuma mutanen da ke cikinta?

[Hoton da ke shafi na 7]

Shaidun Jehobah suna wa’azin bisharar a dukan duniya

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba