Sashe 8
Mutanen Isra’ila Sun Shiga Ka’anan
Joshua ya ja-goranci Isra’ila wajen kame ƙasar Ka’anan. Jehobah ya ba alƙalai ƙarfi don su ceci mutanensa daga zalunci
ƘARNUKA kafin Isra’ila ta shiga ƙasar Ka’anan, Jehobah ya yi alkawarin ba da wannan ƙasar ga zuriyoyin Ibrahim. Yanzu, a ƙarƙashin shugabancin Joshua, Isra’ilawa suna gab da kame Ƙasar Alkawari.
Allah ya yanke hukunci cewa Ka’aniyawa sun cancanci halaka. Sun mamaye ƙasar da mugun lalata, da zubar da jini. Saboda haka, za a halaka biranen Ka’aniyawa da Isra’ilawa suka kame gabaki ɗaya.
Amma, kafin su shiga ƙasar, Joshua ya aika ’yan leƙen asiri guda biyu, waɗanda suka kwana a birnin Jericho a gidan wata mata mai suna Rahab. Ta karɓi ’yan leƙen asirin da hannu biyu kuma ta kāre su, duk da cewa ta san su Isra’ilawa ne. Rahab ta ba da gaskiya ga Allahn Isra’ilawa, domin ta ji abubuwan da Jehobah ya yi don ya ceci mutanensa. Ta sa ’yan leƙen asirin sun rantse cewa ba za a kashe ta da iyalinta ba.
Daga baya, sa’ad da Isra’ilawa suka shiga ƙasar Ka’anan kuma suka kai wa Jericho hari, ta hanyar mu’ujiza, Jehobah ya sa bangwayen Jericho su rugurguje. Sojojin Joshua suka shiga ciki kuma suka halaka birnin, amma ba su kashe Rahab da iyalinta ba. A cikin shekaru shida tare da sojojinsa, Joshua ya kame manyan wurare a Ƙasar Alkawari. Bayan haka, an raba ƙasar ga ƙabilun Isra’ila.
A kusan ƙarshen hidimarsa ga Allah, Joshua ya tara mutanen. Ya gaya musu yadda Jehobah ya bi da kakanninsu kuma ya ƙarfafa su su bauta wa Jehobah. Bayan da Joshua da dattawan da ke hidima tare da shi sun mutu, sai Isra’ilawa suka ƙyale Jehobah kuma suka soma bauta wa allolin ƙarya. Har wajen shekaru 300, al’ummar ta ƙi yin biyayya ga dokokin Jehobah kai tsaye. A wannan lokacin, Jehobah ya ƙyale maƙiyan Isra’ila, kamar Filistiyawa, su zalunce su. Amma sa’ad da Isra’ilawa suka roƙi Jehobah don ya taimake su, ya naɗa alƙalai guda 12, don ya cece su.
Zamanin Alƙalai da aka rubuta a cikin littafin Alƙalawa ya soma ne da Othniel kuma ya kammala da Samson, wanda shi ne mutumi mafi ƙarfi a zahiri da ya taɓa rayuwa a duniya. Gaskiyar da ta bayyana a kai a kai a cikin labari mai ban al’ajabi da aka rubuta a cikin Littafi Mai Tsarki a littafin Alƙalawa ita ce: Yin biyayya ga Jehobah yana kawo albarka, rashin biyayya yana jawo bala’i.
—An ɗauko daga littafin Joshua; Alƙalawa; Levitikus 18:24, 25.
◼ Me ya sa Jehobah ya ceci Rahab da iyalinta?
◼ Menene Isra’ilawa suka yi bayan mutuwar Joshua?
◼ Wace gaskiya ce aka bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki a littafin Alƙalawa?
[’Yan rubutu na ba da bayani a shafi na 11]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua ●
Alƙalawa ●
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
[Taswira a shafi na 11]
(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)
← Shiga Ka’anan
− − Iyakokin wuraren da Isra’ilawa suka kame
FINIKIYA
FILISTIYA
KA’ANAN
Jericho
Urushalima