Maganar Jehobah Tana Cika A Kullayaumi
“Babu wani abu ɗaya [da] ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku: dukansu sun tabbata a gareku.”—JOSHUA 23:14.
1. Wanene Joshua, kuma menene ya yi a ƙarshen rayuwarsa?
SHI mutumi ne mai ƙarfi kuma shugaban sojoji wanda ba ya tsoro, mutum mai bangaskiya da kuma aminci. Ya yi aiki tare da Musa kuma Jehobah ya zaɓe shi ya shugabanci al’ummar Isra’ila daga cikin jeji mai ban tsoro zuwa ƙasar da ke cike da madara da zuma. A kusan ƙarshen rayuwarsa, wannan mutumin da ake girmamawa sosai, wato, Joshua, ya yi wa dattawan Isra’ila jawabin ban kwana mai motsa zuciya. Babu shakka, wannan jawabin ya ƙarfafa bangaskiyar waɗanda suka saurare shi. Kuma zai iya ƙarfafa ka a yau.
2, 3. Wane yanayi ne Isra’ila take ciki sa’ad da Joshua ya yi wa dattawan Isra’ila jawabi kuma menene Joshua ya ce?
2 Ka yi tunanin yanayin kamar yadda aka kwatanta a cikin Littafi Mai Tsarki: “Ananan kuwa bayan kwanaki masu-yawa, sa’anda Ubangiji ya bada hutu ga Isra’ila daga dukan magabtansu na kewaye da su, Joshua kuma ya tsufa, shekarunsa sun yawaita: sai Joshua ya kira dukan Isra’ila da datiɓansu da manyansu, da alƙalawansu, da magabatansu, ya ce masu, Ni na tsufa, shekaruna sun yawaita.”—Joshua 23:1, 2.
3 Joshua yana neman shekaru 110, kuma ya yi rayuwa ne a wani lokaci mai ban al’ajabi a tarihin mutanen Allah. Ya ga ayyuka masu girma na Allah, kuma ya ga cikawar alkawuran Jehobah masu yawa. Domin abubuwan da ya gani da idanunsa, da gaba gaɗi ya ce: “Kun sani cikin zukatanku duka da cikin rayukanku duka, babu wani abu ɗaya [da] ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku: dukansu sun tabbata a gareku, babu wani abu ɗaya [da] ya sare daga ciki.”—Joshua 23:14.
4. Waɗanne alkawura ne Jehobah ya yi wa Isra’ilawa?
4 Waɗanne kalmomin Jehobah ne suka cika a zamanin Joshua? Za mu tattauna alkawura guda uku da Jehobah ya yi wa Isra’ilawa. Na farko, Allah zai cece su daga bauta. Na biyu, zai kāre su. Na uku, zai kula da su. Jehobah ya yi wa mutanensa a zamanin nan irin waɗannan alkawuran, kuma muna ganin su suna cika a yau. Kafin mu tattauna abin da Jehobah ya yi a zamanin nan, bari mu tattauna abin da ya yi a zamanin Joshua.
Jehobah ya Ceci Mutanensa
5, 6. Ta yaya ne Jehobah ya ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar, kuma menene hakan ya nuna?
5 Sa’ad da Isra’ilawa suka yi wa Allah kuka saboda bautar da suke yi a ƙasar Masar, Jehobah ya lura da hakan. (Fitowa 2:23-25) A wajen wani ɗan kurmi da ke cin wuta, Jehobah ya ce wa Musa: “Na kuwa sabko domin in cece [mutanena] daga hannun Masarawa, in fishe su daga wacan ƙasa, in kai su cikin ƙasa mai-kyau mai-faɗi, ƙasa mai-zubasda madara da zuma.” (Fitowa 3:8) Abin farin ciki ne a gan yadda Jehobah yake cika alkawuransa! Sa’ad da Fir’auna ya ƙi ya ƙyale Isra’ilawa su fita daga Masar, Musa ya gaya masa cewa Allah zai juya ruwan da ke kogin Nile zuwa jini. Kalmar Jehobah ta cika. Ruwan da ke Kogin Nile ya zama jini. Kifayen da ke ciki suka mutu, kuma aka kasa shan ruwan kogin. (Fitowa 7:14-21) Fir’auna ya ci gaba da yin taurin kai, hakan ya sa Jehobah ya kawo ƙarin annoba tara, kuma ya bayyana kowannensu kafin su faru. (Fitowa, sura 8-12) Bayan da annoba ta goma ta kashe ’ya’yan fari na Masarawa, Fir’auna ya ƙyale Isra’ilawa su tafi.—Fitowa 12:29-32.
6 Wannan ceton ya sa Jehobah ya ɗauki Isra’ila a matsayin al’ummar da ya zaɓa. Hakan ya ɗaukaka Jehobah a matsayin Mai Cika alkawarinsa, wanda kalmarsa tana cika a kullayaumi. Hakan ya nuna cewa Jehobah ya fi dukan allolin al’ummai iko. Idan muka karanta labarin wannan ceton, hakan zai ƙarfafa bangaskiyarmu. Ka yi tunani yadda zai kasance a ce ka ga abin da ya faru da idanunka! Joshua ya fahimci cewa Jehobah shi ne “Maɗaukaki bisa dukan duniya.”—Zabura 83:18.
Jehobah Ya Kāre Mutanensa
7. Ta yaya ne Jehobah ya kāre Isra’ilawa daga sojojin Fir’auna?
7 Alkawari na biyu kuma fa, wato, kāriyar da Jehobah zai yi wa mutanensa? An ga cikar wannan alkawarin sa’ad da Jehobah ya yi alkawari zai ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar zuwa Ƙasar Alkawari. Ka tuna cewa cikin haushi Fir’auna da sojojinsa masu ƙarfi, tare da ɗarurruwan karusa cike da kayan yaƙi sun bi Isra’ilawa. Wannan mutumi mai girman kai yana da gabagaɗi musamman sa’ad da Isra’ilawa suka rasa inda za su bi a tsakanin dutse da teku. Allah ya taimaki mutanensa sa’ad da ya sa gajimare ya raba Isra’ilawa da Masarawa. A ɓangaren Masarawa duhu ne, amma a wurin Isra’ilawa kuwa haske ne. Sa’ad da gajimaren ya hana Masarawa su ci gaba da tafiya, Musa ya ɗaga sandarsa sai ruwan Jar Tekun ya rabu biyu, hakan ya sa Isra’ilawa suka tsira kuma ya zama tarko ga Masarawa. Jehobah ya halaka sojojin Fir’auna masu ƙarfi gabaki ɗaya kuma ya kāre mutanensa daga halaka.—Fitowa 14:19-28.
8. Wane kāriya ne Isra’ilawa suka fuskanta (a) a jeji da kuma (b) sa’ad da suka shiga Ƙasar Alkawari?
8 Bayan da suka ketare Jar Tekun, Isra’ilawa sun yi tafiya a cikin ƙasar da aka kwatantata da “babban jeji, mai-ban tsoron nan, wurinda macizai masu-wuta su ke, da kunamai, da ƙasa mai-ƙishi inda babu ruwa.” (Kubawar Shari’a 8:15) A nan ma Jehobah ya kāre mutanensa. Sa’ad da za su shiga cikin Ƙasar Alkawari kuma fa? Sojojin Ka’anan masu ƙarfi sun yi musu hamayya. Duk da haka, Jehobah ya ce wa Joshua: “Ka tashi, ka ƙetare wannan Urdun, da kai, da dukan wannan al’umma, zuwa cikin ƙasa wadda ni ke ba su, su ’ya’yan Isra’ila. Babu mutum da za ya iya tsaya gabanka dukan kwanakin ranka: kamar yadda ina tare da Musa, hakanan zan yi tare da kai; ba ni tauye maka, ba ni kuwa yashe ka ba.” (Joshua 1:2, 5) Waɗannan kalaman na Jehobah sun cika. Cikin shekaru shida, Joshua ya kame sarakuna 31 kuma ya shugabanci babban sashe na Ƙasar Alkawari. (Joshua 12:7-24) Jehobah ne ya sa Joshua ya yi nasara.
Jehobah ya Kula da Mutanensa
9, 10. Ta yaya ne Jehobah ya kula da mutanensa a jeji?
9 Ka yi la’akari da alkawari na uku, wato, Jehobah zai kula da mutanensa. Bayan da ya cece su daga ƙasar Masar, Allah ya yi wa Isra’ilawa alkawari cewa: “Zan zubo maku da abinci daga sama: mutanen kuwa za su fita, kowace rana su tattara bukatar yini.” Hakika, Allah ya yi tanadin “abinci daga sama.” “Sa’anda ’ya’yan Isra’ila suka gan shi, suka ce ma junansu, Minene wannan?” Manna ce, abincin da Jehobah ya yi musu alkawari.—Fitowa 16:4, 13-15.
10 Jehobah ya kula da Isra’ilawa har tsawon shekaru 40 a cikin jeji, kuma ya yi musu tanadin abinci da ruwan sha. Ya kuma sa tufafinsu ba su tsufa ba kuma ƙafafuwansu ba su kumbura ba. (Kubawar Shari’a 8:3, 4) Joshua ya ga dukan abin da ya faru. Jehobah ya ceci mutanensa, ya kāre su kuma ya kula da su, kamar yadda ya yi musu alkawari.
Ceto a Zamaninmu
11. Menene ya faru a Brooklyn da ke New York a shekara ta 1914, kuma wane lokaci ne ya kai?
11 A zamaninmu kuma fa? A ranar Jumma’a da safe, ta 2 ga Oktoba, a shekara ta 1914, Charles Taze Russell, wanda yake shugabancin daliɓan Littafi Mai Tsarki ya shigo cikin dakin cin abinci na Brooklyn Bethel da ke New York. Ya ce: “Barkanku da safiya.” Kafin ya zauna, ya yi sanarwa da farin ciki cewa: “Lokacin Al’ummai ya ƙare; kuma zamanin sarakuna ya wuce.” Yanzu lokaci ya yi da Jehobah Mamallakin sararin samaniya zai ceci mutanensa!
12. Su wanene aka cece su a shekara ta 1919, kuma da wane sakamako?
12 Bayan shekaru biyar, Jehobah ya ceci mutanensa daga “Babila Babba,” wato, babbar daular duniya ta addinin ƙarya. (Ru’ya ta Yohanna 18:2) Mutane kaɗan ne kawai a cikinmu da suke raye yanzu suka ga wannan ceto mai ban al’ajabi. Duk da haka, mun ga sakamakon. Jehobah ya sake kafa bauta ta gaskiya kuma ya tattara waɗanda suke so su bauta masa. Annabi Ishaya ya annabta cewa hakan zai faru: “Za ya zama a cikin kwanaki na ƙarshe, dutse na gidan Ubangiji za ya kafu a ƙwanƙolin duwatsu, ya ɗaukaka bisa kan tuddai; al’ummai duka kuma za su zubo wurinsa.”—Ishaya 2:2.
13. Wace ƙaruwa ce a tsakanin mutanen Jehobah ka gani?
13 Kalaman Ishaya sun cika. A shekara ta 1919 shafaffun da suka rage sun soma bishara a dukan duniya wadda ta sa bautar Allah na gaskiya ta ci gaba. A tsakanin shekara ta 1930 zuwa 1939, an fahimci cewa an tattara “waɗansu tumaki” su shiga cikin bauta ta gaskiya. (Yohanna 10:16) A dā su dubbai ne, a yanzu kuwa mutanen da suke goyon bayan bauta ta gaskiya sun kai miliyoyi! A cikin wahayi da aka ba manzo Yohanna, an kira su “taro mai-girma, wanda ba mai-ƙirgawa, daga cikin kowane iri, da dukan kabilai da al’ummai da harsuna.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9) Menene ka gani a zamaninka? Shaidun Jehobah guda nawa ne a lokacin da ka sami gaskiya? A yau, waɗanda suke bauta wa Jehobah sun fi 6,700,000. Domin ya ceci mutanensa daga Babila Babba, Jehobah ya buɗe hanyar ƙaruwa a dukan duniya da muke gani yanzu.
14. Wane ceto ne yake tafe?
14 Wani ceto yana zuwa, wanda zai shafi dukan mutane a duniya. Jehobah zai nuna ƙarfinsa ta wajen halaka dukan waɗanda suke hamayya da shi, kuma zai ceci mutanensa zuwa cikin sabuwar duniya inda adalci zai kasance. Abin farin ciki ne a ga ƙarshen mugunta da kuma farkon zamani mai ɗaukaka a dukan tarihin ’yan adam!—Ru’ya ta Yohanna 21:1-4.
Yadda Jehobah Yake Kāre Mu a Yau
15. Me ya sa ake bukatar kāriyar Jehobah a zamanin nan?
15 Kamar yadda muka fahimta, Isra’ilawa na zamanin Joshua suna bukatar kāriya ta Jehobah. Mutanen Jehobah a yau suna bukatar kāriya kuwa? Hakika! Yesu ya gargaɗi mabiyansa: “[Mutane] za su miƙa ku ga ƙunci, za su kashe ku kuma: za ku zama abin ƙi ga dukan al’ummai sabili da sunana.” (Matta 24:9) Tun shekaru da yawa, Shaidun Jehobah sun jimre wa mugun hamayya da kuma tsanantawa mai tsanani. Duk da haka, Jehobah yana kula da mutanensa. (Romawa 8:31) Kalmarsa ta ba mu tabbaci cewa “babu alatun da aka halitta domin ciwutan” mu da zai hana mu shelar bisharar Mulki da kuma koyarwa.—Ishaya 54:17.
16. Menene ka gani da ya tabbatar maka cewa Jehobah yana kāre mutanensa?
16 Duk da muguntar duniya, mutanen Jehobah suna samun cin gaba. Shaidun Jehobah suna samun ƙaruwa a ƙasashe 236, hakan ya ba da tabbaci cewa Jehobah yana tare da mu kuma yana kāre mu daga waɗanda suke so su halaka mu. Za ka iya tuna shugabannin gwamnati da addinai da suka tsananta wa mutanen Allah a zamaninka? Menene ya faru da su? Ina suke yanzu? An halaka yawancinsu kamar Fir’auna na zamanin Musa da Joshua. Bayin Allah da suka mutu cikin aminci kuma fa? Jehobah zai tuna da su. Hakan ne kawai zai sa su tsira. Hakika, game da batun kāriya, kalaman Jehobah sun cika.
Jehobah Yana Kula da Mutanensa a Yau
17. Wane tabbaci ne Jehobah ya ba da game da abinci na ruhaniya?
17 Jehobah ya kula da mutanensa a cikin jeji, kuma yana kula da su a yau. Muna samun isashen abinci na ruhaniya daga wurin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.” (Matta 24:45) Muna samun ilimin gaskiya na ruhaniya waɗanda a dā suke ɓoye. Wani mala’ika ya gaya wa Daniel: “Ka kuble zantattukan, ka rufe litafin da hatimi, har kwanakin ƙarshe; mutane dayawa za su kai da kawo a guje, ilimi kuma za ya ƙaru.”—Daniel 12:4.
18. Me ya sa za a iya cewa ilimin gaskiya yana ƙaruwa?
18 Yanzu muna zaune a kwanaki na ƙarshe, kuma ilimin gaskiya ya ƙaru sosai. A dukan duniya, ruhu mai tsarki yana kai masu son gaskiya ga cikakken sanin gaskiyar Allah da kuma nufinsa. Littafi Mai Tsarki yana da yawa a duniya yau, haka kuma littatafai da suke taimaka wa mutane su fahimci gaskiyar da Littafi Mai Tsarki yake ɗauke da shi. Alal misali, ka yi la’akari da sashe na abin da ke cikin littafin nan na nazari mai suna Menene Ainihin Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?a Waɗansu babi a wannan littafin sune: “Mecece Koyarwa ta Gaskiya Game da Allah,?” “Ina Matattu Suke,?” “Menene Mulkin Allah,?” da kuma “Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Wahala?” Mutane sun yi tunani sosai game da waɗannan tambayoyin shekaru dubbai da suka wuce. Yanzu an samu amsoshin waɗannan tambayoyin. Bayan shekaru masu yawa na jahilci da kuma koyarwar ƙarya ta Kiristendom, Kalmar Allah ta yi nasara, kuma tana kiyaye dukan waɗanda suke son su bauta wa Jehobah.
19. Waɗanne alkawura ne ka gani sun cika, kuma menene ka kammala?
19 Babu shakka, daga abin da muka gani da idanunmu, za mu iya cewa: “Babu wani abu ɗaya [da] ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku: dukansu sun tabbata a gareku, babu wani abu ɗaya [da] ya sare daga ciki.” (Joshua 23:14) Jehobah ya ceci, ya kāre, kuma yana kula da bayinsa. Za ka iya nuna wani alkawarinsa da bai cika ba a daidai lokacin da ya kafa? Ba za ka iya ba. Mun tabbata da gaskiyar Kalmar Allah.
20. Me ya sa ya kamata mu duba gaba da tabbaci?
20 Me zai faru a nan gaba? Jehobah ya gaya mana cewa yawancinmu za su iya yin begen zama a duniya da aka mai da zuwa aljanna mai kyau. Mutane kaɗan ne daga cikin mu suke da begen yin sarauta da Kristi a sama. Ko menene begenmu, muna da dalilin kasancewa da aminci kamar Joshua. Lokaci na nan zuwa da begenmu zai cika. Sa’an nan za mu duba dukan alkawuran da Jehobah ya yi, kuma mu ce: “Sun tabbata.”
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Wane alkawarin Jehobah ne Joshua ya ga cikawarsa?
• Waɗanne alkawuran Allah ne ka ga cikawarsa?
• Wane tabbaci ne ya kamata mu kasance da shi game da kalmar Allah?
[Hoto a shafi na 19]
Jehobah ya ɗauki mataki don ya ceci mutanensa
[Hoto a shafi na 19]
Ta yaya ne Jehobah ya kāre mutanensa a Jar Teku?
[Hoto a shafi na 20]
Ta yaya ne Jehobah ya kula da mutanensa a jeji?
[Hotuna a shafi na 21]
Jehobah yana kula da mutanensa a yau