Ka Kusaci Allah
Mai Cika Alkawura
JOSHUA 23:14
AMINCEWA da wasu yana yi maka wuya kuwa? Abin baƙin ciki, muna zaune ne a duniyar da ba a yawan amincewa da mutum. Idan wani wanda ka amince da shi ya yi maka laifi, wataƙila saboda ƙarya ko kuma ya ƙi cika alkawari, babu shakka amincewa da ka yi da shi zai ragu. Amma dai, akwai wanda za ka amince da shi da bai zai taɓa ɓata maka rai ba. “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka,” in ji Misalai 3:5. Me ya sa Jehobah ya cancanci irin wannan dogara? Don ba da amsar, bari mu bincika kalaman Joshua, mutumin da ya amince da Jehobah da dukan zuciyarsa, wadda aka rubuta a Joshua 23:14.
Ka yi la’akari da yanayin. Joshua, wanda ya gāji shugabancin Isra’ila daga Musa, ya kusan kai shekara 110 da haihuwa. A cikin waɗannan shekarun, ya ga ayyuka masu girma da Jehobah ya yi wa Isra’ila, har da hanya ta mu’ujiza da ya yi amfani da ita ya cece su a Jar Teku shekaru sittin kafin lokacin. Yanzu, Joshua da yake tuna dukan waɗannan aukuwan ya kira ‘dattiɓai da manya, da alƙalawa, da magabatan’ Isra’ilawa wuri ɗaya. (Joshua 23:2) Kalmar da ya furta yanzu bai nuna hikimar da yake da ita saboda shekarunsa ba kawai amma saboda bimbinin da yake yi daga zuciyarsa da ke cike da imani.
“Yau ni zan bi hanya ta dukan duniya,” Joshua ya bayyana. Furcin nan “hanya ta dukan duniya” karin magana ce da ke nufin mutuwa. Wato, Joshua yana cewa, “ba ni da sauran lokaci da yawa da zan rayu.” Sanin cewa ya kusan mutuwa, babu shakka, Joshua ya yi sa’o’i da yawa yana bimbini a kan rayuwarsa. Waɗanne kalamai na ƙarshe ne zai gaya wa ’yan’uwansa masu bi?
Joshua ya ci gaba: “Babu wani abu ɗaya ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku: dukansu sun tabbata a gareku, babu wani abu ɗaya ya sare daga ciki.” Waɗannan kalamai ne na mutumin da ya dogara ga Allah sosai. Menene dalili? Yin tunani a kan dukan abin da ya gani, Joshua ya fahimci cewa Jehobah yana cika alkawuransa, a ko yaushe.a Sanin dalilin faɗin hakan yana da sauƙi: Joshua yana son ’yan’uwansa Isra’ilawa su kasance da cikakkiyar imani cewa dukan alkawuran Jehobah game da rayuwarsu ta gaba za su cika da gaske.
Wani aikin bincike ya ce game da Joshua 23:14: “Ka fito da dukan alkawuran da ke cikin Littafi Mai Tsarki; sai ka bincika rubutaccen tarihin da ke duniya, kuma ka tambayi dukan halittan da ke cikinta, don ka ga ko akwai lokaci ko da sau ɗaya ne da Allah ya ƙi cika ko kuma ya manta alkawarin da ya yi.” Da zai yiwu a yi irin wannan binciken, za mu faɗi ainihin abin da Joshua ya ce, wato, babu alkawuran Jehobah da ba sa cika.—1 Sarakuna 8:56; Ishaya 55:10, 11.
Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da alkawuran Allah da suka cika, har da wasu da suke cika a gabanmu. Yana kuma ɗauke da alkawuran Jehobah masu ban al’ajabi game da rayuwarmu ta nan gaba.b Me zai hana ka bincika wannan labarin da kanka? Yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai iya sa ka gaskata cewa Mai Cika alkawura ya cancanci mu amince da shi.
[Hasiya]
a Ga wasu daga cikin alkawura, ko tabbaci, da Joshua ya ga cikawarsu. Jehobah zai ba Isra’ila ƙasa ta su. (Gwada Farawa 12:7 da Joshua 11:23.) Jehobah zai ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar. (Gwada Fitowa 3:8 da Fitowa 12:29-32.) Jehobah zai kiyaye mutanensa.—Gwada Fitowa 16:4, 13-15 da Kubawar Shari’a 8:3, 4.
b Don ƙarin bayani game da alkawuran Allah ga rayuwarmu ta nan gaba, ka duba babi na 3, 7, da 8 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwar? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.