Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wt babi na 2 pp. 14-22
  • Ka Girmama Jehovah Domin Shi ne Allah Makaɗaici na Gaskiya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Girmama Jehovah Domin Shi ne Allah Makaɗaici na Gaskiya
  • Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Allah Ƙauna Ne”
  • Nuna Ƙauna ga Wasu
  • ‘Yi Tafiya Cikin Sunan Jehovah’
  • Ka Ƙaunaci Allah Da Yake Ƙaunarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙauna Ta Gina Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • “Ku Yi Zaman Ƙauna”
    Ka Kusaci Jehobah
  • Jehobah Allah Ne Mai Kauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Dubi Ƙari
Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
wt babi na 2 pp. 14-22

Babi Na Biyu

Ka Girmama Jehovah Domin Shi ne Allah Makaɗaici na Gaskiya

1. Wanene ne Allah Makaɗaici na gaskiya?

LITTAFI MAI TSAR KI ya ce ko da yake akwai wasu da yawa da ake ɗauka allohi, “a garemu akwai Allah ɗaya, Uba ne.” (1 Korinthiyawa 8:5, 6) “Allah ɗaya” ɗin nan Jehovah ne, Mahaliccin dukan abubuwa. (Kubawar Shari’a 6:4; Ru’ya ta Yohanna 4:11) Yesu ya ce game da shi “Allahna da Allahnku.” (Yohanna 20:17) Ya yarda da Musa, wanda da farko ya ce: “Ubangiji shi ne Allah; babu wani sai shi.” (Kubawar Shari’a 4:35) Jehovah ya fi kowane abu da ake wa sujjada, kamar su gumaka, siffar mutane, ko kuma magabcinsa Shaiɗan Iblis, “allah na wannan zamani.” (2 Korinthiyawa 4:3, 4) Ya bambanta daga dukan waɗannan, Jehovah, yadda Yesu ya kira shi, “Allah makaɗaici mai-gaskiya” ne.—Yohanna 17:3; Tafiyar tsutsa tamu ce.

2. Yayin da muka koya game da Allah, yaya ya kamata ya shafi rayuwarmu?

2 Mutane da suke nuna godiya da suka koyi game da kyawawan halayen Allah, da kuma abin da ya yi da har ila zai yi dominmu, suna matsowa wajensa. Yayin da ƙaunarsu ga Jehovah ta ƙaru, suna jin ya zama dole su girmama shi. Ta yaya? Hanya ɗaya ita ce, ta gaya wa wasu game da shi. “Da baki kuma a ke shaida zuwa ceto,” in ji Romawa 10:10. Wata hanya kuma ita ce ta yin koyi da shi ta kalma da kuma ta ayyuka. Afisawa 5:1 ya ce: “Ku zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu.” Don mu yi haka sosai, muna bukatar mu san mutuntakar Jehovah sosai.

3. Waɗanne ne muhimman halayen Allah?

3 Duk cikin Littafi Mai Tsarki, da akwai furci da yawa da ke nuna muhimman halayen Allah. Muhimman halayensa hikima ce, da yin gaskiya, da iko, da kuma ƙauna. ‘Hikima tana wurinsa.’ (Ayuba 12:13; Tafiyar tsutse tamu ce.) “Dukan tafarkunsa shari’a ne.” (Kubawar Shari’a 32:4; Tafiyar tsutse tamu ce.) “Mai-ƙarfi ne cikin iko.” (Ishaya 40:26; Tafiyar tsutse tamu ce.) “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Har ila yau, a cikin dukan halayensa huɗu musamman, wanne ne ya fi muhimmanci, wanda ya fi nuna irin Allah da yake?

“Allah Ƙauna Ne”

4. Wanne ne cikin halayen Allah ya motsa shi ya halicci sararin samaniya da dukan abubuwa masu rai?

4 Ka yi la’akari da abin da ya motsa Jehovah ya halicci sararin samaniya da halittu ruhohi da kuma mutane masu basira. Hikimarsa ce ko iko? A’a, ko da Allah ya yi amfani da su, ba su ne suka motsa shi ba. Kuma shari’arsa ba ta bukatar ya ba da kyautar rai ga wasu. Maimako, ƙauna mai girma na Allah ne ta motsa shi ya ba wa wasu rayuwa ta basira. Ƙauna ta motsa shi ya ƙudura cewa mutane masu biyayya za su rayu har abada cikin Aljanna. (Farawa 1:28; 2:15) Ƙauna ta motsa shi ya shirya kawar da hukunci da laifin Adamu ya jawo a kan bil Adam.

5. Bisa Littafi Mai Tsarki, wane hali ne Jehovah yake nuna, kuma me ya sa?

5 Domin haka, cikin dukan halayen Allah, mafi muhimmanci shi ne ƙaunarsa. Mutuntakarsa ce, halinsa kuma. Duk da muhimmancin hikimarsa, shari’a, da kuma iko, Littafi Mai Tsarki bai taɓa cewa Jehovah ɗaya ne cikinsu ba. Amma ya ce shi ƙauna ne. Hakika, Jehovah shi ne ƙauna. Wannan ƙauna ce ta ƙa’ida, ba daga motsin rai ba. Ƙaunar Allah ƙa’idodin gaskiya da adalci ne ke tsare ta. Ƙaunar mafi girma ce, wadda Jehovah Allah kansa ne yake nuna ta. Irin ƙaunar nan nuna rashin son kai ne, ko da yaushe ayyukan da take yi tabbacinta ce.

6. Me ya sa yana yiwuwa mu yi koyi da Allah ko da yake shi mafifici ne a kanmu?

6 Wannan muhimmin hali ne ya iya sa mu yi koyi da irin Allahn nan. Yadda muke ƙasassu, ajizai, masu yawan kuskure, za mu iya jin cewa ba za mu taɓa iya yin koyi da shi ba. Amma ga wani misalin ƙauna mai girma ta Jehovah: Ya san iyawarmu domin haka ba ya bukatar kamilci a gare mu. Ya sani cewa nesa muke da kamilci. (Zabura 51:5) Abin da ya sa ke nan Zabura 130:3, 4 suka ce: “Idan kai, ya Ubangiji, za ka ƙididdiga laifofi, wa za ya tsaya, ya Ubangiji? Amma akwai gafara [ta gaske] a wurinka.” Hakika, Jehovah, “Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai.” (Fitowa 34:6) “Nagari ne kai, ya Ubangiji, mai-hanzarin gafartawa.” (Zabura 86:5) Ta’aziyya ce wannan! Aba ce ta wartsakewa mu bauta wa wannan Allah mai halaye masu kyau don mu more ƙaunarsa, da kula na jinƙai!

7. Ta yaya za a iya ganin ƙaunar Jehovah cikin ayyukansa na halitta?

7 Ana iya ganin ƙaunar Jehovah kuma cikin ayyukansa na halitta. Ka yi tunanin abubuwa masu kyau da yawa da Jehovah ya yi tanadinsu don mu more, kamar su duwatsu masu kyau, kurmi, tafki, da kuma teku. Ya ba mu abinci iri-iri don mu more ɗanɗanonsu kuma mu samu lafiya. Jehovah kuma ya yi tanadin furanni kyawawa dabam dabam da kuma dabbobi masu kyan gani. Ya yi abubuwa da za su faranta wa mutane rai, ko da ba dole ne ya yi hakan ba. Gaskiya, rayuwa cikin wannan muguwar duniya cikin yanayinmu na ajizanci, ba za mu more halittunsa a cikakken hali ba. (Romawa 8:22) Ka yi tunanin abin da Jehovah zai yi mana a Aljanna! Mai Zabura ya ba mu tabbaci: “Kana buɗe hannunka, kana biya ma kowane mai-rai muradinsa.”—Zabura 145:16.

8. Wanne ne misali na musamman na ƙaunar Jehovah gare mu?

8 Menene misali na musamman na ƙaunar Jehovah ga bil Adam? Littafi Mai Tsarki ya yi bayani: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yohanna 3:16) Jehovah ya yi wannan saboda nagarta ne daga mutane? Romawa 5:8 ta amsa: “Allah yana shaidar ƙaunatasa garemu, da shi ke, tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu.” Hakika, Allah ya aika da kamiltaccen Ɗansa zuwa duniya ya ba da ransa hadayar fansa ya fanshe mu daga hukuncin zunubi da mutuwa. (Matta 20:28) Wannan ya buɗe hanya ga mutane da suke ƙaunar Allah su sami rai madawwami. Abin godiya, ƙaunar Allah ta kai wajen duka waɗanda suke so su yi nufinsa, domin Littafi Mai Tsarki ya ce mana: “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.”—Ayukan Manzanni 10:34, 35.

9. Ta yaya ya kamata gaskiyar cewa Jehovah ya ba da Ɗansa fansa gare mu ta shafe mu?

9 Yaya ya kamata gaskiyar cewa Jehovah ya ba da Ɗansa dominmu ya zama fansa, da ke buɗe hanyar rai madawwami, zai shafi yadda muke rayuwa a yanzu? Ya kamata ya sa ƙaunarmu ga Allah na gaskiya, Jehovah, ta yi zurfi. Har ila kuma, ya kamata ya sa mu so mu saurari Yesu, wanda ya wakilci Allah. “[Yesu] ya mutu sabili da duka, domin waɗanda ke rayuwa kada su ƙara rayuwa ga kansu, amma ga wanda ya mutu . . . sabili da su.” (2 Korinthiyawa 5:15) Lalle abin farin ciki ne a bi sawun Yesu, domin shi misali ne mai kyau wajen yin koyi da ƙauna da kuma juyayin Jehovah! Wannan yana cikin abin da ya gaya wa masu tawali’u: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗauka ma kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma mara-nauyi.”—Matta 11:28-30.

Nuna Ƙauna ga Wasu

10. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna ƙauna ga ’yan’uwa Kirista?

10 Ta yaya za mu iya nuna muna da irin ƙauna da Jehovah da Yesu suke da ita gare mu wajen ’yan’uwanmu Kirista? Ka lura da hanyoyi da yawa da za mu iya yin wannan: “Ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha; ƙauna ba ta jin kishi; ƙauna ba ta yin fahariya, ba ta yin kumbura, ba ta yin rashin hankali, ba ta biɗa ma kanta, ba ta jin cakuna, ba ta yin nukura, ba ta yin murna cikin rashin adalci, amma tana murna da gaskiya; tana jimrewa da abu duka, tana gaskata abu duka, tana kafa bege ga abu duka, tana daurewa da abu duka. Ƙauna ba ta ƙarewa daɗai.”—1 Korinthiyawa 13:4-8; 1 Yohanna 3:14-18; 4:7-12.

11. Ga su wanene kuma za mu nuna ƙauna, kuma ta yaya?

11 Ga wanene kuma za mu nuna ƙauna, kuma ta yaya? Yesu ya ce: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” (Matta 28:19, 20) Wannan ya ƙunshi gaya wa waɗanda ba ’yan’uwanmu Kiristoci ba bisharar sabuwar duniya ta aljanna ta Allah. Yesu ya nuna cewa bai kamata ƙaunarmu ta ƙare wajen waɗanda suke da imani ɗaya da mu ba, domin ya ce: “Idan kuna ƙaunar waɗanda ke ƙaunarku, wace lada ke gareku? ko masu-karɓan haraji ba haka su ke yi ba? Idan kuwa kuna gaida ’yan’uwanku kaɗai, ina kun fi waɗansu? ko Al’ummai ba haka su ke yi ba?”—Matta 5:46, 47; 24:14; Galatiyawa 6:10.

‘Yi Tafiya Cikin Sunan Jehovah’

12. Me ya sa sunan Allah ya dace da shi ne kaɗai?

12 Wani muhimmin fanni na girmama Allah na gaskiya shi ne ta sani, yin amfani, da kuma koya wa wasu sunansa mai girma, Jehovah. Mai Zabura ya furta muradin zuciyarsa: “Domin su sani kai, wanda sunanka Jehovah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.” (Zabura 83:18) Sunan nan Jehovah yana nufin “Yakan Sa Ya Kasance.” Shi ne Mai Ƙuduri Mai Girma, koyaushe yana sa ƙudurinsa ya cika. Allah na gaskiya ne kaɗai ya dace da wannan sunan, domin bil Adam ba su da tabbacin cewa ƙoƙarce-ƙoƙarcensu za su yi nasara. (Yaƙub 4:13, 14) Jehovah ne kaɗai zai iya cewa kalmarsa “za ta yi albarka” cikin abin da ya aike ta. (Ishaya 55:11) Mutane da yawa sun yi murna a lokaci na farko da suka ga sunan Allah cikin Littafi Mai Tsarki nasu kuma suka koyi abin da yake nufi. (Fitowa 6:3) Amma za su amfana daga wannan sanin idan suka yi ‘tafiya cikin sunan Jehovah . . . har abada abadin.’—Mikah 4:5.

13. Menene ke ƙunshe cikin sanin sunan Jehovah da kuma yin tafiya cikin sunansa?

13 Game da sunan Allah, Zabura 9:10 ta ce: “Waɗanda sun san sunanka za su dogara gareka.” Wannan ya ƙunshi fiye da sanin sunan Jehovah kawai, wanda ba ya nufin dogara da shi a take ba. Sanin sunan Allah yana nufin fahimtar irin Allah da Jehovah yake, nuna ladabi ga ikonsa, yin biyayya ga umurnansa, dogara gare shi a dukan abu. (Misalai 3:5, 6) Hakazalika, yin tafiya cikin sunan Jehovah yana nufin keɓe kai gare shi da kuma wakiltansa domin kana bauta masa, kana amfani da rayuwarka cikin jituwa da nufin Allah. (Luka 10:27) Kana yin haka?

14. Idan za mu bauta wa Jehovah har abada, me ake bukata ban da ra’ayin cewa hakki ne kawai?

14 Idan za mu bauta wa Jehovah har abada, kada mu yarda ra’ayin cika hakki kawai ya motsa mu. Manzo Bulus ya aririce Timothawus, wanda ya riga yana bauta wa Jehovah shekaru da yawa: “Ka wasa kanka zuwa ibada.” (1 Timothawus 4:7) Ibada tana fitowa ne daga zuciya da ta cika da godiya ga wanda ake wa ibadar. “Ibada” tana ba da ladabi da girma ga Jehovah ne kaɗai. Tana nuna soyayya ta ƙauna domin ɗaukaka mara iyaka gare shi kuma ga hanyoyinsa. Tana sa mu so kowa ya girmama sunansa sosai. Dole ne mu gina ibada a rayuwarmu idan muna so mu yi tafiya cikin sunan Jehovah, Allah makaɗaici na gaskiya har abada.—Zabura 37:4; 2 Bitrus 3:11.

15. Ta yaya za mu yi wa Allah cikakkiyar ibada?

15 Don Allah ya amince da sujjadarmu, dole ne ya kasance ba mu raba sujjadarsa ba, tun da yake shi “Allah mai-kishi ne.” (Fitowa 20:5) Ba za mu yi ƙaunar Allah sa’an nan kuma mu yi ƙaunar muguwar duniya da Shaiɗan ne allahnta ba. (Yaƙub 4:4; 1 Yohanna 2:15-17) Jehovah ya sani sarai irin mutumin da kowannenmu ke ƙoƙari ya zama. (Irmiya 17:10) Idan muna ƙaunar adalci, yana ganin wannan kuma zai taimake mu mu jimre wa gwajinmu na kowacce rana. Zai toƙara mana da ruhu mai tsarki nasa mai iko, zai sa mu yi nasara a kan mugunta da ke ko’ina a duniyar nan. (2 Korinthiyawa 4:7) Zai taimake mu kuma mu riƙe begenmu mai ƙarfi na rai na har abada a duniya ta aljanna. Lalle wannan zato ne mai girma! Ya kamata mu yi godiya ga wannan kuma mu yi sujjada da yardar rai ga Allah na gaskiya, Jehovah, wanda ya sa ya yiwu.

16. Me za ka so ka yi, tare da wasu miliyoyi?

16 Miliyoyin mutane a dukan faɗin duniya sun yi na’am da farin ciki ga gayyatar mai Zabura da ya rubuta: “Ku girmama Ubangiji tare da ni, bari kuma mu ɗaukaka sunansa tare.” (Zabura 34:3) Jehovah yana gayyatarka ka kasance tsakanin garke mai ci gaba a dukan al’ummai da suke girmama shi.

Maimaita Abin da Aka Tattauna

• Yaya Jehovah yake? Wane amfani muke samu ta fahimtar halayensa ƙwarai?

• Ta yaya za mu nuna ƙauna ga wasu?

• Menene ke ƙunshe cikin sanin sunan Jehovah da kuma yin tafiya cikin sunansa?

[Hotuna a shafi na 14]

Cikin ƙaunarsa mai girma, Jehovah zai ‘buɗe hannunsa ya biya wa kowane mai rai muradinsa’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba