Ka Kusaci Allah
Yana Son Mu Yi Nasara
Joshua 1:6-9
IYAYE masu kula suna ƙosa su ga yaransu sun sami ci gaba, su kuma samu gaba mai amfani da rayuwa mai gamsarwa. Hakazalika, Jehobah, Ubanmu na sama yana son yaransa na duniya su yi nasara. Don nuna kulawarsa a gare mu, ya gaya mana yadda za mu yi nasara. Alal misali, ka yi la’akari da kalaman da Joshua ya yi, waɗanda ke rubuce a Joshua 1:6-9.
Ka yi tunani akan wannan batun. Bayan mutuwar Musa, Joshua ya zama sabon shugaban miliyoyi ’ya’yan Isra’ila. Isra’ilawa suna shirin shiga ƙasar da Allah ya yi wa kakanninsu alkawari. Allah yana da wasu shawarwari ga Joshua. Idan ya bi su, za su taimaka masa ya yi nasara. Amma waɗannan shawarwari ba don amfanin Joshua kaɗai ba ne. Idan mun yi amfani da su mu ma za mu yi nasara.—Romawa 15:4.
Jehobah ya gaya wa Joshua cewa ya yi gaba gaɗi da kuma ƙarfi, ba sau ɗaya ba, amma sau uku. (Ayoyi ta 6, 7, 9) Babu shakka, Joshua zai bukaci gaba gaɗi da iko don ya ja-goranci al’ummar zuwa Ƙasar Alkawari. Ta yaya zai nuna waɗannan halayen?
Joshua zai iya samun ƙarfafa da ƙarfi daga hurarrun kalamai. “Ka kiyaye ka aika bisa ga dukan shari’a, wadda Musa bawana ya umurce ka,” Jehobah ya ce. (Aya ta 7) A lokacin, wataƙila Joshua yana da littattafai kaɗan na Littafi Mai Tsarki a rubuce.a Amma dai, samun Kalmar Allah kawai ba zai tabbatar da ci gaba ba. Don ta amfane shi, Joshuwa yana bukatan ya yi abubuwa biyu.
Da farko, wajibi ne Joshua ya dinga cika zuciyarsa da kalmar Allah. Jehobah ya ce: “Za ka riƙa bincikensa dare da rana.” (Aya ta 8) Wani aikin bincike da ya yi magana game da asalin wannan kalmar ya ce: “Allah yana umurtar Joshua cewa ya tuna da Dokarsa ta ‘furta ta a hankali’ ‘ƙididdiga’ ta, ko kuma ‘bayyana wa kansa.’” Karanta da kuma yin bimbini akan Kalmar Allah kowace rana za ta taimaki Joshua ya cim ma ƙalubalen da ke gabansa.
Na biyu, Joshua yana bukatan ya yi amfani da abin da ya koya daga Kalmar Allah. Jehobah ya gaya masa: ‘Ka kiyaye ka aika bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki: gama da hakanan kuma za ka yi nasara.’ (Aya ta 8) An haɗa yin nasarar Joshua da yin nufin Allah. Yaya zai zama hakan? Nufin Allah yakan samu nasara.—Ishaya 55:10, 11.
Joshua ya yi biyayya da shawarar Jehobah. A sakamako, ya more cikakkiyar rayuwa mai gamsarwa a matsayin amintaccen mai bauta wa Jehobah.—Joshua 23:14; 24:15.
Kana son ka yi rayuwa mai cike da ma’ana, kamar Joshua? Jehobah yana son ka yi nasara. Amma samun Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, ba shi kenan ba. Wani Kirista wanda ya daɗe yana aminci ga Allah ya ba da shawara: “Ka karanta Littafi Mai Tsarki kuma ka yi amfani da shi.” Idan kana cika zuciyarka kullum da kalmar Allah kuma kana yin amfani da abin da ka koya, da hakan, kai ma kamar Joshua, “za ka yi nasara.”
[Hasiya]
a Wataƙila hurarrun kalamai da Joshua yake da su sun ƙunshi littattafan Musa guda biyar (Farawa, Fitowa, Levitikus, Littafin Lissafi, da Kubawar Shari’a), littafin Ayuba, da littafi ɗaya ko biyu na zabura.