Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • kn37 pp. 1-4
  • Ƙarshen Addinin Ƙarya Ya Kusa!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ƙarshen Addinin Ƙarya Ya Kusa!
  • Ƙarshen Addinin Ƙarya Ya Kusa!
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Addinin Ƙarya  . . .
  • Addini na Gaskiya . . .
  • Yadda Addinan Karya Suke Bata Sunan Allah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Allah Ya Yarda da Dukan Addinai Ne?
    Hanyar Rai Madawwami​—Ka Same ta Kuwa?
  • Ka Ƙi Addinin Ƙarya!
    Za Ka Iya Zama Aminin Allah!
  • Ka Guji Bautar Ƙarya!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Ƙarshen Addinin Ƙarya Ya Kusa!
kn37 pp. 1-4

Bisharar Mulki lamba na 37

Saƙo Ga Dukan Duniya

Ƙarshen Addinin Ƙarya Ya Kusa!

▪ Menene addinin ƙarya?

▪ Ta yaya zai zo ƙarshensa?

▪ Ta yaya zai shafe ka?

Menene addinin ƙarya?

Kana baƙin ciki domin laifi da ake yi a madadin addini? Yaƙe-yaƙe, ta’addanci da kuma ɓatanci da waɗanda suke da’awar suna bauta wa Allah suke yi yana damun yadda kake ji game da abin da ke daidai? Me ya sa addini ke haddasa matsaloli da yawa?

Laifin ba na dukan addinai ba ne amma na addinin ƙarya. Yesu Kristi, da addini masu suke daraja ya nuna cewa addinin ƙarya na sa a yi munanan ayyuka, kamar yadda “ɓātacen itace ya kan fitarda munanan ’ya’ya.” (Matta 7:15-17) Addinin ƙarya yakan sa a yi waɗanne irin ayyuka?

Addinin Ƙarya  . . .

◼ NA SAKA HANNU A YAƘE-YAƘE DA SIYASA: Jaridar Asiaweek ta ce: “A cikin Asiya da kuma wasu wurare, shugabannai masu neman iko suna sarrafa ra’ayin mutane game da addini yadda bai dace ba don su biya nasu bukatu.” Saboda haka, wannan jaridar ta ba da kashedi: “Kamar dukan duniya ta kusan haukacewa.” Wani sanannen shugaban addini a Amirka ya ce: “Sai an kashe ’yan ta’ada kafin kashe-kashe ya ƙare.” Yaya za a yi wannan in ji shi. “A halaka su duka cikin sunan Ubangiji.” Amma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan wani ya ce, Ina ƙaunar Allah, shi kuwa yana ƙin ɗan’uwansa, maƙaryaci ne shi.” (1 Yohanna 4:20) Yesu ma ya ce: ‘Ku ci gaba da ƙaunar magabtanku.’ (Matta 5:44) Addinai nawa ne ka sani suke saka hannu a yaƙe-yaƙe?

◼ NA YAƊA KOYARWAN ƘARYA: Yawancin addinai sun koyar da cewa kurwa ko kuma ruhu wani ɓangare ne na jikin ’yan adam marar ganuwa da ke ci gaba da rayuwa bayan mutuwa. Ta wannan koyarwa, addinai da yawa suna karɓan kuɗi daga mabiyansu don su yi wa kurwar addu’a. Amma, abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa dabam ne. ‘Mai-rai da ya yi zunubi, shi za ya mutu.’ (Ezekiel 18:4) “Masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san komi ba.” (Mai-Wa’azi 9:5) Yesu ya koyar da cewa za a ta da matattu, wannan ba zai kasance da amfani ba idan ’yan adam suna da kurwa marar mutuwa. (Yohanna 11:11-25) Addininka yana koyar da cewa kurwa ba ta mutuwa?

◼ YA AMINCE DA LALATA: A wasu ƙasashe, rukunin coci suna naɗa ’yan luwaɗi da ’yar maɗigo limamai kuma suna ariritar gwamnati ta yarda ’yan luwaɗi su auri juna, ’yar maɗigo su ma su auri juna. Har coci da suka la’anta lalata sun ƙyale shugabanan addinai da suka yi lalata da yara. Amma menene Littafi Mai Tsarki yake koyarwa? Ya faɗi sarai: ‘Kada ku yaudaru; da masu-fasikanci, da masu-bautan gumaka, da mazinata, da baran mata, da masu-kwana da maza . . . ba za su gāji mulkin Allah ba.’ (1 Korinthiyawa 6:9, 10) Ka san addinai da suke rufe idanunsu ga lalata?

Menene zai faru a nan gaba da addinai da ke yin miyagun ayyuka? Yesu ya yi gargaɗi: “Kowane itacen da ba ya fito da ’ya’yan kirki ba a kan sare shi, a jefa a wuta.” (Matta 7:19) Hakika, za a sare addinin ƙarya kuma a halaka shi! Amma ta yaya wannan zai faru, kuma yaushe? Wahayi na annabci da ke rubuce cikin littafin Ru’ya ta Yohanna, surori 17 da 18, ya ba da amsa.

Ta yaya addinin ƙarya zai zo ƙarshensa?

Ka yi tunanin wannan yanayin. Karuwa tana zaune a kan dabba mai ban tsoro. Dabbar tana da kawuna bakwai da ƙahoni goma. (Ru’ya ta Yohanna 17:1-4) Wacece karuwar take wakilta? Tana rinjayar “sarakunan duniya.” Ta saka tufa shunayya, tana amfani da turaren wuta, kuma tana da arziki ƙwarai. Ƙari ga haka,‘dukan al’ummai’ sun ruɗe ta wurin ayyukanta na sihiri. (Ru’ya ta Yohanna 17:18; 18:12, 13, 23) Littafi Mai Tsarki ya sa mu fahimci cewa wannan karuwa ƙungiyar addini ne na dukan duniya. Ba addini ɗaya kawai take wakilta ba, amma dukan addinai da ke aikata miyagun ayyuka.

Dabba da karuwar ke zaune a kai tana wakiltan masu sarauta na duniya.a (Ru’ya ta Yohanna 17:10-13) Addinin ƙarya na zaune bayan wannan dabba ta siyasa, yana ƙoƙarin rinjayar shawarwarinta da kuma ya yi mata ja-gora.

Amma ba da daɗewa ba, wani abu na ban mamaki zai faru. “Ƙahoni gomaɗin kuma da ka gani, da bisan, za su ƙi karuwan, su lalatadda ita su tsiraitadda ita kuma, za su cinye namanta, su ƙoƙone ta sarai da wuta.” (Ru’ya ta Yohanna 17:16) Farat ɗaya, masu sarauta na duniya za su kai wa addinin ƙarya hari kuma su halaka shi gabaki ɗaya! Menene zai motsa su su yi hakan? Littafin Ru’ya ta Yohanna ya ba da amsar: ‘Allah ya sa cikin zuciyarsu su yi nufinsa.’ (Ru’ya ta Yohanna 17:17) Hakika, Allah zai kama addinin ƙarya da alhakin dukan ayyukan mugunta da ya yi cikin sunansa. Wajen zartar da cikakkiyar shari’a, zai yi amfani da abokanta na siyasa ya zartar da hukunci.

Menene za ka yi idan ba ka son abin da zai faru da addinin ƙarya ya shafe ka? Manzon Allah ya aririta: “Ku fito daga cikinta, ya al’ummata.” (Ru’ya ta Yohanna 18:4) Hakika, yanzu lokaci ne da za ka guji addinin ƙarya! Ina za ka gudu ka je? Ba zuwa addinin rashin yarda da wanzuwar Allah ba, tun da shi ma ba shi da begen tsira. (2 Tassalunikawa 1:6-9) Mafaka ta gaske da muke da ita, ita ce addini na gaskiya. Ta yaya za ka san addinin gaskiya?

Yadda za a gane addini na gaskiya

Waɗanne kyawawan ’ya’ya ya kamata addini na gaskiya ya haifi?—Matta 7:17.

Addini na Gaskiya . . .

◼ NA NUNA ƘAUNA: Masu bauta ta gaskiya “ba na duniya” suke ba, ƙabilanci ko kuma al’ada ba ya raba su, kuma suna nuna ‘ƙauna ga junansu.’ (Yohanna 13:35; 17:16; Ayukan Manzanni 10:34, 35) Maimakon su kashe juna, suna a shirye su mutu domin juna idan bukata ta kama.—1 Yohanna 3:16.

◼ YA GASKATA KALMAR ALLAH: Maimakon ya koyar da ‘takalidu’ da kuma “koyarwa [na] dokokin mutane,” addini na gaskiya na koyarwarsa bisa Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki. (Matta 15:6-9) Me ya sa? Domin “kowane nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa.” —2 Timothawus 3:16.

◼ YANA ƘARFAFA IYALAI KUMA YANA ƊAUKAKA MIZANAN ƊABI’A MAI GIRMA: Addini na gaskiya na koya wa magidanta su ‘yi ƙaunar matansu kamar jikunansu,’ yana taimakon mata su ‘ladabta wa mazansu,’ kuma yana koya wa yara su ‘yi biyayya da iyayensu.’ (Afisawa 5:28, 33; 6:1) Ƙari ga haka, dole ne waɗanda suke da hakki su zama abin koyi.—1 Timothawus 3:1-10.

Da akwai addini da yake bin waɗannan mizanai kuwa? Littafin nan Holocaust Politics, da aka wallafa a shekara ta 2001 ya ce: “Idan ƙarin mutane suna bin abin da Shaidun Jehobah suke wa’azinsa kuma suke yi, da ba a yi halaka ba kuma kisan ƙare-ɗangi da ya dami duniya ba zai kasance ba.”

Hakika, a ƙasashe 235, Shaidun Jehobah suna wa’azin mizanan ɗabi’a na Littafi Mai Tsarki kawai kuma suna rayuwa daidai da shi. Muna ariritarka ka gaya wa Shaidun Jehobah su taimake ka ka koyi abin da Allah ke bukata a gareka domin ka bauta masa a hanyar da ya amince da ita. Ya kamata ka aikata yanzu. Kada ka ɓata lokaci. Ƙarshen addinin ƙarya ya kusa!—Zephaniah 2:2, 3.

Idan kana son ƙarin bayani game da saƙon Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah suke wa’azinsa, kada ka yi jinkirin magana da su a yankinku.

Idan za ka so wani ya zo gidanka, don Allah ka cika fom da yake ƙasa kuma ka aika ga adireshi da ke ƙasa.

□ Don Allah ku neme ni don nazarin Littafi Mai Tsarki na gida kyauta.

[Hasiya]

a Don bayani dalla-dalla a kan wannan batun, ka duba littafin nan Revelation—Its Grand Climax At Hand! Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Bayanin da ke shafi na 3]

“Ku fito daga cikinta, ya al’ummata”

[Bayanin da ke shafi na 3]

Addinin ƙarya na rinjayar “sarakunan duniya”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba