Sashe 19
Yesu Ya Yi Annabci Mai Girma
Yesu ya bayyana abubuwan da za su nuna cewa ya soma sarauta da kuma ƙarshen wannan zamanin
AKAN Dutsen Zaitun, suna kallon Urushalima da kuma haikalinta, manzannin Yesu su huɗu sun tambaye shi a keɓe game da wasu abubuwan da ya faɗa a dā. Yesu bai daɗe da faɗin cewa za a halaka haikalin Urushalima ba. A dā, ya gaya musu game da “matuƙar zamani.” (Matta 13:40, 49) A yanzu manzannin sun tambaye shi: “Yaushe waɗannan abubuwa za su zama? me ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?”—Matta 24:3.
A cikin amsar da ya bayar, Yesu ya gaya musu abin da zai faru kafin a halaka Urushalima. Amma kalaman da ya faɗa suna da ma’ana mai girma sosai. Annabcinsa zai sami cikawa a dukan duniya a gaba. Yesu ya annabta game da aukuwa da yanayin duniya da za su haɗu su zama alamu. Wannan alamar za ta nuna wa waɗanda suke duniya cewa Yesu ya soma sarauta a matsayin Sarki a sama. Wato, alamar za ta nuna cewa Jehobah Allah ya naɗa Yesu a matsayin Sarkin Mulkin Almasihu da aka yi alkawarinsa tun da daɗewa. Alamar tana nufin cewa Mulkin tana gab da cire mugunta kuma ta kawo salama ta gaske ga ’yan adam. Abubuwan da Yesu ya annabta za su zama alamun ranakun ƙarshe na wannan zamanin, wato, yanayin addini, siyasa, da na mutane da ke wanzuwa a yanzu, da kuma somawar sabon zamani.
Sa’ad da yake bayyana abin da zai faru a duniya a lokacin da ya zama Sarki a sama, Yesu ya faɗi cewa za a yi yaƙi a dukan duniya, ƙarancin abinci, manyan girgizar ƙasa, da kuma yaɗuwar cututtuka. Rashin bin doka zai ƙaru. Almajiran Yesu na gaskiya za su yi wa’azin bishara game da Mulkin Allah a dukan duniya. Dukan waɗannan abubuwan za su kai ƙarshensu a “ƙunci mai-girma” wanda ba a taɓa yin irin sa ba.—Matta 24:21.
Ta yaya ne mabiyan Yesu za su san cewa wannan ƙuncin ya kusa? Yesu ya ce: “Daga itacen ɓaure fa sai ku koyi misalinsa.” (Matta 24:32) Bayyanuwar ganyen da ke kan rassan ɓaure alamu ne cewa rani ya kusa. Hakazalika, ganin cewa abubuwan da Yesu ya annabta suna faruwa a cikin ƙayyadadden lokaci alamu ne cewa ƙarshe ya kusa. Babu wani sai Uba kaɗai ne ya san ainihin rana da lokacin da za a soma ƙunci mai girma. Saboda haka, Yesu ya umurci almajiransa: “Ku yi tsaro, . . . gama ba ku san lokacinda sa’a ta ke ba.”—Markus 13:33.
—An ɗauko daga Matta surori 24 da 25; Markus sura ta 13; Luka sura ta 21.
◼ A kan menene manzannin Yesu suka nemi ƙarin sani?
◼ Menene ma’anar alamar da Yesu ya ba da, kuma menene fasalolin wannan alamar?
◼ Wace shawara ce Yesu ya ba almajiransa?
[Akwati a shafi na 22]
ALAMAR BAYYANUWR KRISTI
Yesu ya annabta cewa akwai alamar da za ta nuna cewa lokaci ya kusa da Allah zai halaka wannan lalatacen zamani. Tun daga Yaƙin Duniya na Ɗaya, ’Yan Adam sun shaida abin da Yesu ya annabta. Canje-canjen da ake samu a addinai, siyasa, da zaman mutane a dukan duniya suna ja-gora ne da sauri zuwa ƙarshen wannan zamanin. Yesu ya koya wa mabiyansa cewa idan suna son su tsira, dole ne su “yi tsaro” kuma su ɗauki mataki nan da nan wajen kasancewa a gefen Allah a batun ikon mallaka.a—Luka 21:36; Matta 24:3-14.
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani game da annabcin Yesu, duba shafuffuka na 86-95 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
[Taswira a shafi na 22]
Farawa
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Makoki
Ezekiel
Daniyel
Hosiya
Joel
Amos
Obadiya
Yunana
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
Zakariya
Malakai
● Matta
● Markus
● Luka
Yohanna