Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 1/15 pp. 3-7
  • ‘Ka Zo Ka Bi Ni’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • ‘Ka Zo Ka Bi Ni’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Za Mu Bi Yesu?
  • Ka Yi Koyi da Hikimar Yesu
  • Ka Kasance da Tawali’u Kamar Yesu
  • Ka Kasance Mai Ƙwazo Kamar Yesu
  • Bin Yesu Yana Nufin Mu Ƙaunaci Mutane
  • Me Ya Sa Za Ka Bi “Kristi”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Yesu Ya Kafa Misali Na Tawali’u
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Ka Bi Isharar Da Yesu Ya Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • “Na Yi Muku Kwatanci”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 1/15 pp. 3-7

‘Ka Zo Ka Bi Ni’

“Idan kowane mutum yana nufi shi bi ni, sai shi yi musun kansa, shi ɗauki gicciyensa kowacce rana, shi biyo ni.”—LUK. 9:23.

1, 2. (a) Wace irin gayyata mai kyau ce Yesu ya yi? (b) Ta yaya ka karɓi gayyatar Yesu?

GAB da ƙarshen hidimarsa, Yesu yana wa’azi a Periya, wata ƙasa da ke tsallaken Urdun, a arewa maso gabashin Yahudiya. Wani saurayi ya tambayi shi abin da zai yi domin ya sami rai madawwami. Bayan Yesu ya lura cewa wannan saurayin yana bin Dokar Musa sosai, Yesu ya yi masa wata gayya mai muhimmanci. Ya ce: “Ka tafi, ka sayarda abin da ka ke da shi duka, ka ba fakirai, za ka sami wadata a sama: ka zo kuma, ka biyo ni.” (Mk 10:21) Ka yi tunani, an gayyace shi ya bi Yesu, Ɗa makaɗaici na Allah Maɗaukakin Sarki!

2 Wannan saurayin ya ƙi wannan gayyatar, amma wasu sun karɓi gayyatar. A farkon hidimarsa, Yesu ya gaya wa Filibus: “Ka biyo ni.” (Yoh. 1:43) Filibbus ya karɓi wannan gayyatar kuma daga baya ya zama manzo. Yesu ya sake yi wa Matta wannan gayyatar, shi ma ya karɓi gayyatar. (Mat. 9:9; 10:2-4) Hakika, Yesu ya miƙa irin wannan gayyatar ga dukan waɗanda suke ƙaunar adalci sa’ad da ya ce: “Idan kowane mutum yana nufi shi bi ni, sai shi yi musun kansa, shi ɗauki gicciyensa kowacce rana, shi biyo ni.” (Luk 9:23) Saboda haka, kowane mutum yana iya zama mabiyin Yesu idan yana son ya yi hakan. Kana da irin wannan muradin? Yawancinmu mun riga mun karɓi wannan gayyatar, kuma a hidimar fage muna miƙa irin wannan gayyatar ga mutane.

3. Ta yaya za mu guji zakuɗawa daga bin Yesu?

3 Abin baƙin ciki, wasu da suka nuna suna son gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki sun daina yin nazari. Sun daina nuna ƙwazo, kuma daga baya sun “zakuɗa” daga bin Yesu. (Ibran. 2:1) Ta yaya za mu guji faɗawa irin wannan tarkon? Yana da kyau mu tambayi kanmu: Me ya sa na zaɓi na bi Yesu? Ta yaya za mu bi shi? Amsoshin waɗannan tambayoyi za su taimake mu mu ƙarfafa ƙudurinmu na ci gaba da bin hanya mai kyau da muka zaɓa. Kuma hakan zai taimaka mana mu ƙarfafa wasu su bi Yesu.

Me Ya Sa Za Mu Bi Yesu?

4, 5. Me ya sa Yesu ya cancanci ya yi shugabanci?

4 Annabi Irmiya ya ce: “Ya Ubangiji, na tabbata hanyar mutum ba cikin nasa hannu ta ke ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.” (Irm. 10:23) Tarihi ya nuna gaskiyar kalaman Irmiya. A bayyane yake cewa mutane ajizai ba za su iya yi wa kansu ja-gora ko su mulki kansu ba. Mun yarda mu bi Yesu domin mun koyi cewa shi ne ya cancanci ya zama Shugabanmu fiye da kowane mutum. Ga wasu cikin abubuwan da suka sa ya cancanta.

5 Na farko, Jehobah ne da kansa ya zaɓi Yesu ya zama Almasihu. Wanene ya fi Mahaliccinmu sanin irin Shugaban da muke bukata? Na biyu, Yesu yana da halaye masu ban sha’awa da za mu iya koyi da su. (Karanta Ishaya 11:2, 3.) Shi misali ne mafi kyau. (1Bit. 2:21) Na uku, Yesu ya damu ƙwarai da waɗanda suke bin sa, kamar yadda ya nuna sa’ad da ya mutu dominsu. (Karanta Yohanna 10:14, 15.) Kuma ya nuna cewa shi makiyayi ne mai kula yayin da yake yi mana ja-gora zuwa rayuwar da ke kawo farin ciki a yanzu da kuma rayuwa ta har abada a nan gaba. (Yoh 10:10, 11; R. Yoh 7:16, 17) Domin waɗannan dalilan da wasu, mun yanke shawara mai kyau sa’ad da muka karɓi gayyatar bin sa. Amma, menene wannan tafarkin ya ƙunsa?

6. Menene bin Yesu ya ƙunsa?

6 Kasancewa mabiyan Yesu ya wuce kiran kanmu Kirista kawai. Mutane fiye da biliyan biyu ne suke da’awar cewa su Kiristoci ne a yau, amma ayyukansu sun tabbatar da cewa su “masu-aika mugunta” ne. (Karanta Matta 7:21-23.) Sa’ad da mutane masu marmari suka karɓi gayyatar su bi Yesu, muna bayyana musu cewa Kiristoci na gaskiya suna sa dukan rayuwarsu ta jitu da koyarwa da kuma misalin Yesu, kuma suna yin hakan a rayuwarsu ta yau da kullum. Ta wajen kwatanta ma’anar hakan, yi la’akari da wasu abubuwa da muka sani game da Yesu.

Ka Yi Koyi da Hikimar Yesu

7, 8. (a) Mecece hikima, kuma me ya sa Yesu yake da ita sosai? (b) Ta yaya ne Yesu ya nuna hikima, kuma ta yaya za mu yi koyi da shi?

7 Yesu ya nuna halaye masu yawa da suka fita dabam, amma za mu mai da hankali ne a kan guda huɗu: hikimarsa, tawali’unsa, ƙwazonsa, da kuma ƙaunarsa. Na farko, yi la’akari da hikimarsa, wato, iyawarsa na yin amfani da sani da kuma fahimi a hanyoyi masu kyau. Manzo Bulus ya rubuta: “[Yesu] wanda an ɓoye dukan dukiya ta hikima da ta ilimi cikinsa.” (Kol. 2:3) A ina ne Yesu ya sami irin wannan hikimar? Shi da kansa ya ce: “Ina faɗin waɗannan magana yadda Uba ya koya mani.” (Yoh. 8:28) Jehobah ne ya ba shi hikima, saboda haka, matakan da Yesu ya ɗauka ba su ba mu mamaki ba.

8 Alal misali, Yesu ya nuna fahimi a irin tafarkin rayuwar da ya zaɓa. Ya zaɓi ya yi rayuwa mai sauƙi, ta wajen mai da hankali ga abu ɗaya: yin nufin Allah. Ya yi amfani da lokacinsa da kuma ƙarfinsa wajen faɗaɗa ayyukan Mulki. Muna bin misalin Yesu ta wajen yin “rayuwa mai sauƙi,” kuma mu guje wa nauyaya wa kanmu da abubuwa da ba su zama dole ba da suke ɗaukan hankalinmu da kuma ƙarfi. (Mat. 6:22, NW) Kiristoci da yawa sun ɗauki matakin sauƙaƙa irin salon rayuwa da suke yi domin su ba da ƙarin lokaci ga hidima. Wasu sun shiga hidimar majagaba. Idan kana ɗaya daga cikinsu, an yaba maka sosai. “Fara biɗan mulkinsa” yana kawo farin ciki mai yawa da kuma gamsuwa.—Mat. 6:33.

Ka Kasance da Tawali’u Kamar Yesu

9, 10. Ta yaya ne Yesu ya nuna tawali’unsa?

9 Sashe na biyu na halin Yesu da za mu tattauna shi ne tawali’unsa. Sa’ad da mutane ajizai suka sami iko, sau da yawa suna nuna cewa su masu martaba ne. Yesu bai yi haka ba! Duk da matsayinsa wajen cika nufin Jehobah, Yesu bai yi fahariya ko kaɗan ba. Kuma an ƙarfafa mu mu yi koyi da shi a wannan ɓangaren. Manzo Bulus ya rubuta: “Ku kasance da wannan hali a cikinku wanda ke cikin Kristi Yesu kuma: shi da shi ke cikin surar Allah, ba ya maida kasancewarsa daidai da Allah abin rairaito ba, amma ya wofinta kansa da ya ɗauki surar bawa, yana kasancewa da sifar mutane.” (Filib. 2:5-7) Menene hakan ya ƙunsa?

10 Yesu ya more gata mai girma na kasancewa da Ubansa a sama, amma da son rai ya “wofinta kansa.” An tura ransa zuwa cikin wata budurwa Bayahudiya, kuma bayan wata tara an haife shi jarari marar ƙarfi a cikin gidan wani kafinta talaka. A cikin gidan Yusufu, Yesu ya yi girma, ya zama ɗan ƙaramin yaro da kuma saurayi. Ba shi da zunubi. Duk da haka, a dukan ƙuruciyarsa ya kasance mai biyayya ga iyayensa ajizai masu zunubi. (Luk 2:51, 52) Hakika wannan tawali’u ne mai girma!

11. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin koyi da tawali’un Yesu?

11 Muna koyi da Yesu sa’ad da da son rai muka karɓi ayyukan da ake ganin ba su da martaba. Alal misali, ka yi la’akari da aikin yin wa’azin bishara. Irin wannan aikin zai iya kasancewa marar martaba, musamman ma idan mutane suka nuna ƙiyayya, ko suka yi ba’a. Amma, ta wajen jimrewa a aikin wa’azin, za mu taimaki mutane su karɓi gayyatar Yesu su bi shi. Da haka mun taimaka wajen ceton rayuka. (Karanta 2 Timothawus 4:1-5.) Wani misali kuma shi ne kula da Majami’ar Mulkinmu. Wannan ya ƙunshi ayyuka kamar su zubar da shara, wanke ƙasa, da kuma inda ake ba haya, waɗannan ayyuka ne ƙanana. Duk da haka, mun fahimci cewa kula da Majami’ar Mulkinmu, wadda ita ce cibiyar bauta ta gaskiya, sashe ne na bautarmu mai tsarki. Ta wajen yin aikin da ake ɗauka marar martaba da son rai, muna nuna tawali’u kuma ta haka muna bin sawun Kristi.

Ka Kasance Mai Ƙwazo Kamar Yesu

12, 13. (a) Ta yaya Yesu ya nuna ƙwazo, kuma mecece ta motsa shi? (b) Menene zai motsa mu mu kasance da ƙwazo a hidima?

12 Yi la’akari da ƙwazon Yesu a hidima. Yesu ya yi abubuwa masu yawa sa’ad da yake duniya. Sa’ad da yake matashi, wataƙila ya yi aikin kafinta tare da Yusufu, mijin mahaifiyarsa. A lokacin hidimarsa, Yesu ya yi mu’ujizai, waɗanda suka haɗa da warkar da majiyyata da kuma ta da matattu. Amma ainihin aikinsa shi ne yin wa’azin bishara da kuma koyar da waɗanda za su saurare shi. (Mat. 4:23) A matsayinmu na mabiyansa, mu ma aikinmu ke nan. Ta yaya za mu iya bin misalinsa? Wani abu shi ne, za mu iya kasancewa da irin wannan muradin kamar Yesu.

13 Fiye da komi, ƙaunar da yake yi wa Allah ta motsa Yesu ya yi wa’azi da kuma koyarwa. Yesu kuma yana ƙaunar gaskiyar da yake koyarwa. A gareshi, wannan gaskiyar aba ce mai tamani ƙwarai, kuma yana ɗokin ya gaya wa mutane. A matsayinmu na masu koyarwa, muna jin yadda ya ji. Ka yi tunanin wasu gaskiya masu tamani da muka koya daga Kalmar Allah! Mun san batun ikon mallaka na dukan sararin samaniya da kuma yadda za a warware shi. Mun fahimci abin da Nassosi suka koyar game da yanayin matattu da kuma albarkar Mulki da za a samu a sabuwar duniya ta Allah. Ko da mun koyi waɗannan gaskiya ba da daɗewa ba ko daɗewa, muhimmancinsu ba ya shuɗewa. Waɗannan gaskiya suna da tamani ƙwarai. (Karanta Matta 13:52.) Ta wajen yin wa’azi da ƙwazo, muna nuna wa mutane ƙaunarmu ta abin da Jehobah ya koyar da mu.

14. Ta yaya za mu iya yin koyi da yadda Yesu yake koyarwa?

14 Ka yi la’akari kuma da yadda Yesu ya koyar. A kowane lokaci, yana mai da hankalin masu sauraronsa ga Nassosi. A yawancin lokaci yana gabatar da bayani mai muhimmanci ta wajen cewa: “An rubuta.” (Mat. 4:4; 21:13) A cikin kalamansa da aka rubuta, ya yi ƙauli kai tsaye ko kuma ya yi nuni a wasu hanya ga rabin Nassosin Ibrananci. Kamar Yesu, mun dogara ƙwarai a kan Littafi Mai Tsarki a hidimarmu kuma muna ƙoƙarin gabatar da Nassosi a duk lokacin da hakan zai yiwu. Ta haka, muna taimaka wa masu zuciyar kirki su gani da kansu cewa muna koyar da abin da Allah ya ce, ba namu ba. Muna yin farin ciki idan mutum ya yarda ya karanta Littafi Mai Tsarki kuma ya tattauna muhimmanci da kuma ma’anar Kalmar Allah! Sa’ad da irin waɗannan mutanen suka karɓi gayyatar su bi Yesu, farin cikinmu yana ƙaruwa sosai.

Bin Yesu Yana Nufin Mu Ƙaunaci Mutane

15. Wane hali ne na Yesu ya fita dabam, kuma ta yaya yin bimbini a kansa zai shafe mu?

15 Ɓangare na ƙarshe na halin Yesu da za mu tattauna shi ne ya fi taɓa zuciya, wato, ƙaunar da yake yi wa mutane. Manzo Bulus ya rubuta: “Ƙaunar Kristi tana i mana.” (2 Kor. 5:14) Sa’ad da muka yi bimbini a kan irin ƙaunar da Yesu yake yi wa dukan ’yan adam da kowannenmu, hakan na daɗaɗa zuciyarmu, kuma yana motsa mu mu bi misalinsa.

16, 17. A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya nuna ƙaunarsa ga mutane?

16 Ta yaya ne Yesu ya nuna ƙauna ga mutane? Ba da ransa da ya yi da son rai domin ’yan adam ita ce ƙauna mafi girma da ya nuna. (Yoh. 15:13) Amma, a lokacin hidimarsa, Yesu ya nuna ƙauna a wasu hanyoyi. Alal misali, ya nuna juyayi ga waɗanda suke shan wahala. Sa’ad da ya ga Maryamu da kuma waɗanda suke tare da ita suna kukan mutuwar Li’azaru, baƙin cikin da suke yi ya dame shi ƙwarai. Ko da yake yana gab da ta da Li’azaru daga matattu, abin ya motsa Yesu har “ya yi kuka.”—Yoh. 11:32-35.

17 A farkon hidimar Yesu, wani kuturu ya je wajen Yesu kuma ya ce masa: “Idan ka yarda, kana da iko ka tsarkake ni.” Menene Yesu ya yi? Labarin ya ce: “Ya ji juyayi.” Sai ya yi wani abin mamaki. “Ya miƙa hannunsa, ya taɓa shi, ya ce masa, Na yarda; ka tsarkaka. Nan da nan kuturta ta rabu da shi, ya tsarkaka.” Bisa Dokar Musa, kutare ba su da tsarki, kuma Yesu yana iya warkar da mutumin ba tare da ya taɓa shi ba. Duk da haka, sa’ad da Yesu yake warkar da kuturun, ya sa mutumin ya ji cewa wani ya taɓa shi, wataƙila hakan shi ne na farko tun shekaru masu yawa. Hakika wannan juyayi ne mai girma!—Mar. 1:40-42.

18. Ta yaya za mu nuna “juyayi”?

18 Mu mabiyan Kristi, an umurce mu mu nuna ƙaunarmu ta wajen nuna “juyayi.” (1 Bit. 3:8) Ba zai yi sauƙi ba a fahimci yadda ɗan’uwa mai bi da yake fama da wani mugun ciwo yake ji, musamman ma idan ba mu taɓa fuskantar irin wannan cutar ba da kanmu. Duk da haka, Yesu ya nuna juyayi ga masu ciwo ko da yake shi da kansa bai taɓa yin ciwo ba. Ta yaya za mu koyi irin wannan juyayin? Ta wajen saurarawa da haƙuri sa’ad da waɗanda suke wahala suke gaya mana yadda suke ji. Muna iya tambayar kanmu, ‘Da a ce ni ne ke fama da wannan yanayi, da yaya zan ji?’ Idan muka kyautata fahimtarmu ta yadda wasu suke ji, za mu fi iya “ƙarfafa masu-raunanan zukata.” (1Tas. 5:14) Da haka, za mu ci gaba da bin Yesu.

19. A waɗanne hanyoyi ne misalin Yesu suka shafe mu?

19 Hakika mun sami abin nazari mai ban marmari a ayyuka da kuma kalaman Yesu Kristi! Da zarar mun ƙara sani game da shi, haka nan kuma za mu so mu zama kamarsa, kuma haka za mu so mu taimaki wasu su ma su zama kamarsa. Ko ta yaya, bari mu ci gaba da kasancewa da marmarin bin Sarki Almasihu, a yanzu da har abada!

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Ta yaya za mu nuna hikima kamar Yesu?

• A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna tawali’u?

• Ta yaya za mu iya nuna ƙwazo ga hidima?

• A waɗanne hanyoyi ne za mu iya koyi da Yesu wajen nuna ƙauna ga mutane?

[Akwati/Hotunan da ke shafi na 5]

Littafin Da Zai Taimaka Mana Mu Yi Koyi Da Kristi

A taron gunduma na shekara ta 2007, an fito da littafi mai shafi 192 mai jigo “Come Be My Follower.” An shirya wannan littafin ne don ya taimaka wa Kiristoci su mai da hankali ga Yesu, musamman a kan halayensa da kuma ayyukansa. Bayan babi na ɗaya da na biyu da gabatarwa ne, sashe na farko ya taƙaita halayen Yesu na musamman, wato, tawali’unsa, gaba gaɗinsa, hikimarsa, biyayyarsa, da kuma jimrewarsa.

Bayan haka, akwai sashe da suka tattauna ayyukan Yesu a matsayin malami da mai wa’azin bishara da kuma wasu hanyoyi da ya nuna ƙaunarsa mai girma. A littafin gabaki ɗaya, an ba da bayanan da za su taimaki Kirista ya yi koyi da Yesu.

Muna da tabbaci cewa wannan littafin zai motsa dukanmu mu bincika kanmu kuma mu yi tambaya: ‘Ina bin Yesu kuwa da gaske? Ta yaya zan bi shi da kyau?’ Zai kuma taimaka wa “waɗanda aka ƙadara su ga rai na har abada” su zama mabiyan Kristi.—A. M. 13:48.

[Hotunan da ke shafi na 4]

Yesu ya yarda ya zo duniya kuma a haife shi jariri ɗan adam. Wane hali ne hakan yake bukata?

[Hotunan da ke shafi na 6]

Menene zai motsa mu mu zama masu ƙwazo a hidima?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba