Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wt babi na 18 pp. 159-166
  • “Ba na Duniya Su Ke Ba”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ba na Duniya Su Ke Ba”
  • Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Mulkina Ba na Wannan Duniya Ba Ne”
  • Almajiran Suna Bin Ja-Gorar Yesu
  • Kiristoci da Suka Riƙe Aminci Cikin Kwanaki na Ƙarshe
  • Tsakatsaki Na Kirista A Kwanaki Na Ƙarshe
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Shiga Harkokin Siyasa?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Ku Nisanta Kanku Daga Harkokin Wannan Duniyar da Babu Hadin Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Abin da Nisanta Kanmu Daga Harkokin Duniya Yake Nufi
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
wt babi na 18 pp. 159-166

Babi Na Goma Sha Takwas

“Ba na Duniya Su Ke Ba”

1. (a) Kafin mutuwarsa, menene Yesu ya yi addu’arsa domin almajiransa? (b) Me ya sa kasancewa “ba na duniya ba” ke da muhimmanci?

A DAR EN da za a kashe shi, Yesu ya yi addu’a domin almajiransa. Da sanin cewa Shaiɗan zai matsa musu ƙwarai, Yesu ya ce wa Ubansa: “Ba na yin addu’a ka ɗauke su daga cikin duniya ba, amma domin ka tsare su daga Mugun. Ba na duniya su ke ba, kamar yadda ni ba na duniya ba ne.” (Yohanna 17:15, 16) Me ya sa kasancewa a ware daga duniya yake da muhimmanci haka? Domin Shaiɗan ne mai mulkin wannan duniyar. Kiristoci ba za su so su zama na duniyar nan da ke cikin ikonsa ba.—Luka 4:5-8; Yohanna 14:30; 1 Yohanna 5:19.

2. A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya kasance ba na duniya ba?

2 Kasancewa ba na duniya ba ba ya nufin cewa Yesu ba ya ƙaunar wasu. Akasarin haka, ya warkar da masu ciwo, ya ta da matattu, ya koyar da Mulkin Allah ga mutane. Har ma ya ba da ransa domin bil Adam. Amma ba ya son halaye na rashin ibada da kuma ayyukan waɗanda suke nuna halin duniyar Shaiɗan. Saboda haka, ya yi gargaɗi game da sha’awoyin lalata, rayuwar son abin duniya, da kuma neman suna. (Matta 5:27, 28; 6:19-21; Luka 20:46, 47) Shi ya sa ba abin mamaki ba ne da Yesu kansa ya guji siyasar duniya. Ko da yake shi Bayahude ne, ya riƙe aminci game da jayayyar siyasa da ke tsakanin Romawa da Yahudawa.

“Mulkina Ba na Wannan Duniya Ba Ne”

3. (a) Wace tuhuma ce shugabannan addinin Yahudawa suka yi game da Yesu wajen Bilatus, kuma me ya sa? (b) Me ya nuna cewa bai so ya zama sarki ba?

3 Ka yi la’akari da abin da ya faru lokacin da shugabannan addinai suka kama Yesu kuma suka kai shi wajen Bilatus Ba-Bunti, gwamnan Roma. A hakikanin gaskiya, waɗannan shugabannan sun damu ne domin Yesu ya fallasa riyarsu. Domin su sa gwamnan ya hukunta Yesu, suka tuhume shi da cewa: “Muka iske wannan mutum yana ɓāta al’ummarmu, kuma yana hana bada gandu ga Kaisar, yana cewa shi da kansa Kristi ne, sarki.” (Luka 23:2) Wannan a bayyane yake cewa ƙarya ne, domin shekara guda da ta shige mutanen suka yi ƙoƙarin su mai da Yesu sarki, ya ƙi. (Yohanna 6:15) Ya san cewa zai zama Sarki a nan gaba a samaniya. (Luka 19:11, 12) Kuma, ba mutane ba ne za su ɗora shi kan gadon sarauta, amma Jehovah ne.

4. Menene halin Yesu game da biyan haraji?

4 Kwanaki uku kawai kafin a kama Yesu, Farisawan suka yi ƙoƙarin su sa Yesu ya faɗi wani abin da zai sa masa laifi game da al’amarin biyan haraji. Amma ya ce: “Gwada mini sule [na Romawa]. Yana da sura da rubutu na wanene?” Da suka ce “Na Kaisar ne,” ya amsa: “Abin da ke na Kaisar fa, ku bayar ga Kaisar; na Allah kuwa ku bayar ga Allah.”—Luka 20:20-25.

5. (a) Wane darasi ne Yesu ya koya wa almajiransa a lokacin da aka zo a kama shi? (b) Yaya Yesu ya bayyana dalilin abin da ya yi? (c) Menene sakamakon wannan gwajin?

5 A’a, Yesu bai koyar da yin tawaye ba ga masu iko na duniya. Lokacin da sojoji da wasu mutane suka zo su kama Yesu, Bitrus ya zaro takobi ya yanke kunnen wani mutum. Amma Yesu ya ce: “Mayar da takobinka gidansa: gama dukan waɗanda suka ɗauki takobi, da takobi za su lalace.” (Matta 26:51, 52) Washe gari Yesu ya bayyana abin da ya yi ga Bilatus, yana cewa: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne: da mulkina na wannan duniya ne, da ma’aikatana su a yi yaƙi, domin kada a bashe ni cikin hannun Yahudawa.” (Yohanna 18:36) Bilatus ya yarda cewa ‘babu dalilin tsare’ Yesu. Amma da taron malalata suka matsa masa, Bilatus ya sa aka rataye Yesu.—Luka 23:13-15; Yohanna 19:12-16.

Almajiran Suna Bin Ja-Gorar Yesu

6. Yaya Kiristoci na farko suka nuna suna guje wa halin duniya amma suna ƙaunar mutane?

6 Almajiran Yesu sun fahimci abin da kasancewa ba na duniya ba ke bukata. Yana nufin guje wa halin rashin ibada da kuma ayyuka na duniyar nan, da sun haɗa da nuna ƙarfi da nishaɗi na lalata irin da ake yi cikin babban gidan wasa na Roma. Domin haka, aka ce da almajiran maƙiyan mutane. Ba sa ƙin mutane, suna aiki tuƙuru su taimake wasu su amfana daga tanadin Allah don ceto.

7. (a) Saboda kasancewarsu ba na duniya ba, menene almajirai na farko suka fuskanta? (b) Yaya suka ɗauki masu mulki da kuma biyan haraji, kuma me ya sa?

7 An tsananta wa mabiyan Yesu yadda aka yi da shi, sau da yawa daga hannun hukumomi da aka yi musu ƙarya. Duk da haka, a shekara ta 56 A.Z., manzo Bulus ya rubuta zuwa ga Kiristoci a Roma, yana ariritarsu su “yi zaman biyayya da ikon masu-mulki [masarauta ta siyasa]: gama babu wani iko sai na Allah.” Ba cewa Jehovah ne ya kafa gwamnati ba, amma ya ƙyale su su kasance har sai lokacin da Mulkinsa zai mallaki dukan duniya. Daidai ne da Bulus ya aririci Kiristoci su daraja masu mulki kuma su biya haraji.—Romawa 13:1-7; Titus 3:1, 2.

8. (a) Har yaya Kiristoci za su yi biyayya ga masu mulki? (b) Ta yaya Kiristoci na farko suka bi misalin Yesu?

8 Amma, biyayya ga masu mulki kaɗan ne, ba gabaki ɗaya ba. Sa’ad da dokokin mutum suka saɓa wa na Allah, waɗanda suke bauta wa Jehovah ya kamata su yi biyayya ga dokokinsa. Ka lura da abin da littafin nan On the Road to Civilization—A World History ya ce game da Kiristoci na farko: “Kiristoci suka ƙi sa hannu cikin wasu harkoki na mazaunan Romawa. Kiristocin . . . sun ga shiga soja ƙaryata bangaskiyarsu ce. Ba sa ɗaukan wani matsayi na siyasa. Ba sa bauta wa daula.” Lokacin da majalisa ta Yahudawa ‘suka dokaci’ almajiran su daina wa’azi, suka amsa: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.”—Ayukan Manzanni 5:27-29.

9. (a) Me ya sa Kiristoci a Urushalima suka yi abin da suka yi a shekara ta 66 A.Z.? (b) A wace hanya ce wannan tafarki ne mai kyau?

9 Game da jayayya na siyasa da na sojoji, almajiran ba su sa hannu ba sam sam. A shekara ta 66 A.Z., Yahudawa a Yahudiya sun yi wa Kaisar tawaye. Nan da nan sojojin Roma suka kewaye Urushalima. Menene Kiristoci da suke cikin birnin suka yi? Suka tuna da gargaɗin Yesu cewa su fita daga birnin. Yayin da Romawa suka koma na ɗan lokaci, Kiristoci suka gudu zuwa ƙetaren Kogin Urdun zuwa cikin duwatsun Pella. (Luka 21:20-24) Riƙe amincinsu ya zama tafarki ga Kiristoci masu aminci daga baya.

Kiristoci da Suka Riƙe Aminci Cikin Kwanaki na Ƙarshe

10. (a) A cikin wane aiki ne Shaidun Jehovah suke shagala, kuma me ya sa? (b) Game da me suke riƙe aminci?

10 Tarihi ya nuna cewa wani rukuni a cikin kwanaki na ƙarshen nan sun iya riƙe aminci a yin koyi da Kiristoci na farko? E, Shaidun Jehovah sun yi haka. A wannan lokaci duka, sun ci gaba da yin wa’azi cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai iya kawo madawwamin salama, ni’ima, da kuma farin ciki ga masu ƙaunar adalci. (Matta 24:14) Amma game da jayayya da ke tsakanin al’ummai, suna riƙe aminci ƙwarai.

11. (a) Yaya riƙe amincin Shaidun ya bambanta daga ayyukan limamai? (b) Menene ra’ayin Shaidun Jehovah game da abin da wasu ke yi cikin siyasa?

11 Akasarin waɗannan, limamai na addinan wannan duniyar sun shagala cikin harkokin siyasa ƙwarai. A wasu ƙasashe, suna kamfen don wani ko kuma don a tumbuke wani. Har wasu limamai suna riƙe da matsayi na siyasa. Wasu sun matsa wa ’yan siyasa su goyi bayan wasu tsari da limaman suka yarda da shi. Amma Shaidun Jehovah ba sa sa hannu cikin siyasa. Ba sa ma hana mutane daga sa hannu a zancen siyasa, a neman matsayi, ko kuma su jefa ƙuri’a. Yesu ya ce almajiransa ba za su zama na duniya ba, saboda haka Shaidun Jehovah ba sa sa hannu cikin siyasa.

12. Menene ya faru saboda addinan wannan duniya ba su riƙe aminci ba?

12 Yadda Yesu ya annabta, al’ummai sau da yawa suna zuwa yaƙi. Har wasu dangogi tsakanin al’ummai sun yi yaƙi da juna. (Matta 24:3, 6, 7) Shugabannan addini sun goyi bayan wata al’umma ko kuma wani dangi gaba da ɗayan, suna ariritar mabiyansu su yi hakanan. Menene sakamakon? ’Yan addini suna kashe juna kawai domin bambancin al’umma ko kuma na ƙabila. Wannan ya saɓa da nufin Allah.—1 Yohanna 3:10-12; 4:8, 20.

13. Menene tabbaci ke nunawa game da tsaka-tsaki na Shaidun Jehovah?

13 Amma, Shaidun Jehovah suna tsaka-tsaki ƙwarai cikin dukan faɗace-faɗace. Hasumiyar Tsaro fitar 1 ga Nuwamba, 1939 (Turanci) ta ce: “Dukan waɗanda suke a gefen Ubangiji za su kasance a tsaka-tsaki wajen al’ummai da suke yaƙi.” Shaidun Jehovah a dukan al’ummai a dukan yanayi suna ci gaba da riƙe matsayinsu. Ba su ƙyale rabuwa ta siyasar duniya da yaƙe-yaƙe su lalata ’yan’uwancinsu na dukan ƙasashe ba. Sun “bubbuge takobansu su zama garmuna, māsunsu kuma su zama lauzuna.” Domin suna tsaka-tsaki, ba sa yin yaƙi.—Ishaya 2:3, 4; 2 Korinthiyawa 10:3, 4.

14. Saboda kasancewa da bambanci da duniya, menene Shaidun Jehovah suka fuskanta?

14 Menene wani sakamako na tsaka-tsakinsu? Yesu ya ce: “Domin ku ba na duniya ba ne, amma ni na zaɓe ku daga cikin duniya, . . . duniya tana ƙinku.” (Yohanna 15:19) An jefa Shaidun Jehovah da yawa cikin kurkuku domin su bayin Allah ne. An gana wa wasu azaba, wasu kuma an kashe su, makamancin abin da ya faru da Kiristoci na ƙarni na farko. Wannan domin Shaiɗan “allah na wannan zamani” ne yana hamayya da bayin Jehovah, waɗanda ba nasa ba.—2 Korinthiyawa 4:4; Ru’ya ta Yohanna 12:12.

15. (a) Zuwa ina ne dukan al’ummai suke nufa, kuma menene Shaidun Jehovah suke mai da hankali su guje wa? (b) Me ya sa ware kai daga duniya yake da muhimmanci?

15 Bayin Jehovah suna farin ciki cewa su ba na duniya ba ne, domin dukan al’ummai suna tafiya zuwa ƙarshensu a Armageddon. (Daniel 2:44; Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16; 19:11-21) Za mu guji irin wannan sakamakon saboda mun ware kanmu daga duniya. Mu mutane da muke da haɗin kai a duniya duka, muna da aminci ga Mulkin Allah na samaniya. Hakika, zama ba na duniya ba, muna ba da kanmu ga ba’a da kuma tsanantawa. Amma ba da jimawa ba, wannan zai ƙare, tun da wannan muguwar duniya da ke ƙarƙashin Shaiɗan za ta halaka har abada. A wata sassa, waɗanda suke bauta wa Jehovah za su rayu har abada cikin sabuwar duniyarsa ta adalci cikin Mulkin Allah.—2 Bitrus 3:10-13; 1 Yohanna 2:15-17.

Maimaita Abin da Aka Tattauna

• Yaya Yesu ya nuna cewa zama “ba na duniya ba” ya shafe shi?

• Menene halin Kiristoci na farko wajen (a) halin duniya? (b) masu mulkin, da kuma (c) biyan haraji?

• A waɗanne hanyoyi ne Shaidun Jehovah a wannan zamanin suke ba da tabbaci na tsaka-tsakinsu na Kirista?

[Hoto a shafi na 165]

Yesu ya bayyana cewa shi da mabiyansa “ba na duniya ba ne”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba