BABI NA 21
Yesu Ya Bayyana ‘Hikima Daga Allah’
1-3. Yaya maƙwabtan Yesu na dā suka ɗauki koyarwarsa, kuma mene ne suka kasa ganewa game da shi?
MASU sauraron suka yi mamaki. Saurayin, Yesu yana tsaye a gabansu a majami’a yana koyarwa. Ba baƙo ba ne a gare su—ya yi girma a birninsu, kuma ya yi aikin sassaƙa na shekaru da yawa a tsakaninsu. Wataƙila wasu sun zauna a gidaje da Yesu ya taimaka aka gina, ko kuma sun yi aiki a gonarsu da karkiyar da shi ya sassaƙa da hannunsa.a Amma yanzu yaya za su bi koyarwar wannan masassaƙi a dā?
2 Yawancin waɗanda suke sauraro sun yi mamaki, suna tambaya: “Ina wannan mutum ya sami hikimar nan haka?” Amma sun kuma ce: “Wannan ba shi ne ɗan kafintan nan ba? Ba mamarsa ce sunanta Maryamu ba?” (Matiyu 13:54-58; Markus 6:1-3) Abin nadama, waɗanda suka taɓa zama maƙwabtan Yesu suka ce, ‘Wannan masassaƙin, mutum ne kawai kamar mu.’ Duk da hikima da take daga maganarsa, suka ƙi shi. Ba su sani ba cewa hikima da ya bayar ba tasa ba ce.
3 A ina Yesu ya sami wannan hikimar? Yesu ya ce, “Abubuwan da nake koyarwa ba nawa ba ne, amma na wanda ya aiko ni ne.” (Yohanna 7:16) Manzo Bulus ya yi bayani cewa Allah ya sa Yesu “ya zama mana hikima.” (1 Korintiyawa 1:30) Hikimar Jehobah aka bayyana ta wajen Ɗansa, Yesu. Hakika, gaskiya ne da Yesu ya ce: “Da ni da Ubana, ɗaya ne.” (Yohanna 10:30) Bari mu bincika wajaje uku da Yesu ya nuna ‘hikima daga Allah.’
Abin da Ya Koyar
4. (a) Mene ne jigon saƙon Yesu, kuma me ya sa wannan yake da muhimmanci ƙwarai? (b) Me ya sa shawarar Yesu koyaushe mai amfani ce kuma domin amfanin masu sauraronsa?
4 Da farko, ka yi la’akari da abin da Yesu ya koyar. Jigon saƙonsa shi ne “labari mai daɗi na Mulkin Allah.” (Luka 4:43) Wannan yana da muhimmanci ƙwarai domin aikin da Mulkin zai yi wajen kunita ikon mallaka na Jehobah kuma ya kawo albarka ta dindindin ga ’yan Adam. A koyarwarsa, Yesu kuma ya ba da shawara mai hikima domin rayuwa ta yau da kullum. Ya tabbatar da kansa cewa shi ne “Mai Ba da Shawara Mai Ban Mamaki” da aka annabta. (Ishaya 9:6) Hakika, me ya sa shawararsa ba za ta zama abin ban mamaki ba? Yana da ilimi ƙwarai na Kalmar Allah da kuma nufinsa, ya kuma fahimci ƙwarai yanayin mutane, da kuma ƙauna mai zurfi ga mutane. Saboda haka, shawararsa koyaushe mai amfani ce kuma domin amfanin masu sauraronsa. Yesu ya furta “magana mai ba da rai na har abada.” Hakika, idan aka bi shawararsa, tana kai wa zuwa ceto.—Yohanna 6:68.
5. Mene ne wasu batutuwa da Yesu ya taɓa a Huɗuba a kan Dutse?
5 Huɗuba a kan Dutse fitaccen misali ne na hikima marar kama da aka gani a cikin koyarwar Yesu. Huɗubarsa, da aka rubuta a Matiyu 5:3–7:27, wataƙila za ta ɗauki minti 20 ne kawai ya yi ta. Amma gargaɗinta ba ta da lokaci—tana da muhimmanci daidai kamar ranar da aka yi ta. Yesu ya taɓa batutuwa da yawa, har da yadda za a gyara dangantaka da wasu. (5:23-26, 38-42; 7:1-5, 12), yadda za a kasance da tsabta ta ɗabi’a (5:27-32), da kuma yadda za a yi rayuwa mai ma’ana (6:19-24; 7:24-27). Amma Yesu ya yi fiye da gaya wa masu sauraronsa tafarkin hikima; ya nuna musu ta wajen bayani, koyarwa, da kuma ba da tabbaci.
6-8. (a) Waɗanne dalilai ne masu kyau Yesu ya bayar domin guje wa alhini? (b) Mene ne ya nuna cewa shawarar Yesu ta nuna hikima daga sama?
6 Alal misali, ka lura da shawara ta hikima game da yadda za a bi da damuwa game da abin duniya, kamar yadda aka faɗa a Matiyu sura 6. “Kada ku damu da yadda za ku rayu game da abin da za ku ci ko abin da za ku sha, ko kuma yadda za ku sami riguna domin jikinku,” Yesu ya ba mu shawara. (Aya ta 25) Abinci da tufafi wajibi ne don rayuwa, kuma daidai ne a damu game da samun waɗannan. Amma Yesu ya gaya mana “kada ku damu” saboda waɗannan abubuwa.b Me ya sa?
7 Ka saurara yayin da Yesu ya yi bayani mai gamsarwa. Tun da Jehobah ya ba mu rai da kuma jiki, ba zai iya ya ba mu abinci ba ne da zai rayar da rai da kuma tufafi da zai rufe jiki? (Aya ta 25) Idan Allah yana bai wa tsuntsaye abinci kuma yana yi wa furanni tufafi kyawawa, yaya kuwa ba zai kula da mutane masu bauta masa ba! (Ayoyi 26, 28-30) Hakika, damuwa da yawa ba ta da amfani. Ba za ta ƙara rayuwarmu ba ko kaɗan.c (Aya ta 27) Ta yaya za mu guje wa alhini? Yesu ya ba da shawara: Ku ci gaba da bai wa bautar Allah waje na farko a rayuwarku. Waɗanda suka yi haka za su tabbata cewa dukan bukatunsu Ubansu na saman zai “ba” su. (Aya ta 33) A ƙarshe, Yesu ya bayar da shawara mai amfani ƙwarai—ku ɗauki kwana ɗaɗɗaya. Me ya sa za ku ƙara alhinin gobe a kan na yau? (Aya ta 34) Ƙari ga wannan, me ya sa za ka damu da abin da wataƙila ba zai faru ba ma? Amfani da irin wannan shawara zai kāre mu daga ciwon zuciya a cikin wannan duniya da ta cika da damuwa.
8 Hakika, shawarar da Yesu ya bayar tana da amfani a yau kamar yadda take sa’ad da ya ba da ita kusan shekaru 2,000 da suka shige. Wannan ba tabbaci ba ne na hikima daga sama? Shawara mai kyau ƙwarai daga wajen mutane masu ba da shawara tana shuɗewa kuma a maimaita ta ko kuma a sake ta. Amma duk da lokaci mai yawa da suka shige koyarwar Yesu ta kasance mai amfani. Amma wannan bai kamata ya ba mu mamaki ba, domin wannan Mai-shawara yana faɗin “kalmar Allah ne.”—Yohanna 3:34.
Yadda Yake Koyarwa
9. Mene ne wasu sojoji suka ce game da koyarwar Yesu, kuma me ya sa wannan ba zugugu ba ne kawai?
9 Waje na biyu da Yesu ya nuna hikima ta Allah yadda yake koyarwa ne. A wani lokaci, wasu sojoji da aka aike su su kama shi suka koma hannu goma, suna cewa: “Babu mutumin da ya taɓa magana kamar wannan mutum.” (Yohanna 7:45, 46) Wannan ba zugugu ba ne kawai. Dukan mutane da suka taɓa rayuwa, Yesu, wanda ya zo daga “sama,” yana da ilimi mai yawa da kuma fahimi daga inda ya yi magana. (Yohanna 8:23) Hakika ya koyar yadda babu wani mutumin da zai iya. Ka bincike hanyoyi biyu kawai na wannan Malami mai hikima.
‘Jama’a suka yi mamakin koyarwarsa’
10, 11. (a) Me ya sa za mu yi mamaki game da yin amfani da misalai na Yesu? (b) Mece ce almara, kuma waɗanne misalai ne suka nuna dalilin da ya sa almara ta Yesu tana da kyau wajen koyarwa?
10 Amfani da kyau da misalai. Aka gaya mana, “Yesu ya gaya wa taron mutanen duk waɗannan abubuwa da misalai. Ba ya gaya musu wani abu sai tare da misali.” (Matiyu 13:34) Babu abin da za mu yi sai dai mamaki ga irin wannan iyawarsa marar kama na koyar da gaskiya mai muhimmanci ta wajen amfani da abubuwa na yau da kullum. Manoma suna shuki, mata suna shirin gasa gurasa, yara suna wasa a kasuwa, masunta suna zuba taru, makiyaya suna neman tunkiya da ta ɓata—waɗannan abubuwa ne da masu sauraronsa suke gani sau da yawa. Sa’ad da aka haɗa abubuwa da aka saba da su, irin waɗannan gaskiya suna kahuwa da wuri da kuma zurfi cikin zuciya.—Matiyu 11:16-19; 13:3-8, 33, 47-50; 18:12-14.
11 Yesu sau da yawa ya yi amfani da almara, gajeren labari daga inda ake koyar gaskiya ta ɗabi’a da kuma ta ruhaniya. Tun da yake labarai sun fi sauƙi a tuna da su kuma a fahimce su fiye da abubuwa da ba a gani, almarar ta taimaka wajen adana koyarwar Yesu. A cikin almara da yawa, Yesu ya kwatanta Ubansa ƙwarai yadda ba za a iya manta da shi ba da wuri. Alal misali, waye ba zai fahimci darasin wannan almara na ɗa almubazzari—cewa wanda ya bauɗe idan ya nuna tuba ta gaskiya, Jehobah zai ji tausayinsa kuma ya sake karɓansa?—Luka 15:11-32.
12. (a) Ta wace hanya ce Yesu ya yi amfani da tambayoyi a koyarwarsa? (b) Ta yaya Yesu ya rufe bakin waɗanda suka tuhumi ikonsa?
12 Ƙwarewa wajen yin amfani da tambaya. Yesu ya yi amfani da tambayoyi domin ya sa masu sauraro su kai ga nasu kammala, su bincika abin da ke motsa su, da kuma shawarar da suka yanke. (Matiyu 12:24-30; 17:24-27; 22:41-46) Sa’ad da shugabannan addini suka yi tambaya ko yana da iko daga wurin Allah, Yesu ya amsa: “Izinin da Yohanna ya yi baftisma da shi, Allah ne ya ba shi, ko kuwa mutum?” Da tambayar ta ba su mamaki, suka ce tsakaninsu: “Idan muka ce, ‘Daga wurin Allah ne,’ zai ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba? Amma za mu iya cewa daga wurin mutum ne kuwa? Suna jin tsoron abin da mutane za su yi musu, domin dukan mutane sun ɗauka cewa Yohanna annabi ne.” A ƙarshe, suka amsa: “Ba mu sani ba.” (Markus 11:27-33; Matiyu 21:23-27) Da tambaya mai sauƙi, Yesu ya rufe bakinsu kuma ya bayyana mugunta da take zukatansu.
13-15. Ta yaya almara ta Basamariye maƙwabci ta nuna hikimar Yesu?
13 A wani lokaci Yesu yana haɗa hanyoyin ta wajen saka tambaya mai saka tunani a cikin misalinsa. Sa’ad da wani lauya Bayahude ya tambayi Yesu abin da ake bukata domin a samu rai na har abada, Yesu ya mai da shi ga Dokar Musa, wadda ta umurci ƙaunar Allah da kuma ta maƙwabci. Da yake so ya tabbatar da kansa mai adalci ne, mutumin ya yi tambaya: “Shin, wane ne maƙwabcina?” Yesu ya amsa ta wajen ba da wani labari. Wani Bayahude yana tafiya shi kaɗai sa’ad da ’yan fashi suka fāɗa masa, suka ƙyale shi rai a hannun Allah. Sai ga wasu Yahudawa biyu suna wucewa, na farkon firist ne sai kuma Balawi. Duk suka ƙyale shi. Amma sai wani Basamariye ya zo, tausayi ya motsa shi ya ɗaɗɗaure raunukan mutumin ya kai shi masauƙi inda zai warke. Da ya ƙare labarin, sai Yesu ya tambayi mai yi masa tambaya: “A ganinka wane ne a cikin mutanen nan uku ya nuna halin maƙwabci ga mutumin nan da ya faɗi a hannun ’yan fashi?” Mutumin dole ya ba da amsa: “Wannan da ya ji tausayinsa.”—Luka 10:25-37.
14 Ta yaya almarar ta nuna hikimar Yesu? A zamanin Yesu, Yahudawa suna amfani da kalmar nan “maƙwabci” ga waɗanda suke bin al’adunsu ne kawai—hakika ba ga Samariyawa ba. (Yohanna 4:9) Da Yesu ya faɗi labarin cewa Basamariye ne ya ji rauni kuma Bayahude ya yi taimako, da wannan zai juya ƙiyayyar? Yesu cikin hikima ya ƙaga labarin cewa Basamariye ne ya taimaki Bayahude. Ka lura kuma da tambayar da Yesu ya yi a ƙarshen labarin. Ya gyara fahimtarsu na kalmar nan “maƙwabci.” Lauya watau ya yi tambaya ne: ‘Waye ya kamata ya zama abin ƙaunata?’ Amma Yesu ya yi tambaya: “A ganinka wane ne a cikin mutanen nan uku ya nuna halin maƙwabci.” Yesu ya mai da hankali ba ga wanda aka yi wa kirki ba, wanda ya yi raunin, amma ga wanda ya yi kirki, Basamariye ɗin. Maƙwabci na gaskiya yana ɗaukan zarafi ya nuna ƙauna ga wasu ko da daga ina suka fito. Yesu ba zai bayyana darasin fiye da haka ba.
15 Shin abin mamaki ne da mutane suka yi “mamakin koyarwar” Yesu kuma suka matsa wajensa? (Matiyu 7:28, 29) A wani lokaci ‘taro mai-yawa’ suka kasance kusa da shi na kwana uku, babu abinci ma!—Markus 8:1, 2.
Hanyar Rayuwarsa
16. A wace hanya ce Yesu ya ba da “ainihin tabbacin” cewa hikima ta Allah ce take yi masa ja-gora?
16 Waje na uku da ya nuna hikimar Jehobah shi ne hanyar rayuwarsa. Ayyukan hikima a bayyane suke. “Wanene a cikinku mai-hikima ne?” almajiri Yakubu ya yi tambaya. Sai ya amsa tambayarsa, yana cewa: “Bari ɗabi’arsa da ta dace ta ba da ainihin tabbacin haka.” (Yakub 3:13, The New English Bible) Yadda Yesu ya bi ɗabi’a ya ba da “ainihin tabbacin haka” cewa hikima ta Allah ce take ja-gorarsa. Bari mu bincika yadda ya nuna fahimi, a hanyar rayuwarsa da kuma a sha’aninsa da wasu.
17. Waɗanne tabbaci ne muke da su cewa Yesu ya kasance da cikakken daidaita a rayuwarsa?
17 Ka lura cewa mutane waɗanda ba su da fahimi sau da yawa suna kama gefe ɗaya? Hakika yana bukatar hikima a daidaita. Nuna hikima ta Allah, Yesu yana da daidaita ƙwarai. Fiye da kome, ya saka abubuwa na ruhaniya farko a rayuwarsa. Ya shagala ƙwarai a cikin aikin shelar bishara. “Dalilin zuwana ke nan.” (Markus 1:38) Abin duniya, ba su suka fi muhimmanci ba a gare shi; kamar dai ba shi da abin duniya. (Matiyu 8:20) Duk da haka, ba marar farin ciki ba ne. Kamar Ubansa, ‘Allah mai farin ciki,’ Yesu mutum ne mai farin ciki, kuma ya ƙara ga farin cikin wasu. (1 Timoti 1:11; 6:15) Sa’ad da ya halarci wani bikin aure—ainihi abin da ake kaɗe-kaɗe, waƙe-waƙe, da kuma farin ciki—bai je ba ne don ya ɓata sha’ani. Sa’ad da giya ta ƙare, ya mai da ruwa ta zama giya, aba da take “faranta wa mutum zuciya.” (Zabura 104:15; Yohanna 2:1-11) Yesu ya amsa gayyata da yawa zuwa dina, kuma sau da yawa ya yi amfani da irin wannan zarafin wajen koyarwa.—Luka 10:38-42; 14:1-6.
18. Ta yaya Yesu ya nuna fahimi marar kure a sha’aninsa da almajiransa?
18 Yesu ya nuna fahimi marar kure a sha’aninsa da wasu. Fahiminsa game da yadda mutane suke ya sa ya fahimci almajiransa ƙwarai. Ya tabbata cewa ba kamilai ba ne. Duk da haka, ya fahimci gano halayensu masu kyau. Ya ga waɗannan mutane da Jehobah ya jawo za su kasance na kirki. (Yohanna 6:44) Duk da kurakuransu, Yesu ya nuna ya yarda da su da son rai. Ya nuna wannan yardar, ya ba da hakki mai girma ga almajiransa. Ya umarce su su yi wa’azin bishara, kuma ya tabbata za su iya su cika wannan umurnin. (Matiyu 28:19, 20) Littafin Ayukan Manzanni ya tabbatar da cewa sun yi aikin da aka umarce su cikin aminci. (Ayyukan Manzanni 2:41, 42; 4:33; 5:27-32) A bayyane yake, Yesu ya yi hikima da ya yarda da su.
19. Ta yaya Yesu ya nuna cewa shi mutum “mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya”?
19 Kamar yadda muka lura a Babi na 20, Littafi Mai Tsarki ya danganta tawali’u da kuma rashin tsanantawa da hikima. Hakika, Jehobah ne ya kafa misali mafi kyau a wannan batun. Amma Yesu kuma fa? Yana daɗaɗa rai mu ga yadda Yesu ya nuna tawali’u a sha’aninsa da almajiransa. Tun da mutum ne kamili, ya fi su. Duk da haka, bai raina almajiransa ba. Ko kuma ya nemi ya nuna su ba kome ba ne. Akasarin haka, ya yi la’akari da kasawarsu kuma ya yi haƙuri da kurakuransu. (Markus 14:34-38; Yohanna 16:12) Ba shi da muhimmanci ne da yara ma suka sake a wajen Yesu? Babu shakka, suna matsa wajensa domin sun fahimci cewa shi mutum “mai tawali’u ne, mai sauƙin kai.”—Matiyu 11:29; Markus 10:13-16.
20. Ta yaya Yesu ya nuna la’akari a sha’aninsa da mace ta Al’umma wadda ’yarta take da aljan?
20 Yesu ya nuna tawali’u na Allah har yanzu a wata hanya. Yana da la’akari, sa’ad da jinƙai ya sa wannan ya dace. Alal misali, ka tuna da lokacin da mace daga Al’ummai ta roƙe shi ya warkar da ’yarta da take da aljan. A hanyoyi uku dabam dabam Yesu ya nuna da farko cewa ba zai taimake ta ba—na fari, ya ƙi ya yi mata magana; na biyu, ya faɗa kai tsaye cewa an aiko shi, ba domin na Al’ummai ba ne, amma domin Yahudawa; kuma na uku, ta wajen ba da misali da ya nuna haka. Duk da haka, matar ta nace, wannan ya ba da tabbacin bangaskiya mai ƙarfi ƙwarai. Yin la’akari da wannan yanayi, mene ne Yesu ya yi? Ya yi abin da ya ce ba zai yi ba. Ya warkar da ’yar matar. (Matiyu 15:21-28) Yana da tawali’u na ban mamaki, ko ba haka ba? Ka tuna, tawali’u ne tushen hikima ta gaske.
21. Me ya sa za mu yi ƙoƙari mu yi koyi da mutuntaka, furci, da kuma hanyoyin Yesu?
21 Za mu yi godiya cewa Linjila ta bayyana mana kalmomi da kuma ayyukan mutum mafi hikima da ya taɓa rayuwa! Bari mu tuna cewa Yesu kamilin kamani ne na Ubansa. Ta wajen bin mutuntaka, furci, da kuma hanyoyin Yesu, za mu koyi hikima da take zuwa daga bisa. A cikin babi na gaba za mu ga yadda za mu yi amfani da hikima ta Allah a rayuwarmu.
a A lokacin Littafi Mai Tsarki, ana kiran masassaƙa wajen gina gidaje, gyara kujeru, da kuma kayan aikin gona. Justin Martyr, na ƙarni na biyu A.Z., ya rubuta game da Yesu: “Yana aikin sassaƙa sa’ad da yake tsakanin mutane, yana gyara ƙotoci da karkiya.”
b Aikatau na Helenanci da aka fassara “damu” yana nufin “a janye hankalin zuciya.” Kamar yadda aka yi amfani da shi a Matiyu 6:25, tana nufin damuwa ƙwarai da take janye ko kuma raba zuciya, ta ɗauke murna daga rayuwa.
c Babu shakka, nazarin kimiyya ya nuna cewa damuwa da yawa za ta iya sa mu cikin haɗarin kamuwa da ciwon zuciya da kuma wasu cututtuka masu yawa da za su rage tsawon rai.