Maganar Jehovah Rayayyiya Ce
Darussa Daga Littafin Joshuwa
ISRA’ILAWA sun yi farin cikin jin waɗannan kalamai sa’ad da suka yi zango a Filayen Mowab a shekara ta 1473 K.Z.: “Ku shirya wa kanku guzuri, gama nan gaba da kwana uku za ku haye Kogin Urdun don ku mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku ke ba ku.” (Joshuwa 1:11) Tafiyarsu ta shekara 40 ta kusa ƙarewa.
Bayan shekaru ashirin, shugabansu Joshuwa ya tsaya a tsakiyar ƙasar Ka’anan kuma ya ce wa dattawan Isra’ila: “Ga shi kuma, na rarraba wa kabilanku ƙasashen al’umman da suka ragu, da na waɗanda na shafe su tsakanin Urdun da Bahar Rum wajen yamma. Ubangiji Allahnku ne zai sa su gudu a gabanku, ya kore su daga ƙasar. Za ku mallaki ƙasarsu kamar yadda Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku.”—Joshuwa 23:4, 5.
Littafin Joshuwa tarihi ne mai kayatarwa na abin da ya faru a cikin waɗannan shekaru 22, wanda Joshuwa ne ya rubuta a shekara ta 1450 K.Z. Yayin da muke tsaye a bakin ƙofar sabuwar duniya da aka yi mana alkawari, yanayinmu kamar na ’ya’yan Isra’ila ne da suke shirin mallakar Ƙasar Alkawari. Da marmari na ƙwarai, bari mu mai da hankali ga littafin Joshuwa.—Ibraniyawa 4:12.
A “FILAYEN YARIKO”
(Joshuwa 1:1–5:15)
Joshuwa ya sami aiki mai muhimmanci sa’ad da Jehovah ya gaya masa: “Bawana Musa ya rasu, sai ka tashi ka haye Kogin Urdun, kai da dukan jama’an nan, zuwa cikin ƙasar da nake ba Isra’ilawa”! (Joshuwa 1:2) Joshuwa ne ke da hakkin ya yi wa miliyoyin mutane ja-gora zuwa Ƙasar Alkawari. Domin su soma shiri, ya aiki ’yan leƙen asiri biyu zuwa Yariko—birnin da za su fara ci da yaƙi. A cikin wannan birnin akwai wata karuwa mai suna Rahab, wadda ta ji game da ayyuka masu ban al’ajabi da Jehovah ya yi wa mutanensa. Ta kāre ’yan leƙen asirin kuma ta taimaka musu, sakamakon haka, aka yi mata alkawarin kāriya.
Sa’ad da ’yan leƙen asirin suka dawo, Joshuwa da mutanen sun riga sun shirya domin su haye Urdun. Ko da yake Urdun ta cika maƙil, wannan bai zame musu tangarɗa ba, domin Jehovah ya sa ruwan da ke gangarowa daga sama ya tsaya cik kuma ruwan da ke gangarawa ya yanke zuwa Tekun Gishiri. Bayan sun gama haye Urdun, Isra’ilawa sun yi zango a Gilgal, kusa da Yariko. Bayan kwana huɗu, sun yi bikin Ketarewa a filayen Yariko, a ranar 14 ga watan Abib da yamma. (Joshuwa 5:10) Washegari, suka fara cin wasu daga cikin furen da ke ƙasar, kuma aka daina ba su manna. A wannan lokaci ne Joshuwa ya yi wa kowane ɗa na miji da aka haifa a cikin dajin kaciya.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
2:4, 5—Me ya sa Rahab ta ruɗi bayin sarki da suke neman ’yan leƙen asirin? Rahab ta yi kasadar kāre ’yan leƙen asirin don ta riga ta ba da gaskiya ga Jehovah. Saboda haka, ba dole ba ne ta gaya wa mutanen da suke so su cuci mutanen Allah inda ’yan leƙen asirin suke. (Matiyu 7:6; 21:23-27; Yahaya 7:3-10) Hakika, Rahab ta “sami kuɓuta saboda aikatawarta,” har da dabarar da ta yi na ɓatar da bayin sarki.—Yakubu 2:24-26.
5:14, 15—Wanene ɗan “sarkin yaƙin rundunar Ubangiji”? Ɗan sarkin da ya zo ya karfafa Joshuwa sa’ad da suka fara kame Ƙasar Alkawari ba wani ba ne “Kalma” ne, Yesu Kristi kafin ya zama mutum. (Yahaya 1:1; Daniyel 10:13) Abin ƙarfafa ne mu kasance da tabbacin cewa Yesu Kristi da aka ɗaukaka yana tare da mutanen Allah a yau sa’ad suke yaƙinsu na ruhaniya!
Darussa da Za Mu Koya:
1:7-9. Karatun Littafi Mai Tsarki kullum, yin bimbini a kan abin da ya ce a kowane lokaci, da kuma yin amfani da abin da muka koya za su taimaka mana a ƙoƙarinmu na ruhaniya.
1:11. Joshuwa ya umurci mutanen su shirya abinci da wasu abubuwan da suke bukata, kada su sa rai cewa Allah ne zai ba su dukan abin da suke bukata. Umurnin Yesu kada mu damu da abubuwa na rayuwa, tare da alkawarin da ya yi cewa “za a ƙara muku dukan waɗannan abubuwa” ba ya nufin cewa kada mu ƙoƙarta don mu taimaka wa kanmu.—Matiyu 6:25, 33.
2:4-13. Bayan ta ji labarin manyan ayyukan da Jehovah ya yi da kuma irin lokaci mai tsanani da take ciki, Rahab ta yanke shawarar ta taimaka wa masu bauta masa. Idan kana nazarin Littafi Mai Tsarki da daɗewa kuma ka fahimci cewa muna “zamanin ƙarshe,” bai kamata kai ma ka yanke shawarar bauta wa Allah ba?—2 Timoti 3:1.
3:15. Tun da yake rahoton da ’yan leƙen asirin suka kawo yana da kyau, Joshuwa ya aikata da wuri, bai jira har sai lokacin da ruwayen Urdun sun ragu ba. Idan ya kai ga ayyukan da suka shafi ibada ta gaskiya, dole ne mu aikata da gabagaɗi maimakon mu tsaya muna jinkiri har sai mun ga yanayi da ya dace.
4:4-8, 20-24. Duwatsu guda 12 da aka ɗauka a cikin Urdun za su zama abin tunawa ne ga Isra’ilawa. Yadda Jehovah yake kāre mutanensa na zamani daga hannun maƙiyansa ya zame musu abin tunawa cewa yana tare da su.
CI GABA DA YAƘI
(Joshuwa 6:1–12:24)
An rufe birnin Yariko “ba mai fita, ba mai shiga.” (Joshuwa 6:1) Ta yaya za a kama birnin? Jehovah ya gaya wa Joshuwa dabarar da zai yi. Ba da daɗewa ba garun garin ya faɗi kuma aka halaka birnin. Rahab da iyalin mahaifinta ne kaɗai suka sami tsira.
Garin da kuma za a kama ita ce alkaryar Ai. ’Yan leƙen asirin da aka aika sun kawo rahoton cewa mazauna birnin ba su da yawa, saboda haka ba a bukatan maza masu yawa don a halakar da ita. Amma, mutanen Ai sun kori sojoji kusan 3,000 da aka aika don su halaka birnin. Menene dalilin haka? Domin Jehovah ba ya tare da Isra’ilawa. Akan na ƙabilar Yahuza ya yi zunubi sa’ad da ake halaka Yariko. Bayan ya warware matsalar, Joshuwa ya sake kai wa Ai hari. Domin sun ci nasara a kan Isra’ilawa da farko, sarkin Ai na ɗokin sake tararsu da yaƙi. Amma Joshuwa ya yi amfani da dabara domin gabagaɗin da mutanen Ai suke da shi kuma ya ƙwace birnin.
Gibeyon ‘babban birni ce, har ma ta fi Ai girma, kuma duka mazajenta ƙarfafa ne.’ (Joshuwa 10:2) Sa’ad da suka ji game da nasarar da Isra’ilawa suka samu a kan Yariko da Ai, mutanen Gibeyon suka ruɗi Joshuwa har ya yi alkawarin salama da su. Al’ummai da suke kewaye da su suka ɗauki wannan a matsayin burga ce a garesu. Sai sarakunansu guda biyar suka haɗa hannu suka kai wa Gibeyon hari. Isra’ilawa suka ceci Gibeyonawa kuma suka sami nasara a kan maharan. Sauran nasarar da Isra’ila ta samu a ƙarƙashin shugabancin Joshuwa sun haɗa da biranen da suke kudu da yamma, da kuma nasarar da suka samu bisa rundunar haɗin gwiwa ta sarakuna da ke arewa. Duka sarakunan da aka ci da yaƙi a yammacin Urdun su 31 ne.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
10:13—Ta yaya wannan abin ban al’ajabi ya faru? “Akwai abin da zai fi ƙarfin Ubangiji,” mahaliccin sama da ƙasa ne? (Farawa 18:14) Idan Jehovah ya ga dama, yana iya tsayar da yadda duniya take juyawa domin rana da wata su zama kamar sun tsaya cik. Ko kuwa yana iya ƙyale duniya da wata su ci gaba da juyawa kuma ya sa hasken rana da wata su ci gaba da haskakawa. Ko yaya dai, “ba a taɓa yin yini kamar wannan ba” a tarihi.—Joshuwa 10:14.
10:13—Menene littafin Yashar? An sake ambata wannan a 2 Sama’ila 1:18 da ke nuni ga wata “Waƙa”—waƙar makoki bisa Saul Sarkin Isra’ila da kuma ɗansa Jonatan. Wataƙila wannan littafin yana cike ne da waƙoƙin tarihi waɗanda sanannu ne ga Yahudawa.
Darussa da Za Mu Koya:
6:26; 9:22, 23. La’anar da Joshuwa ya furta a lokacin da suke halaka Yariko ta cika bayan shekaru 500. (1 Sarakuna 16:34) La’anar da Nuhu ya yi wa jikansa Ka’anan ta cika sa’ad da Gibeyonawa suka zama bayi. (Farawa 9:25, 26) Maganar Jehovah kullum tana cika.
7:20-25. Wasu suna iya ɗaukan satar da Akan ya yi ɗan ƙaramin laifi, wataƙila su yi tunanin cewa ai ba ta jawo wa sauran illa ba. Suna iya ɗaukan ’yar ƙaramar satar ɗan ƙaramin laifi ga dokar Littafi Mai Tsarki. Amma mu kuwa, mu zama kamar Joshuwa a ƙudurinmu na yin tsayayya da matsi na ayyukan laifi ko lalata.
9:15, 26, 27. Kada mu ɗauki yarjejeniyar da muka yi da wasa kuma mu cika alkawarin da muka yi.
JOSHUWA YA SOMA AIKINSA MAI MUHIMMANCI NA ƘARSHE
(Joshuwa 13:1–24:33)
Da yake ya tsufa, yana da kusan shekara 90—sai Joshuwa ya fara raba ƙasar. Wannan babban aiki ne kuwa! Ƙabilun Gad da Ra’ubainu da rabin ƙabilar Manassa sun riga sun sami nasu gadōn a gabashin Urdun. Sauran ƙabilun da suka rage sun sami nasu gadōn a yammacin Urdun ta wajen jefa ƙuri’a.
An kafa mazauni a Shilo a yankin Ifraimu. Kalibu ya sami birnin Hebron, Joshuwa kuma ya sami Timnat-sera. Lawiyawa kuwa sun sami birane 48, har da biranen mafaka guda 6. A kan hanyarsu ta komawa wajen gadōnsu da ke gabashin Urdun, mayaƙan Ra’ubainawa, da Gadawa, da rabin ƙabilar Manassa suka “gina babban bagade.” (Joshuwa 22:10) Ƙabilun da suke yammacin Urdun suka ɗauki wannan a matsayin ridda, kuma hakan ya kusan jawo yaƙin ƙabilanci, amma ta tattaunawa aka kauce wa zubar da jini.
Bayan Joshuwa ya zauna na wani ɗan lokaci a Timnat-sera, sai ya kira dattawa, da shugabanni, da alƙalai, da jarumawan Isra’ila ya umurce su su kasance da gaba gaɗi su kuma riƙe aminci ga Jehovah. Daga bisani, Joshuwa ya tattara duka ƙabilun Isra’ila a Shekem. A nan ne ya tuna musu yadda Jehovah ya bi da su tun lokacin Ibrahim, kuma ya sake yi musu gargaɗi su “yi tsoron Ubangiji [su] kuma bauta masa da sahihanci da aminci.” Hakan ya motsa mutanen suka ce: “Za mu bauta wa Ubangiji Allahnmu, za mu kuma yi biyayya da muryarsa.” (Joshuwa 24:14, 15, 24) Bayan waɗannan al’amura, sai Joshuwa ya rasu yana ɗan shekara 110.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
13:1—Wannan bai saɓa wa abin da aka ambata a Joshuwa 11:23 ba? A’a, domin cin nasara bisa Ƙasar Alkawari ya kasu kashi biyu: Na farko ya ƙunshi yaƙin al’ummar da ta ci sarakunan Kan’anan 31, wanda ya karye ƙarfin Kan’aniyawa, na biyun kuma shi ne yaƙin da kowace ƙabila ta yi don ta mallaki ta ta gadōn ƙasar. (Joshuwa 17:14-18; 18:3) Ko da yake Isra’ilawa ba su kori Kan’aniyawa da ke tsakaninsu gaba ɗaya, waɗanda suka tsira ba su zame wa Isra’ila abin burga ba. (Joshuwa 16:10; 17:12) Joshuwa 21:44 ta ce: “Ubangiji kuma ya ba da hutawa ko’ina.”
24:2—Baban Ibrahim Tera, na bauta wa gumaka ne? Da ma can, Tera ba ya bauta wa Jehovah Allah. Wataƙila yana bauta wa wata, mai suna Sin—wanda sanannen allah ne a Ur. A tatsuniya na al’adar Yahudawa, an ce Tera na ƙera gumaka. Amma dai, sa’ad da Ibrahim ya bar Ur cikin umurnin Allah, Tera ya bi shi zuwa Haran.—Farawa 11:31.
Darussa da Za Mu Koya:
14:10-13. Ko da yake ya kai shekara 85, Kalibu ya tambaya a ba shi aiki mai wuya na korar mutanen da ke yankin Hebron. Wurin da Anakawa—ƙattai suke zaune. Da taimakon Jehovah, wannan mayaƙi mai basira ya sami nasara, kuma Hebron ta zama birnin mafaka. (Joshuwa 15:13-19; 21:11-13) Misalin Kalibu ya ƙarfafa mu kada mu guje wa aiki mai wuya na tsarin Allah.
22:9-12, 21-33. Dole ne mu mai da hankali mu kauce wa yin shakkar muradin wasu.
“Ba Ɗayan da Bai Tabbata Ba”
Sa’ad da ya tsufa, Joshuwa ya gaya wa mutanen Isra’ila cewa: “Dukan abubuwan alheri da Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku sun tabbata, ba ɗayan da bai tabbata ba.” (Joshuwa 23:14) Tarihin Joshuwa ya kwatanta wannan sarai!
Manzo Bulus ya rubuta: “Ai, duk abin da aka rubuta tun dā, an rubuta ne domin a koya mana, domin mu ɗore cikin sa zuciyan nan tamu ta haƙuri da ta’aziyyar da Littattafai ke yi mana.” (Romawa 15:4) Muna da tabbacin cewa begenmu a alkawuran Allah daidai ne. Babu alkawarin da ba zai tabbata ba; dukansu za su tabbata.
[Taswira a shafi na 5]
Ƙasashe da aka kame a ƙarƙashin shugabancin Joshuwa
BASHAN
GILEYAD
ARABA
NEGEB
Tekun Gishiri
Akshaf (Akko)
Geder
Horma
Hazor
Madon
Lasharon
Shimron
Yakneyam
Dor
Magiddo
Kedesh
Ta’anak
Hefer
Tirza
Afek
Taffuwa
Betel
Ai
Gilgal
Yariko
Gaza
Urushalima
Makkeda
Yarmut
Adullam
Libna
Lakish
Eglon
Hebron
Debir
Arad
[Hoto a shafi na 4]
Ka san dalilin da ya sa Rahab karuwa ta sami kuɓuta?
[Hoto a shafi na 5]
Joshuwa ya umurci Isra’ilawa su “yi tsoron Ubangiji, [su] bauta masa”
[Hoto a shafi na 7]
Satar da Akan ya yi ba ɗan ƙarami laifi ba ne, domin ta jawo babban ɓarna
[Hoto a shafi na 7]
“Ta bangaskiya garun Yariko ya rushe.”—Ibraniyawa 11:30