Babi Na Ashirin
Ka Yi Sauraron Ranar Jehovah
1. Da farko da ka koyi cewa ceto daga wahalar wannan tsohon zamani ya yi kusa, yaya ka ji?
ƊAYA cikin abubuwa na farko da ka koya daga Littafi Mai Tsarki shi ne cewa nufin Jehovah ne dukan duniya ta zama aljanna. A cikin sabuwar duniyar, ba za a ƙara ganin yaƙi, aikata laifi, talauci, ciwo, wahala, da mutuwa ba kuma. Matattu ma za su dawo. Bege ne mai ban sha’awa ƙwarai! Yadda wannan yake kusa kusa ya nuna tabbaci cewa sarautar Kristi da ba a gani ta soma a shekara ta 1914 kuma tun lokacin muna cikin kwanakin ƙarshe na wannan muguwar duniya. A ƙarshen waɗannan kwanaki na ƙarshe, Jehovah zai halaka wannan zamanin kuma ya kawo sabuwar duniyar da ya yi alkawarinta!
2. Mecece ‘ranar Jehovah’?
2 Littafi Mai Tsarki ya kira wannan lokacin halaka mai zuwa ‘ranar Jehovah.’ (2 Bitrus 3:10) “Ranar fushin Ubangiji” ne da dukan duniyar Shaiɗan. (Zephaniah 2:3) Zai kai iyakarsa a “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka. . . . da ake ce da shi da Ibrananci Har–Magedon [Armageddon],” inda za a halaka “sarakunan dukan duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16) Hanyar rayuwarka tana nuna ka tabbata cewa wannan ‘ranar Jehovah’ ta kusa?—Zephaniah 1:14-18; Irmiya 25:33.
3. (a) Yaushe ranar Jehovah za ta zo? (b) Yaya ya zama da amfani da Jehovah bai faɗi “ranan nan da sa’an nan ba”?
3 Littafi Mai Tsarki bai faɗa mana daidai lokacin da Yesu Kristi zai zo ya Zartar da hukunci na Jehovah a kan zamanin Shaiɗan ba. “Amma zancen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani, ko mala’iku cikin sama, ko Ɗan, sai Uban,” in ji Yesu. (Markus 13:32) Idan wani bai ƙaunaci Jehovah da gaske ba, zai saka ranarsa gefe guda kuma ya juya ga biɗan abin duniya. Amma waɗanda suke ƙaunar Jehovah da gaske za su bauta masa da zuciya ɗaya, ko da yaushe ƙarshen wannan zamanin zai zo.—Zabura 37:4; 1 Yohanna 5:3.
4. Menene gargaɗi da Yesu ya yi?
4 Da yake gargaɗi wa masu ƙaunar Jehovah, Yesu ya ce: “Ku yi lura, ku yi tsaro, . . . : gama ba ku san lokacinda sa’a ta ke ba.” (Markus 13:33-37) Ya aririce mu kada mu yarda wa ci da sha ko kuma “alhinin rai” su janye hankalinmu ainu da za mu kasa fahimtar lokaci da muke ciki.—Luka 21:34-36; Matta 24:37-42.
5. Kamar yadda Bitrus ya yi bayani, me ranar Jehovah za ta zo da shi?
5 Bitrus ma ya yi mana gargaɗi mu saurari “ranar Allah, [muna] kuwa marmarin zuwanta ƙwarai; bisa ga zuwanta kuwa sammai da su ke cin wuta za su narke, rundunan kuma za su narke da ƙuna mai-zafi.” Dukan gwamnatocin mutane—“sammai”—za a halaka, yadda zai faru ga jam’iyyar miyagun mutane gabaki ɗayanta—“duniya”—da “runduna,” ra’ayoyi da ayyuka na wannan muguwar duniya, kamar halayen neman ’yancin kai daga Allah da hanyoyin rayuwarta ta lalata da son abin duniya. Za a sake waɗannan da “sababbin sammai [Mulkin Allah na samaniya] da sabuwar duniya [sabuwar jam’iyyar mutane], inda adalci ya ke zaune.” (2 Bitrus 3:10-13) Waɗannan aukuwa da za su birkita duniya, za su fara farat ɗaya ne a rana da sa’ar da ba a yi tsammani ba.—Matta 24:44.
Ka Kasance a Farke ga Alamar
6. (a) Amsar Yesu ga tambayar almajiransa har yaya ne ta shafi ƙarshen zamanin Yahudawa? (b) Wane ɓangaren amsar Yesu ne ya mai da hankali a kan aukuwa da kuma halaye daga shekara ta 1914 zuwa gaba?
6 Domin irin lokaci da muke ciki, ya kamata mu sarƙu da daki-dakin haɗaɗiyar alama da ta nuna wannan kwanaki na ƙarshe—“cikar zamani.” Ka tuna cewa lokacin da Yesu ya ba da amsar tambayar da ke a Matta 24:3 ga almajiransa, wasu abubuwan da ya kwatanta a ayoyi 4 zuwa 22 sun ɗan cika a zamanin Yahudawa tsakanin shekara ta 33 da ta 70 A.Z. Amma annabcin ya samu cikarsa mai girma tun shekara ta 1914, lokacin ‘bayyanuwar [Kristi] da ƙarshen zamanin.’ Matta 24:23-28 ta faɗi game da abin da zai faru daga shekara ta 70 A.Z. zuwa lokacin bayyanuwar Kristi. Aukuwa da aka kwatanta a Matta 24:29–25:46 za ta faru a lokaci na ƙarshe ne.
7. (a) Me ya sa ya kamata mu ma mu kasance a farke ga yadda yanayin abubuwa na yanzu ke cika alamar? (b) Ka amsa tambayoyi da ke a ƙarshen wannan izifi, ka nuna yadda wannan alamar ta cika tun daga shekara ta 1914.
7 Mu kanmu ya kamata mu lura da aukuwa da kuma halayen da suke cika alamar. Haɗa waɗannan abubuwa da annabcin Littafi Mai Tsarki zai taimake mu mu saurari ranar Jehovah. Yana taimakonmu kuma mu kasance da rinjaya yayin da muke gargaɗi wasu game da yadda wannan rana take kusa. (Ishaya 61:1, 2) Tunawa da waɗannan, bari mu maimaita tambayoyi na gaba da suka nanata ɓangaren alamar, yadda suke a Matta 24:7 da Luka 21:10, 11.
A wace hanya ce musamman ‘al’umma ta tasam wa al’umma mulki kuma ta tasam wa mulki’ ta soma cika a shekara ta 1914? Game da yaƙe-yaƙe, menene ya faru tun lokacin?
A shekara ta 1918, wace annoba ce ta ci rayuka da ta ɗara na Yaƙin Duniya na I? Duk da ilimin mutum na magunguna, waɗanne cututtuka ne har yanzu suke kashe miliyoyi?
Yaya ne karancin abinci ya shafi duniya duk da ci gaban kimiyya a ƙarnin da ya shige?
Menene ya tabbatar maka cewa 2 Timothawus 3:1-5, 13 suna kwatanta ba yadda rayuwa take ba, ko da yaushe, amma yadda yanayi ke daɗa muni yayin da muke kusa da kwanaki na ƙarshe?
Ware Mutane
8. (a) Menene kuma da aka kwatanta a Matta 13:24-30, 36-43 da Yesu ya haɗa shi da ƙarshen zamani? (b) Mecece almarar Yesu take nufi?
8 Da akwai wasu aukuwa na musamman da Yesu ya haɗa su da ƙarshen wannan zamanin. Ɗaya cikinsu shi ne ware “ ’ya’yan mulki” daga “ ’ya’yan Mugun.” Yesu ya faɗa wannan cikin almararsa na gonar alkama da wani maƙiyi ya shuka da zawa. “Alkama” ta almararsa tana wakilta Kiristoci shafaffu na gaskiya. “Zawan” waɗanda suke da’awar su Kiristoci ne amma sun nuna kansu “ ’ya’yan Mugun” domin sun manne wa duniya, wadda Iblis ne mai mulkinta. An ware waɗannan daga “ ’ya’yan mulki [na Allah]” kuma an ajiye su don halaka. (Matta 13:24-30, 36-43) Wannan ya riga ya faru ne?
9. (a) Bayan Yaƙin Duniya na I, wane aikin ware dukan waɗanda suke da’awar su Kiristoci ne ya auku? (b) Yaya Kiristoci shafaffu suka nuna su bayin Mulkin ne da gaske?
9 Bayan Yaƙin Duniya na I, aka ware dukan waɗanda suke da’awar su Kirista ne cikin azuzuwa biyu: (1) Limaman Kiristendam da mabiyansu da suka fito su ba da goyon baya ƙwarai ga Haɗin Kan Al’ummai (yanzu Majalisar Ɗinkin Duniya) yayin nan kuma suna riƙe amincinsu ga ƙasa, na (2) Kiristoci na bayan yaƙin, da suka ba da goyon baya sosai ga Mulkin Almasihu, ba ga al’ummai na wannan duniyar ba. (Yohanna 17:16) Waɗannan sun nuna kansu cewa su bayin Mulkin Allah ne ta yin wa’azin “wannan bishara ta mulki” a duk faɗin duniya. (Matta 24:14) Menene sakamakon haka?
10. Menene sakamako na farko a aikin wa’azi na Mulki?
10 Da farko, an tattara raguwa na waɗanda aka shafe da ruhun Allah, waɗanda suke da begen kasancewa tare da Kristi a zama sashe na Mulki na samaniya. Ko da yake waɗannan a watse suke cikin al’ummai, an kawo su cikin haɗin kai na ƙungiya. Hatimcewa na ƙarshe na waɗannan shafaffu ya yi kusa.—Ru’ya ta Yohanna 7:3, 4.
11. (a) Wane aikin tattarawa ne yake ci gaba, kuma a jituwa da wane annabci? (b) Mecece cikar wannan annabci ke nunawa?
11 Sai kuma a ƙarƙashin ja-gorar Kristi, aka soma tattara “taro mai-girma . . . daga cikin kowane iri, da dukan ƙabilai da al’ummai da harsuna.” Waɗannan suka zama “waɗansu tumaki” da za su tsira daga “babban tsananin” zuwa sabuwar duniya ta Allah. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14; Yohanna 10:16) Wannan aiki na wa’azin Mulkin Allah kafin ƙarshen ya zo ya ci gaba zuwa wannan lokaci. Da aminci, taro mai girma na waɗansu tumaki, da yanzu sun kai miliyoyi, suna taimakon raguwar shafaffun su sanar da wannan saƙo mai muhimmanci na Mulki. Ana jin wannan saƙon a dukan al’ummai.
Me Zai Faru a Nan Gaba?
12. Yaya yawan aikin wa’azin da ya rage yake kafin ranar Jehovah ta zo?
12 Dukan waɗannan abubuwa na baya suna nuna cewa mun kusa da ƙarshen kwanaki na ƙarshe kuma cewa ranar Jehovah ta kusa. Amma akwai annabce-annabce ne har ila da za su cika kafin ranar razana ta soma? E. Abu ɗaya shi ne, ba a gama ware mutane ba tukuna a batun Mulkin. A wasu hanyoyi ana shan hamayya mai tsanani na shekaru da yawa, amma yanzu an sami ƙari a sababbin almajirai. Har a inda mutane suke ƙin bisharar ma, a bayyane jinƙan Jehovah yake ta wurin wa’azin da muke yi. Saboda haka, mu ci gaba da aikin! Yesu ya tabbatar mana cewa idan aikin ya ƙare, ƙarshen zai zo.
13. Kamar yadda aka rubuta a 1 Tassalunikawa 5:2, 3, wace aukuwa ta musamman ce za ta faru, kuma me wannan za ta nufa a gare mu?
13 Wani annabcin Littafi Mai Tsarki na musamman ya ce: “Suna cikin faɗin, Kwanciyar rai da lafiya, sai ga halaka farat ta auko musu, kamar yadda faya ta kan auko ma mace mai-ciki; ba kuwa za su tsira ba ko kaɗan.” (1 Tassalunikawa 5:2, 3) Yadda wannan shelar “kwanciyar rai da lafiya” za ta auku fa ba a sani ba tukuna. Amma lallai ba zai zama cewa shugabannan duniya sun magance matsalolin mutane ba. Waɗanda suke sauraron ranar Jehovah ba za su ruɗe da wannan shelar ba. Sun sani cewa ba zai daɗe ba, halaka farat za ta auko.
14. Wace aukuwa ce za ta auku a lokacin ƙunci mai girma, yaya tsarin zai zama?
14 A somawar ƙunci mai girma, masu sarauta za su yi gaba da Babila Babba, daular duniya na addinin ƙarya, kuma za su halaka ta. (Matta 24:21; Ru’ya ta Yohanna 17:15, 16) Bayan haka, al’ummai za su juya ga waɗanda suke goyon bayan ikon mallaka na Jehovah, suna tsokanar fushin Jehovah a kan gwamnatoci na siyasa da masu goyon bayansu, yana kawo halakarsu gabaki ɗaya. Daga ƙunci mai girma, wannan ne zai zama abin da Armageddon zai kammala. Sai a saka Shaiɗan a rami, ba zai iya rinjayar mutane kuma ba. Wannan zai kammala ranar Jehovah da za a ɗaukaka sunansa.—Ezekiel 38:18, 22, 23; Ru’ya ta Yohanna 19:11–20:3.
15. Me ya sa ba hikima ba ce mu yi tunani cewa ranar Jehovah tana da nisa?
15 Ƙarshen wannan tsarin zai zo a daidai lokaci, yadda Allah ya tsara. Ba zai makara ba. (Habakkuk 2:3) Ka tuna, halakar Urushalima a shekara ta 70 A.Z. ta zo da sauri, lokacin da Yahudawa ba su yi tsammaninta ba, lokacin da suke jin babu wani haɗari. Babila ta dā kuma fa? Ƙaƙƙarfa ce, da gaba gaɗi, da garu masu ƙwari. Amma a dare ɗaya ta halaka. Hakanan, halaka ta farat ɗaya za ta zo a kan wannan mugun zamani. Idan ya faru, bari a iske mu cikin haɗin kai a bauta ta gaskiya, bayan mun saurari ranar Jehovah.
Maimaita Abin da Aka Tattauna
• Me ya sa yake da muhimmanci mu saurari ranar Jehovah? Yaya za mu yi wannan?
• Yaya aikin ware mutane da ake yi yake shafan mu?
• Me har ila zai faru a nan gaba kafin ranar Jehovah ta soma? Saboda haka, menene ya kamata mu kanmu mu riƙa yi?
[Hotuna a shafi na 180, 181]
Ba da daɗewa ba kwanaki na ƙarshe zai ƙare a halaka zamanin Shaiɗan