Darasi na 15
Taimaka Ma Wasu su Yi Nufin Allah
Me yasa zaka gaya ma wasu abinda ka ke koyawa? (1)
Da wa zaka iya rabon bishara? (2)
Wane sanadi ne halayenka zai kasance da shi bisa wasu? (2)
Yaushe ne zaka iya wa’azi tare da ikklisiyar? (3)
1. Yanzu fa, ka riga ka koya nagargarun abubuwa dayawa daga Littafi Mai-Tsarki. Wannan sanin ya kamata shi kai ga gina halaye ta Kirista. (Afisawa 4:22-24) Irin sanin muhimmin abu ne domin ka sami rai madawwami. (Yohanna 17:3) Amma dai, wasu ma suna bukatar bisharar don su ma su tsira. Tilas ne dukan Kiristoci na gaskiya su bada shaida ga wasu. Dokar Allah ce.—Romawa 10:10; 1 Korinthiyawa 9:16; 1 Timothawus 4:16.
2. Zaka iya soma ta yin rabon abubuwa masu-kyau da ka koya da waɗanda ke kusa da kai. Ka faɗe su ga iyalinka, abokai, abokan makaranta, da abokan aiki. Ka yi haka da tawali’u da kuma haƙuri. (2 Timothawus 2:24, 25) Kuma ka tuna cewa mutane sun fi lura da halayen mutum fiye da sauraran abinda ya ke faɗi. Saboda haka halayenka mai-kyau zai iya jawo wasu su saurare saƙon da ka faɗa masu.—Matta 5:16; 1 Bitrus 3:1, 2, 16.
3. Akwana a tashi, zaka inganta soma yin wa’azi tare da ikkilisiyar Shaidun Jehovah da ke yankinka. Wannan muhimmin mataki ne cikin girmanka. (Matta 24:14) Dubi farincikinsa idan ka iya taimake wani ya zama bawan Jehovah kuma samu madawwamin rai!—1 Tassalunikawa 2:19, 20.