Ka Guji Bautar Ƙarya!
“Ku fito daga cikinsu, ku ware, in ji Ubangiji, Kada ku taɓa kowane abu marar-tsarki.”—2 KORINTHIYAWA 6:17.
1. A wane yanayi na ruhaniya sahihan mutane da yawa suka iske kansu?
MUTANE da yawa ba su san gaskiya game da Allah ba da kuma abin da ’yan adam za su fuskanta a nan gaba. Da yake ba su sami amsoshi game da damuwarsu na ruhaniya ba, sun rikice kuma ba su san na yi ba. Mutane miliyoyi sun zama bayi ga camfi, al’adu, da bukukuwa da suke ɓata wa Mahaliccinmu rai. Mai yiwuwa, kana da maƙwabta da dangi da suka gaskata da wutar jahannama, allah-uku-cikin ɗaya, kurwa marar mutuwa, da wasu koyarwar ƙarya.
2. Menene shugabannan addinai suka yi, da wane sakamako?
2 Me ya sa mutane da yawa ba su san Allah ba? Abin mamaki, addini ne ya sa, musamman ƙungiyar addinai da shugabannai da suke ɗaukaka ra’ayi da ya saɓa da na Allah. (Markus 7:7, 8) Saboda haka, an yaudari mutane da yawa suka gaskata cewa suna bauta wa Allah na gaskiya, amma ainihi ɓata masa rai suke yi. Addinin ƙarya yana da hannu kai tsaye don wannan mummunan yanayi.
3. Wanene ainihi yake ɗaukaka addinin ƙarya, yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta shi?
3 Da akwai halitta marar ganuwa da ke goyon bayan addinin ƙarya. Manzo Bulus ya ce game da shi: “Allah na wannan zamani ya makantadda hankulan marasa-bada gaskiya, domin kada hasken bisharar darajar Kristi, wanda shi ke surar Allah, ya waye musu.” (2 Korinthiyawa 4:4) Shaiɗan Iblis ne “allah na wannan zamani.” Shi ne ainihi mai ɗaukaka bautar ƙarya. Bulus ya rubuta: “Shaiɗan da kansa ya kan mayarda kansa kamar mala’ika na haske. Ba wani abu ne fa masu-hidimansa kuma su mayarda kansu masu-hidiman adalci.” (2 Korinthiyawa 11:14, 15) Shaiɗan yana sa munanan abubuwa su zama masu kyau kuma yana yaudarar mutane su gaskata ƙarya.
4. Menene Dokar Allah ga Isra’ila ta dā ta ce game da annabawan ƙarya?
4 Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya haramta addinin ƙarya. Alal misali, Dokar Musa ta gargaɗi mutane da Allah ya zaɓa su guje wa annabawan ƙarya. Kowanne mutum da yake ɗaukaka koyarwa da ba ta gaskiya ba ce da kuma bautar allolin ƙarya “za a kashe shi; domin ya yi zancen tayarwa ga Ubangiji.” An umurci Isra’ilawa su ‘kawarda mugunta daga cikinsu.’ (Kubawar Shari’a 13:1-5) Hakika, Jehobah ya ɗauki addinin ƙarya a matsayin mugunta.—Ezekiel 13:3.
5. Wane gargaɗi ya kamata mu yi biyayya da shi a yau?
5 Yesu Kristi da manzanninsa sun nuna yadda Jehobah yake ji game da addinin ƙarya. Yesu ya gargaɗi almajiransa: “Ku yi hankali da masu-ƙaryan annabci, masu-zuwa wurinku da fatar tumaki, amma daga ciki kerketai ne masu-hauka.” (Matta 7:15; Markus 13:22, 23) Bulus ya rubuta cewa “fushin Allah ya bayana daga sama bisa dukan rashin ibada da rashin adalci na mutane, masu-danne gaskiya cikin rashin adalci.” (Romawa 1:18) Yana da muhimmanci Kiristoci na gaskiya su yi biyayya ga wannan gargaɗin kuma su guje wa duk wanda ke hana mutane sanin gaskiyar Kalmar Allah ko kuma yake yaɗa koyarwar ƙarya!—1 Yohanna 4:1.
Ka Guje wa “Babila Babba”
6. Ta yaya aka kwatanta “Babila Babba” a cikin Littafi Mai Tsarki?
6 Ka yi la’akari da yadda littafin Ru’ya ta Yohanna ya kwatanta addinin ƙarya. Littafin ya kwatanta cewa karuwa ce da ta yi maye da take da iko bisa mulkoki da yawa da mutanensu. Wannan mata ta alama ta yi fasikanci da sarakuna da yawa kuma ta yi maye da jinin masu bauta ta gaskiya ga Allah. (Ru’ya ta Yohanna 17:1, 2, 6, 18) An rubuta suna a goshinta da ya yi daidai da halinta na ƙazanta mai ban ƙyama. Sunan shi ne “Babila Babba, uwar karuwai da abubuwa masu ban ƙyama na duniya.”—Ru’ya ta Yohanna 17:5.
7, 8. Ta yaya addinin ƙarya ya yi karuwanci, da wane sakamako?
7 Yadda Nassi ya kwatanta Babila Babba ya yi daidai da rukunin addinan ƙarya na duniya. Ko da yake addinai da yawa ba sa cikin ƙungiyar addini ɗaya na duniya, amma, duk kanwar ja ce domin nufinsu da kuma ayyukansu ɗaya ne. Yadda malalaciya a littafin Ru’ya ta Yohanna ta kwatanta, addinin ƙarya na rinjayar gwamnatoci sosai. Kamar matar da ba ta kasance da aminci ga wa’adinta na aure ba, addinin ƙarya ya yi karuwanci ta wajen hulɗa da rukunin siyasa da yawa. Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Ku mazinata, ba ku sani ba abutar duniya magabtaka ce da Allah? Dukan wanda ya ke so shi zama abokin duniya fa yana maida kansa magabcin Allah.”—Yaƙub 4:4.
8 Haɗa addinin ƙarya da siyasa ya kawo wahala sosai ga ’yan adam. Dokta Xolela Mangcu, mai nazarin siyasa na Afirka ya lura cewa “tarihin duniya ya cika da misalan mutane da aka kashe su babu gaira, wanda addini da siyasa ne suka jawo hakan.” Wata jarida ta kwanan nan ta ce: “Jayayyar da aka fi kisa kuma wadda ta fi haɗari a yau . . . na da nasaba da addini.” An kashe mutane miliyoyi a yaƙe-yaƙe da addini ke goyon bayansa. A alamance Babila Babba ta yi maye da jinin bayin Allah, domin ta tsananta musu kuma ta kashe su.—Ru’ya ta Yohanna 18:24.
9. Ta yaya aka furta ƙiyayyar Jehobah ga bautar ƙarya a littafin Ru’ya ta Yohanna?
9 Abin da zai faru da Babila Babba ya nuna cewa Jehobah ya tsane bautar ƙarya. Ru’ya ta Yohanna 17:16 ta ce: “Ƙahoni gomaɗin kuma da ka gani, da bisan, za su ƙi karuwan, su lalatadda ita su tsiraitadda ita kuma, za su cinye namanta, su ƙoƙone ta sarai da wuta.” Na farko, babban bisan zai maƙure ta kuma ya cinye namanta. Sa’an nan, za a ƙone raguwarta sarai da wuta. Hakanan ma, ba da daɗewa ba gwamnatin duniya za ta ɗauki irin wannan matakin a kan addinin ƙarya. Allah zai motsa su su yi hakan. (Ru’ya ta Yohanna 17:17) An kusa halaka Babila Babba, wato, daular duniya na addinin ƙarya. “Ba kuwa za a ƙara ganinta ba.”—Ru’ya ta Yohanna 18:21.
10. Menene ya kamata ya zama matsayinmu game da addinin ƙarya?
10 Wane matsayi ne game da Babila Babba ya kamata masu bauta na gaskiya su kasance ciki? A kalmomi da ya fita sarai, Littafi Mai Tsarki ya ba da umurni: “Ku fito daga cikinta, ya al’ummata, domin kada ku yi tarayya da zunubanta, kada ku sha rabon annobanta.” (Ru’ya ta Yohanna 18:4) Dole ne waɗanda suke so su tsira su fito daga addinin ƙarya kafin ya makara ainun. Sa’ad da yake duniya, Yesu Kristi ya annabta cewa a kwanaki na ƙarshe, mutane da yawa za su yi da’awa suna bin sa. (Matta 24:3-5) Zai gaya wa irin waɗannan: “Ban taɓa saninku ba daɗai: rabu da ni, ku masu-aika mugunta.” (Matta 7:23) Yesu Kristi, Sarki da ke sarauta yanzu ya ƙi addinin ƙarya.
Yadda Za Ka Guje Ta
11. Menene ya kamata mu yi don mu guje wa addinin ƙarya?
11 Kiristoci na gaskiya sun guji bautar ƙarya ta wajen ƙin koyarwar addinan ƙarya. Wannan yana nufin cewa ba za mu saurari tsarin ayyuka na addini a kan rediyo da talabijin ba, kuma ba za mu karanta littattafai na addini da ke yaɗa ƙarya game da Allah da kuma Kalmarsa ba. (Zabura 119:37) Zai yi kyau kada mu sa hannu a taro da kuma ayyukan nishaɗi da ƙungiya da ke tarayya da addinin ƙarya ta shirya. Ƙari ga haka, ba za mu tallafa wa bautar ƙarya a kowace hanya ba. (1 Korinthiyawa 10:21) Ƙin waɗannan abubuwa na kāre mu “kada kowa shi same [mu] ta wurin iliminsa da ruɗinsa na banza, bisa ga tadar mutane, bisa ga ruknai na duniya, ba bisa ga Kristi ba.”—Kolossiyawa 2:8.
12. Ta yaya mutum zai yanke kowace tarayya da ƙungiya ta addinin ƙarya?
12 Idan har ila sunan wani da yake son ya zama Mashaidin Jehobah na cikin rajistan addinin ƙarya kuma fa? A irin wannan yanayi, mutumin zai rubuta wasiƙa da ta nuna cewa ba ya son ya kasance cikin wannan addinin ƙarya kuma. Yana da muhimmanci sosai wannan mutumin ya ɗauki mataki ya guji kowane irin gurɓacewa na bautar ƙarya. Ya kamata ayyukan wanda yake son ya zama Mashaidi ya nuna wa ƙungiyar addinin da masu lura sarai cewa ya daina sha’ani da addinin.
13. Wane gargaɗi ne Littafi Mai Tsarki ya ba da game da guje wa bautar ƙarya?
13 Manzo Bulus ya rubuta: “Kada ku yi karkiya marar-dacewa tare da marasa-bangaskiya, gama wace zumunta ke tsakanin adalci da zunubi? Ko kuwa wace tarayya haske ya ke da duhu? Kuma ina magamin Kristi da Belial? Ina rabon mai-bada gaskiya kuma wurin marar-bada gaskiya? Ina gamin haikalin Allah da gumaka? . . . Domin wannan, ku fito daga cikinsu, ku ware, in ji Ubangiji, kada ku taɓa kowane abu mara-tsarki.” (2 Korinthiyawa 6:14-17) Muna biyayya da waɗannan kalmomin ta wajen guje wa bautar ƙarya. Gargaɗin Bulus yana bukatar mu guje wa masu bautar ƙarya ne?
“Ku Yi Tafiya Cikin Hikima”
14. Dole ne mu guje wa waɗanda suke bautar ƙarya gabaki ɗaya? Ka ba da bayani.
14 Ya kamata masu bauta ta gaskiya su daina kowane sha’ani da waɗanda suke bin bautar ƙarya? Shin ya kamata mu ƙi kowace tarayya da waɗanda ba sa bin imaninmu? A’a. Doka ta biyu cikin manyan dokoki biyu ta ce: “Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Matta 22:39) Muna ƙaunar maƙwabtanmu sa’ad da muke musu wa’azin bisharar Mulki. Muna kuma ƙaunarsu sa’ad da muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su da kuma sanar da su bukatar su guje wa bautar ƙarya.
15. Menene yake nufi mu kasance “ba na duniya ba”?
15 Ko da muna wa maƙwabtanmu wa’azin bishara, da yake mu mabiyan Yesu ne mu “ba na duniya ba ne.” (Yohanna 15:19) Kalmar “duniya” a nan na nuni ga ’yan adam da suke bare daga Allah. (Afisawa 4:17-19; 1 Yohanna 5:19) Mu ba na duniya ba ne idan muka ƙi halayensu da furcinsu da ke ɓata wa Jehobah rai. (1 Yohanna 2:15-17) Bugu da ƙari, daidai da ƙa’idar cewa “zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki,” za mu guje wa abokantaka da waɗanda ba sa rayuwa bisa sharuɗa na Kirista. (1 Korinthiyawa 15:33) Don mu zama ba na duniya ba za mu kasance “marar-aibi daga duniya.” (Yaƙub 1:27) Saboda haka, kasancewa ba na duniya ba, ba ya nufin mu daina kowane sha’ani da mutane.—Yohanna 17:15, 16; 1 Korinthiyawa 5:9, 10.
16, 17. Yaya ya kamata Kiristoci su bi da waɗanda ba su san gaskiyar Littafi Mai Tsarki ba?
16 To, yaya za mu bi da waɗanda ba su san gaskiyar Littafi Mai Tsarki ba? Bulus ya rubuta wa ikilisiya da ke Kolossi: “Ku yi tafiya cikin hikima wajen waɗanda ke waje, kuna rifta zarafi. Bari zancenku kullum ya kasance tare da alheri, gyartace da gishiri, domin ku sani yadda za ku amsa tambayar kowa.” (Kolossiyawa 4:5, 6) Manzo Bitrus ya rubuta: “Amma cikin zukatanku ku tsarkake Kristi kamar Ubangiji: kullum a shirye ku ke ku amsa ma kowane mai-tambayanku dalilin begen da ke cikinku, amma dai da ladabi da tsoro.” (1 Bitrus 3:15) Bulus ya gargaɗi Kiristoci “kada su ambaci kowa da mugunta, su kasance marasa-faɗa, masu-laushin hali, suna nuna iyakacin tawali’u ga dukan mutane.”—Titus 3:2.
17 Da yake mu Shaidun Jehobah ne, mu guje wa zafin hali ko kuma yi wa mutane taurin kai. Ba za mu yi amfani da furcin zargi ba don mu kwatanta mutane na wasu addinai. Maimakon haka, mu kasance da basira, ko idan ma maigida, maƙwabci, ko abokin aiki ba shi da halin kirki ko kuma mai baƙar magana ne.—Kolossiyawa 4:6; 2 Timothawus 2:24.
“Ka Kiyaye Kwatancin Sahihiyan Kalmomi”
18. Wane mummunar yanayi na ruhaniya waɗanda suka koma bautar ƙarya suke ciki?
18 Bayan mutum ya koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki, zai zama abin baƙin ciki ya koma ga bautar ƙarya. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta mummunar sakamakon yin haka sa’ad da ya ce: “Idan, bayanda suka tsira ma ƙazamtar duniya ta wurin sanin Ubangiji da Mai-ceto Yesu Kristi, sun sāke nannaɗewa a ciki kuma har an ci su, ya zama masu muhalin ƙarshe ya fi na farko muni. . . . Ya zama garesu bisa ga karin maganar nan mai-gaskiya, Kāre yana komawa zuwa wajen haraswatasa, gursuna wadda ta yi wanka kuma ga birkiɗa cikin lāka.”—2 Bitrus 2:20-22.
19. Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance a faɗake ga kome da zai iya yi wa ruhaniyarmu lahani?
19 Dole mu kasance a faɗake ga duk wani abin da zai yi wa ruhaniyarmu lahani. Kuma suna nan da yawa! Manzo Bulus ya yi gargaɗi: “Ruhu yana faɗi a sarari, cikin kwanaki na ƙarshe waɗansu za su ridda daga imani, suna maida hankali.” (1 Timothawus 4:1) Muna zama “cikin kwanaki na ƙarshe.” Waɗanda ba su guje wa bautar ƙarya ba za su zama “waɗanda ana wofadda su suna shillo ga kowace iskan sanarwa, ta wurin wawa-idon mutane masu-gwaninta.”—Afisawa 4:13, 14.
20. Ta yaya za mu kāre kanmu daga tasiri mai lahani na bautar ƙarya?
20 Ta yaya za mu kāre kanmu daga tasiri mai lahani na addinin ƙarya? Ka yi la’akari da dukan abubuwa da Jehobah ya yi tanadinsu. Muna da Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki. (2 Timothawus 3:16, 17) Jehobah ya kuma yi tanadin abinci na ruhaniya a yawalce ta “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Matta 24:45) Yayin da muke ci gaba cikin gaskiya, ya kamata mu gina marmarin “abinci mai-ƙarfi domin isassun mutane” da kuma son zuwan taron Kirista inda muke koyan gaskiya ta ruhaniya. (Ibraniyawa 5:13, 14; Zabura 26:8) Bari mu ƙuduri aniyar amfani da tanadin Jehobah don mu “kiyaye kwatancin sahihiyan kalmomi” da muka ji. (2 Timothawus 1:13) Ta haka za mu guje wa bautar ƙarya.
Me Ka Koya?
• Mecece “Babila Babba”?
• Menene dole ne mu yi don mu guje wa bautar ƙarya?
• Waɗanne haɗarurruka ne ya kamata mu guje wa domin ruhaniyarmu?
[Hoto a shafi na 18]
Ka san abin da ya sa aka kwatanta “Babila Babba” da malalaciya?
[Hoto a shafi na 19]
“Babila Babba” za ta halaka nan ba da daɗewa ba
[Hoto a shafi na 21]
Muna nuna “ladabi da tsoro” ga waɗanda ba masu bi ba ne