Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 5/15 pp. 28-32
  • Me Ya Sa Za Ka Bi “Kristi”?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Za Ka Bi “Kristi”?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Don Mu Daɗa Ƙulla Dangantaka da Jehobah
  • Don Mu Yi Koyi da Jehobah Sosai
  • Yesu Ne Shafaffe na Jehobah
  • Yesu Ne Kawai Hanyar Samun Ceto
  • An Umurce Mu Mu Saurari Kristi
  • Wanene Yesu Kristi?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Wane ne Yesu Kristi?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • ‘Ka Zo Ka Bi Ni’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Wane ne Yesu?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 5/15 pp. 28-32

Me Ya Sa Za Ka Bi “Kristi”?

“Idan kowane mutum yana nufi shi bi ni, sai shi yi musun kansa, . . . kowacce rana, shi biyo ni.”—LUK 9:23.

1, 2. Me ya sa yake da muhimmanci mu tattauna abin da ya sa ya kamata mu bi “Kristi”?

JEHOBAH yana farin cikin ganin sababbi da suke son su san gaskiya da kuma matasa da suke cikin taron masu bauta masa a duniya! Yayin da kake ci gaba da yin nazarin Littafi Mai Tsarki, halartan taron Kirista a kai a kai, ka kuma ƙara saninka ta gaskiyar da ke ceton rai da ke cikin Kalmar Allah, kana bukatar ka yi tunani sosai game da gayyatar Yesu: “Idan kowane mutum yana nufi shi bi ni, sai shi yi musun kansa, shi ɗauki gicciyensa kowacce rana, shi biyo ni.” (Luk 9:23) Yesu yana cewa kana bukatar ka yi musun kanka kuma ka zama mabiyinsa. Yana da muhimmanci mu bincika abin da ya sa ya kamata mu bi “Kristi.”—Mat. 16:13-16.

2 Waɗanda suka riga suka soma bin sawun Yesu Kristi kuma fa? An ƙarfafa mu mu “yalwata gaba gaba a ciki.” (1 Tas. 4:1, 2) Ko mun soma bauta ta gaskiya kwanan nan ko kuma mun yi hakan sun ta daɗewa, yin tunani a kan dalilin da ya sa muke bin Kristi zai taimake mu mu yi amfani da shawarar Bulus kuma mu bi shi a rayuwarmu ta kullum. Bari mu tattauna dalilai biyar da suka sa ya kamata mu bi Kristi.

Don Mu Daɗa Ƙulla Dangantaka da Jehobah

3. Waɗanne hanyoyi biyu ne za su taimaka mana mu san Jehobah?

3 Sa’ad da yake magana da ’yan Atina yayin da ya “tsaya a tsakiyar tudun Arasa,” manzo Bulus ya ce: “[Allah] yana sanya masu wokatai waɗanda ya ayana, da iyakan mazauninsu: domin su nemi Allah, ko halama su a lallaba su same shi, ko da shi ke ba shi da nisa da kowane ɗayanmu ba.” (A. M. 17:22, 26, 27) Muna iya biɗar Allah kuma mu san shi sosai. Alal misali, sa’ad da muka dubi halitta, muna koyan abubuwa da yawa game da halayen Allah da iyawarsa. Yin bimbini da godiya a kan ayyukansa na halitta zai iya koya mana abubuwa masu yawa game da Mahalicci. (Rom. 1:20) Jehobah ya kuma bayyana abubuwa dalla-dalla game da kansa a cikin rubutacciyar Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. (2 Tim. 3:16, 17) Sa’ad da muka daɗa yin ‘bimbinin [game da] aikinsa’ kuma muka mai da hankali sosai ‘a kan aike aikensa,’ hakan zai taimaka mana mu ƙara sanin Jehobah da kyau.—Zab. 77:12.

4. Yaya bin Kristi zai taimake mu mu san Jehobah sosai?

4 Hanya mai kyau ta sanin Jehobah sosai ita ce bin Kristi. Ka yi tunanin ɗaukakar da Yesu yake da ita tare da Ubansa “tun duniya ba ta zama ba.” (Yoh. 17:5) Shi ne “farkon halittar Allah.” (R. Yoh. 3:14) Da yake shi “ɗan fari ne gaban dukan halitta,” ya yi rayuwa shekaru aru-aru a sama da Ubansa, Jehobah. Kafin ya zo duniya, ba wai kawai Yesu yana tare da Ubansa ba ne. Shi abokin zaman Allah ne, yana aiki cikin farin ciki da Maɗaukaki Duka, kuma babu wanda ya taɓa ƙulla dangantaka na kud da kud kamar Allah da Yesu. Yesu ya lura da yadda Ubansa yake yin abubuwa, ya lura da yadda yake ji game da abubuwa da kuma halayensa, ya yi koyi da kuma soma yin dukan abubuwan da ya koya game da Ubansa. A sakamakon haka, wannan Ɗan mai biyayya ya zama kamar Ubansa, wanda hakan ya sa Littafi Mai Tsarki ya kira shi ‘surar Allah marar-ganuwa.’ (Kol. 1:15) Ta wajen bin Kristi sawu da kafa, za mu iya ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah.

Don Mu Yi Koyi da Jehobah Sosai

5. Menene zai taimake mu mu yi koyi da Jehobah sosai, kuma me ya sa?

5 An yi mu ‘cikin surar Allah, bisa ga kamaninsa,’ saboda haka, muna iya nuna halayen Allah. (Far. 1:26) Manzo Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su “zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu.” (Afis. 5:1) Bin Kristi yana taimaka mana mu yi koyi da Ubanmu na samaniya. Domin Yesu ne ya fi kowa nuna tunanin Jehobah da ayyukansa, kuma babu wanda zai iya koya mana sosai game da Jehobah fiye da shi. Sa’ad da yake duniya, Yesu bai sanar da sunan Jehobah kawai ba. Maimakon haka, ya bayyana mana ainihin ko wanene Allah. (Karanta Matta 11:27.) Yesu ya yi hakan ta hanyar kalamansa da ayyukansa, koyarwarsa da kuma misalinsa.

6. Menene koyarwar Yesu ta bayyana game da Jehobah?

6 Ta koyarwarsa, Yesu ya bayyana mana abin da Allah yake bukata a gare mu da kuma yadda yake ji game da masu bauta masa. (Mat. 22:36-40; Luk 12:6, 7; 15:4-7) Alal misali, bayan ya yi ƙaulin ɗaya daga cikin Dokokin Goma, wato, “ba za ka yi zina ba,” Yesu ya bayyana ra’ayin Allah game da abin da yake cikin zuciyar mutum tun kafin ya yi wannan zunubin. Ya ce: “Dukan wanda ya duba mace har ya yi ƙyashinta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyatasa.” (Fit. 20:14; Mat. 5:27, 28) Bayan ya faɗi yadda Farisawa suka bayyana wani kalami cikin Doka wadda ta ce “ka yi ƙaunar maƙwabcinka, ka ƙi magabcinka,” Yesu ya taimaka musu su san tunanin Jehobah, ya ce: “Ku yi ƙaunar magabtanku, kuma waɗanda su kan tsananta muku, ku yi musu addu’a.” (Mat. 5:43, 44; Fit. 23:4; Lev. 19:18) Fahimtar yadda Allah yake tunani da kuma yadda yake ji da kuma abin da yake bukata a gare mu zai taimaka mana mu yi koyi da shi sosai.

7, 8. Menene muka koya game da Jehobah daga misalin Yesu?

7 Yesu ya kuma bayyana yadda Ubansa yake ji ta wurin misalinsa. Sa’ad da muka karanta cikin Linjila cewa Yesu ya ji tausayin mabukata, ya yi juyayin waɗanda suke wahala, yadda ya yi fushi da almajiransa da suka tsauta wa yara, hakan ya nuna mana ainihin yadda Ubansa yake ji da kuma motsin ransa. (Mar. 1:40-42; 10:13, 14; Yoh. 11:32-35) Ka yi tunanin yadda ayyukan Yesu suka taimaka mana mu fahimci halayen Allah. Mu’ujizai da Kristi ya yi sun nuna cewa yana da iko sosai, ko ba haka ba? Duk da haka, bai taɓa yin amfani da wannan ikon don ya azurta kansa ba ko kuma ya yi wa mutane mugunta. (Luk 4:1-4) Matakin da ya ɗauka na jefar da ’yan kasuwa masu haɗama daga haikali ya nuna sarai cewa ya san abin da ya dace! (Mar. 11:15-17; Yoh. 2:13-16) Koyarwarsa da kuma zantattukan alheri da ya yi amfani da su don ya motsa zukatan mutane sun nuna cewa ya ‘fi Sulemanu’ hikima. (Mat. 12:42) An kwatanta ƙaunar da Yesu ya nuna ta wajen ba da ransa domin mutane sa’ad da Littafi Mai Tsarki ya ce, “ba wanda ya ke da ƙauna wadda ta fi gaban wannan.”—Yoh. 15:13.

8 Ɗan Allah ya wakilci Jehobah ƙwarai a dukan abubuwan da ya ce da kuma waɗanda ya yi, shi ya sa ya ce: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.” (Karanta Yohanna 14:9-11.) Bin Kristi daidai yake da yin koyi da Jehobah.

Yesu Ne Shafaffe na Jehobah

9. A wane lokaci ne kuma yaya Yesu ya zama Shafaffe na Allah?

9 Ka yi la’akari da abin da ya faru a kakar shekara ta 29 A.Z., sa’ad da Yesu ɗan shekara talatin ya zo wajen Yohanna Mai Baftisma. “Sa’anda aka yi masa baftisma, ya fita nan da nan daga cikin ruwa: ga kuwa sammai suka buɗe masa, ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya yana zuwa bisansa.” A wannan lokacin ne, ya zama Kristi, ko kuma Almasihu. Sa’an nan, Jehobah da kansa ya sanar cewa Yesu ne Shafaffensa, yana cewa: “Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina ya ji daɗinsa sarai.” (Mat. 3:13-17) Wannan dalili ne mai kyau da ya kamata ya motsa mu mu bi Kristi!

10, 11. (a) A waɗanne hanyoyi ne aka yi amfani da laƙabin nan “Kristi” ga Yesu? (b) Me ya sa ya kamata mu ci gaba da bin Yesu Kristi?

10 A cikin Littafi Mai Tsarki, an yi amfani da laƙabin nan “Kristi” ga Yesu a hanyoyi dabam-dabam, kamar Yesu Kristi, Kristi Yesu, da kuma Kristi. Yesu da kansa ya fara amfani da furcin nan “Yesu Kristi” wato, suna da yake biye da laƙabi. Sa’ad da yake addu’a ga Ubansa, ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.” (Yoh. 17:3) Yin amfani da wannan laƙabin yana jawo hankali ga mutumin da Allah ya aiko kuma ya zama Shafaffensa. Sa’ad da aka saka laƙabin kafin sunan, wato “Kristi Yesu,” ana nanata matsayinsa ne maimakon shi da kansa. (2 Kor. 4:5) Yin amfani da furcin nan “Kristi,” yana nanata matsayinsa ne na Almasihu.—Yoh 4:29.

11 Duk yadda aka yi amfani da lakabin nan “Kristi” ga Yesu, hakan yana nanata wannan gaskiya mai muhimmanci: Ko da yake Ɗan Allah ya zo duniya a matsayin mutum kuma ya sanar da nufin Ubansa, shi ba mutum kawai ba ne ko kuwa annabi kawai; ya zo ne ya zama Shafaffe na Jehobah. Kada mu yi wasa da bin wannan Shafaffen.

Yesu Ne Kawai Hanyar Samun Ceto

12. Wane furci da aka yi wa Thomas ne yake da muhimmanci a gare mu?

12 An ambata wani dalili na musamman na ci gaba da bin Almasihu a cikin kalmominsa ga manzanninsa masu aminci, ya faɗe su ne sa’o’i kaɗan kafin ya mutu. Sa’ad da yake amsa tambayar Thomas game da furcin Yesu na tafiya don ya shirya musu wuri, Yesu ya ce: “Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yoh. 14:1-6) A lokacin, Yesu yana magana ne ga manzaninsa masu aminci guda sha ɗaya. Ya yi musu alkawari cewa za su zauna a sama, amma kalmominsa suna da muhimmanci ma ga waɗanda suke da begen samun rai madawwami a duniya. (R. Yoh. 7:9, 10; 21:1-4) Ta yaya?

13. A wace hanya ce Yesu ‘hanya’?

13 Yesu Kristi shi ne ‘hanya.’ Wato, ta hanyarsa ce kawai za mu iya yi wa Allah magana. Hakan gaskiya a batun addu’a, idan muka yi addu’a ta hanyar Yesu ne kaɗai za mu iya samun tabbaci cewa Uba zai ba mu duk abin da muka roƙe shi idan hakan ya jitu da nufinsa. (Yoh. 15:16) Amma, Yesu wata ‘hanya’ ne a wani ɓangaren kuma. Zunubi ya ware ’yan adam daga Allah. (Isha. 59:2) Yesu ya ba da “ransa kuma abin fansar mutane dayawa.” (Mat. 20:28) A sakamakon haka, Littafi Mai Tsarki ya bayyana cewa: “Jinin Yesu . . . yana tsarkake mu kuma daga zunubi duka.” (1 Yoh. 1:7) Ta hakan, Ɗan ya buɗe hanyar sulhuntawa da Allah. (Rom. 5:8-10) Sai mun ba da gaskiya ga Yesu da kuma yi masa biyayya ne kawai za mu iya samun amintacciyar dangantaka da Allah.—Yoh. 3:36.

14. Ta yaya ne Yesu ya zama “gaskiya”?

14 Yesu shi ne “gaskiya” ba wai kawai domin yana faɗin gaskiya ba a koyaushe kuma yana rayuwar da ta yi daidai da gaskiyar ba, amma domin dukan annabce-annabce da aka rubuta game da Almasihu sun cika a kansa. Manzo Bulus ya rubuta: “Kome yawan alkawura na Allah, a cikinsa akwai i.” (2 Kor. 1:20) “Inuwar kyawawan matsaloli masu-zuwa” da suke cikin Dokar Musa sun bayyana a Kristi Yesu. (Ibran. 10:1; Kol. 2:17) Dukan annabce-annabce sun mai da hankali ne a kan Yesu, kuma sun taimake mu mu fahimci matsayinsa mai muhimmanci wajen cika nufin Jehobah. (R. Yoh. 19:10) Don mu amfana daga cikar abin da Allah ya nufa dominmu, muna bukatar mu bi Almasihu.

15. A wane azanci ne Yesu ya zama “rai”?

15 Yesu ne “rai” domin ya sayi ’yan adam da jininsa, kuma rai madawwami kyauta ce da Allah yake ba da wa ta hanyar “Kristi Yesu Ubangijinmu.” (Rom. 6:23) Yesu “rai” ne kuma ga waɗanda suka mutu. (Yoh. 5:28, 29) Bugu da ƙari, ka yi tunanin abin da zai yi a matsayin Babban Firist a lokacin Sarautarsa ta Shekara Dubu. Zai ceci talakawansa a duniya har abada daga zunubi da mutuwa!—Ibran. 9:11, 12, 28.

16. Wane dalili ne muke da shi da ya sa muke bin Yesu?

16 Amsar da Yesu ya ba Thomas a lokacin tana da ma’ana mai girma a gare mu. Yesu ne hanya da gaskiya da kuma rai. Shi ne wanda Allah ya aiko duniya don a ceci duniya ta wurinsa. (Yoh. 3:17) Kuma ba mai zuwa wurin Uba sai ta hanyarsa. Littafi Mai Tsarki ya faɗi dalla-dalla cewa: “Babu ceto ga waninsa: gama babu wani suna ƙarƙashin sama, da aka bayar wurin mutane, inda ya isa mu tsira.” (A. M. 4:12) Ko da menene muka yi imani da shi a dā, tafarkin hikima ce mu gaskata da Yesu, mu bi shi, kuma mu samu rai.—Yoh. 20:31.

An Umurce Mu Mu Saurari Kristi

17. Me ya sa yake da muhimmanci mu saurari Ɗan Allah?

17 Bitrus, Yohanna, da Yakubu sun ga sake kamani na Yesu. A lokacin sun ji murya daga sama tana cewa: “Wannan Ɗana ne, zaɓaɓena: ku ji shi.” (Luk 9:35) Yin biyayya ga umurnin nan na mu saurari Almasihu yana da muhimmanci sosai.—Karanta A. M. 3:22, 23.

18. Ta yaya za mu saurari Yesu Kristi?

18 Saurarar Yesu ya ƙunshi ‘zuba ido gare shi, mu [kuma] lura da misalinsa sosai.’ (Ibran. 12:2, 3) Saboda haka, yana da kyau “mu daɗa mai da hankali” ga abin da muka karanta game da shi a cikin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafan “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” da kuma abin da muka ji game da shi a taron Kirista. (Ibran. 2:1; Mat. 24:45) A matsayin mu na tumakinsa, bari mu ɗokin saurarar Yesu kuma mu bi shi.—Yoh. 10:27.

19. Menene zai taimake mu mu ci gaba da bin Kristi?

19 Zai yiwu mu ci gaba da bin Kristi, duk da matsaloli? Hakika, za mu iya, muddin mun “kiyaye kwatancin sahihiyan kalmomi” ta wajen yin abin da muka koya “cikin bangaskiya da ƙauna wadda ke cikin Kristi Yesu.”—2 Tim. 1:13.

Menene Ka Koya?

• Me ya sa bin “Kristi” zai daɗa sa mu kusaci Jehobah sosai?

• Me ya sa yin koyi da Yesu ya yi daidai da yin koyi da Jehobah?

• Me ya sa Yesu ne ‘hanya, gaskiya, da kuma rai’?

• Me ya sa za mu saurari Shafaffe na Jehobah?

[Hotunan da ke shafi na 29]

Koyarwar Yesu ta nuna tunani mai ɗauakaka na Jehobah

[Hotunan da ke shafi na 30]

Dole ne mu bi Shafaffe na Jehobah da aminci

[Hotunan da ke shafi na 32]

Jehobah ya sanar: ‘Wannan Ɗana ne ƙaunatacena: ku ji shi’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba