Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 2/15 pp. 21-25
  • Mecece Bayyanuwar Kristi Take Nufi A Gare ka?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mecece Bayyanuwar Kristi Take Nufi A Gare ka?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Lokaci Mai Tsawo
  • Fahimtar Alamar
  • Tsarar da ta Fahimci Alamar
  • “Ku Yi Tsaro”
  • ‘Bari Mulkinka Ya Zo’
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Yaushe Mulkin Allah Zai Zo?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 2/15 pp. 21-25

Mecece Bayyanuwar Kristi Take Nufi A Gare ka?

“Mecece kuma alamar dawowarka, da ta ƙarewar zamani?”—MAT. 24:3.

1. Wace tambaya mai muhimmanci ce manzannin Yesu suka yi?

KUSAN shekaru dubu biyu da suka shige, manzannin Yesu su huɗu sun yi wata tambaya sa’ad da suke tattaunawa da Ubangijinsu a keɓe a kan Dutsen Zaitun. Sun tambaye shi cewa: “Yaushe za a yi waɗannan abubuwa? Mecece kuma alamar dawowarka, da ta ƙarewar zamani?” (Mat. 24:3, Littafi Mai Tsarki.) A wannan tambayar, manzannin sun yi amfani da furci biyu masu muhimmanci, “alamar dawowarka” da “ƙarewar zamani.” Menene waɗannan furcin suke nufi?

2. Mecece ma’anar kalmar nan “ƙarewa”?

2 Bari mu fara tattauna furci na biyu, yi la’akari da kalmar nan “ƙarewa,” kalmar Helenanci da aka fassara syn·teʹlei·a. Wannan kalmar syn·teʹlei·a tana nufin “ƙarewa,” ita kuwa kalmar Helenanci te’los, mai kama da wannan tana nufin “ƙarshe.” Za mu iya kwatanta bambancin da ke tsakanin waɗannan kalaman biyu da jawabin da aka yi a Majami’ar Mulki. Ƙarewar jawabin ita ce sashe na ƙarshe, inda mai jawabin zai ɗan ba da lokaci wajen tuna wa masu sauraro abubuwan da ya faɗa sa’an nan kuma ya nuna yadda bayanin ya shafe su. Ƙarshen jawabin shi ne lokacin da mai jawabin ya bar kan dakalin. Hakazalika, kamar yadda yake a cikin Littafi Mai Tsarki, furcin nan “ƙarewar zamani” yana nuni ne ga somawar lokaci har zuwa ƙarshenta.

3. Waɗanne abubuwa ne suka faru a lokacin dawowar Yesu?

3 “Dawowar” da manzannin suka yi tambaya a kai kuma fa? Wannan ita ce kalmar Helenanci da aka fassara pa·rou·siʹa.a Pa·rou·siyar Kristi ko kuma dawowarsa ta soma ne sa’ad da aka naɗa Yesu ya zama Sarki a sama a shekara ta 1914 kuma za ta ci gaba har lokacin “ƙunci mai-girma,” sa’ad da zai dawo don ya halaka miyagu. (Mat. 24:21) Abubuwa dabam dabam masu yawa, har da “kwanaki na ƙarshe” na wannan mugun zamanin, tattara zaɓaɓɓu, da kuma tashinsu daga matattu zuwa sama duk sun faru ne a wannan lokaci na bayyanuwar Yesu. (2 Tim. 3:1; 1 Kor. 15:23; 1 Tas. 4:15-17; 2 Tas. 2:1) Za a iya cewa wannan lokacin na “ƙarewar zamani” (syn·teʹlei·a) ya yi daidai da lokacin aka kira dawowar Kristi (pa·rou·siʹa).

Lokaci Mai Tsawo

4. Ta yaya ne bayyanuwar Yesu ta yi kama da abubuwan da suka faru a zamanin Nuhu?

4 Domin kalmar nan pa·rou·siʹa tana nufin lokaci mai tsawo, hakan ya jitu da abin da Yesu ya ce game da bayyanuwarsa. (Ka karanta Matta 24:37-39.) Idan ka lura za ka ga cewa Yesu bai kwatanta bayyanuwarsa da ɗan gajeren lokacin da aka yi Rigyawa a zamanin Nuhu ba. Maimakon haka, ya kwatanta bayyanuwarsa da lokaci mai tsawo da ya kai ga Rigyawa. Wannan ya haɗa da gina kwalekwalen da Nuhu ya yi da kuma aikin wa’azi, har zuwa lokacin da aka soma Rigyawar. Waɗannan abubuwan sun faru ne cikin shekaru masu yawa. Hakazalika, bayyanuwar Kristi ta haɗa da abubuwan da za su faru har lokacin ƙunci mai girma.—2 Tas. 1:6-9.

5. Ta yaya ne kalaman da ke cikin Ru’ya ta Yohanna sura 6 ta nuna cewa bayyanuwar Yesu lokaci ne mai tsawo?

5 Wasu annabce-annabce na Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa bayyanuwar Kristi tana nuni ne ga lokaci mai tsawo ba wai kawai ga zuwansa na halaka miyagu ba. Littafin Ru’ya ta Yohanna ta nuna Yesu yana kan farin doki kuma an ɗora masa kambi. (Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 6:1-8, Littafi Mai Tsarki.) Bayan da ya zama Sarki a shekara ta 1914, an kwatanta cewa Yesu ya “fita yana mai nasara domin ya ƙara cin nasara.” Labarin ya nuna cewa wasu mahaya da ke kan dawakai kala dabam dabam suna bin sa a baya. A annabce wannan yana waƙiltar yaƙi, ƙarancin abinci, cuta, kuma waɗannan abubuwan duk sun auku ne a cikin wannan lokaci mai tsawo da aka kira “kwanaki na ƙarshe.” Muna ganin cikar wannan annabcin a zamaninmu.

6. Menene Ru’ya ta Yohanna sura 12 ta sa muka fahimta game da bayyanuwar Kristi?

6 Ru’ya ta Yohanna sura 12 ta ba da ƙarin haske game da Mulkin Allah da aka kafa a sama. A nan mun karanta game da yaƙin da aka yi a sama. Miƙa’ilu, Yesu Kristi a matsayinsa a sama, tare da mala’ikusa sun yi yaƙi da Iblis da kuma aljanunsa. A sakamakon haka, an jefo Shaiɗan Iblis da aljanunsa zuwa duniya. A nan, labarin ya gaya mana cewa Iblis yana fushi sosai “domin ya sani sauran zarafinsa kaɗan ne.” (Ka karanta Ru’ya ta Yohanna 12:7-12.) Babu shakka, bayan da aka kafa Mulkin Kristi a sama ne aka sami lokaci mai tsawo na ƙarin “kaito” ga duniya da mazaunanta.

7. Mecece Zabura ta biyu ta ce, kuma wace dama ce aka ambata a ciki?

7 Ita ma zabura ta biyu ta yi annabci game da naɗa Yesu a matsayin Sarki a kan Dutsen Sihiyona na sama. (Ka karanta Zabura 2:5-9; 110:1, 2.) Amma, wannan zaburar ta nuna cewa an ba masu mulka duniya da kuma talakawansu lokaci mai tsawo don su miƙa wuyansu ga sarautar Kristi. An aririce su su “yi hikima” kuma su bari a ‘hora’ su. Hakika, a wannan lokacin “masu-albarka ne dukan waɗanda ke dogara gareshi [Allah]” ta wajen bauta wa Jehobah da kuma Sarkin da ya naɗa. Saboda haka, an ba da dama a lokacin bayyanuwar Kristi a ikon sarauta.—Zab. 2:10-12.

Fahimtar Alamar

8, 9. Su wanene za su fahimci alamar bayyanuwar Kristi kuma su fahimci ma’anarta?

8 Sa’ad da Farisawa suka tambaye shi lokacin da Mulki zai zo, Yesu ya amsa da cewa ba za a ‘ganta da ido ba’ kamar yadda suke zato. (Luk 17:20, 21, Littafi Mai Tsarki.) Marasa bi ba za su fahimci hakan ba. Yaya kuwa za su iya? Ba su ma amince ba cewa Yesu ne Sarkinsu na nan gaba ba. To, su waye ne za su fahimci alamar bayyanuwar Kristi kuma su gane muhimmancinsa?

9 Yesu ya ci gaba da cewa almajiransa za su ga alamar kamar yadda za su ga “walƙiya, sa’anda tana walkatawa daga wajen wani sashen sama, tana haskakawa har zuwa wancan sashen sama.” (Ka karanta Luka 17:24-29.) Yana da kyau mu lura cewa Matta 24:23-27 ta bayyana dalla-dalla cewa Yesu yana magana ne game da bayyanuwarsa.

Tsarar da ta Fahimci Alamar

10, 11. (a) A dā ta yaya aka bayyana ma’anar “wannan tsara” da ke Matta 24:34? (b) Su wanene almajiran Yesu suka fahimci cewa suna cikin wannan “tsara”?

10 A dā, wannan mujallar ta bayyana cewa a ƙarni na farko, ‘wannan tsara’ da aka ambata a Matta 24:34 tana nufin “taron Yahudawan da suka ƙi tuba a wannan lokacin.”b Wannan bayanin ya zama gaskiya ne domin a sauran wuraren da Yesu ya yi amfani da wannan kalmar “tsara” ba ta da ma’ana mai kyau, kuma a yawancin lokatai, Yesu yana amfani ne da siffa marar kyau, kamar ‘muguwa’ don kwatanta tsarar. (Mat. 12:39; 17:17; Mar. 8:38) Saboda haka, a dā an fahimci cewa a cikarta ta zamani, Yesu yana nuni ne ga muguwar “tsara” na marasa bi waɗanda za su ga alamun da ke nuna “ƙarewar zamani” (syn·teʹlei·a) da kuma ƙarshen zamani (teʹlos).

11 Hakika, sa’ad da Yesu ya yi amfani da kalmar nan “tsara” a hanya marar kyau, yana magana ne ga ko kuwa game da miyagun da ke zamaninsa. Amma abin da kalamansa da aka rubuta a Matta 24:34 suke nufi ke nan? Ka tuna cewa almajiran Yesu guda huɗu sun je sun same shi a “kaɗaice.” (Mat. 24:3, Littafi Mai Tsarki.) Tun da yake Yesu bai yi amfani da siffa marar kyau ba sa’ad da yake yi musu magana game da “wannan tsara,” babu shakka, manzannin sun fahimci cewa su da ’yan’uwansu manzanni suna cikin ‘tsarar’ da ba za ta shuɗe ba har “sai an cika waɗannan abu duka.”

12. Menene wannan batun ya bayyana game da waɗanda Yesu yake magana game da su sa’ad da ya yi amfani da kalmar nan “tsara”?

12 Menene zai sa mu kammala cewa hakan gaskiya ne? Za mu yi hakan ne ta wajen bincika batun sosai. Kamar yadda aka rubuta a Matta 24:32, 33, Yesu ya ce: ‘Daga itacen ɓaure fa sai ku koyi misalinsa: sa’anda reshensa ya rigaya ya yi tabshi, yana kuwa hudo da ganyaye, kun san bazara ta kusa; hakanan ku kuma, lokacida kun ga waɗannan al’amura duka, ku sani ya yi kusa, har bakin ƙofa.’ (Ka gwada da Markus 13:28-30; Luka 21:30-32.) Bayan haka, a Matta 24:34, mun karanta: ‘Hakika, ina ce maku Wannan tsara ba za ta shuɗe ba sai an cika waɗannan abu duka.’

13, 14. Me ya sa za mu iya cewa wannan “tsara” da Yesu ya ambata tana nufin almajiransa?

13 Yesu ya ce almajiransa, waɗanda za a shafa da ruhu mai tsarki ne za su iya fahimtar wasu abubuwa sa’ad da suka ga “waɗannan abu duka” suna faruwa. Saboda haka, Yesu yana magana ne game da almajiransa sa’ad da ya faɗi kalaman da muka karanta a aya ta 34: “Wannan tsara ba za ta shuɗe ba sai an cika waɗannan abu duka.”

14 Ba kamar marasa bi ba, almajiran Yesu za su ga alamar kuma su fahimci muhimmancinta. Za su ‘koya’ daga fasalolin alamar kuma su “san” ma’anarsu ta gaskiya. Za su fahimci cewa “ya yi kusa, har bakin ƙofa.” Ko da yake gaskiya ne cewa Yahudawa waɗanda ba mabiya ba ne da kuma shafaffun Kiristoci masu aminci sun ga kaɗan daga cikin cikawar kalaman Yesu a ƙarni na farko, mabiyansa shafaffu na wannan lokacin kaɗai ne suka koya daga abubuwan da suka faru, kuma su kaɗai ne kawai suka fahimci ainihin ma’anar abubuwan da suka gani.

15. (a) Su wanene wannan “tsara” na wannan zamanin da Yesu ya ambata? (b) Me ya sa ba za mu iya lissafa ainihin tsawon “wannan tsara” ba? (Ka duba akwatin da ke shafi na 25.)

15 Waɗanda ba su da fahimi na ruhaniya a yau suna jin cewa ba a ‘gan’ alamar bayyanuwar Kristi ba. Suna tunanin cewa komi yana tafiya kamar dā. (2 Bit. 3:4) A wata sassa kuwa, ’yan’uwan Kristi shafaffu masu aminci, wato, rukunin Yohanna na zamani sun fahimci wannan alamar kamar walƙiya kuma sun fahimci ainihin ma’anarta. A matsayinsu na rukuni, waɗannan shafaffun su ne “tsara” na wannan zamanin da ba za su shuɗe ba har “sai an cika waɗannan abu duka.”c Wannan ya nuna cewa wasu a cikin shafaffu ’yan’uwan Kristi za su kasance a raye a duniya har somawar babban tsanani da aka annabta.

“Ku Yi Tsaro”

16. Menene dukan almajiran Kristi za su yi?

16 Muna bukatar fiye da sanin alamar kawai. Yesu ya ci gaba da cewa: ‘Abin da ni ke ce maku ina ce ma duka, Ku yi tsaro.’ (Mar. 13:37) Wannan shi ne abin da ya fi muhimmanci ga dukanmu a yau ko da mu shafaffu ne ko kuwa taro mai girma. Shekaru fiye da tasa’in sun wuce tun sa’ad da aka naɗa Yesu ya zama Sarki a sama a shekara ta 1914. Ko da yake ba shi da sauƙi, dole ne mu kasance a shirye kuma mu ci gaba da yin tsaro. Sanin cewa Kristi yana sarauta a yanzu zai taimaka mana mu yi hakan. Kuma hakan ya sa mu san cewa nan ba da daɗewa ba zai zo ya halaka maƙiyansa “cikin sa’a da ba [mu] sa tsammani ba.”—Luka 12:40.

17. Yaya ya kamata mu ji domin mun fahimci ma’anar bayyanuwar Kristi, kuma menene ya kamata mu ƙudurta cewa za mu yi?

17 Fahimin da muke da shi game da bayyanuwar Kristi yana taimaka mana mu daɗa sanin da muke da shi na gaggawar lokaci. Mun san cewa Yesu ya riga ya bayyana kuma ya soma sarauta a sama a matsayin Sarki tun shekara ta 1914. Nan ba da daɗewa ba zai zo ya halaka miyagu kuma ya kawo canji mai yawa a duniya gabaki ɗaya. Saboda haka, muna bukatar mu ƙudurta sosai fiye da dā cewa za mu saka hannu sosai a aikin da Yesu ya annabta sa’ad da ya ce: ‘Za a kuma yi bisharan nan ta Mulkin Sama ko’ina a duniya domin shaida ga dukkan al’ummai. Sa’an nan kuma sai ƙarshen [teʹlos] ya zo.’—Mat. 24:14.

[Hasiya]

a Don samun ƙarin bayani game da pa·rou·siʹa, ka duba Insight on the Scriptures, Littafi na 2, shafuffuka na 676-679.

b Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Nuwamba, 1995, shafuffuka na 20-24, 27.

c Wannan tsara kamar ta jitu da cikar wahayi na farko da ke cikin littafin Ru’ya ta Yohanna. (R. Yoh. 1:10–3:22) Wannan sashen na ranar Ubangiji ya soma ne tun daga shekara ta 1914 kuma zai ci gaba har sai shafaffe mai aminci na ƙarshe ya mutu kuma aka ta da shi daga matattu.—Ka duba littafin nan Revelation—Its Grand Climax At Hand! shafi na 24, sakin layi na 4.

Mecece Amsarka?

• Ta yaya muka san cewa bayyanuwar Yesu lokaci ne mai tsawo?

• Su wanene suka gane bayyanuwar Yesu kuma suka fahimci ma’anarta?

• Su wanene wannan tsara na zamani da aka ambata a Matta 24:34?

• Me ya sa ba za mu iya lissafa ainihin yawan lokacin “wannan tsara” ba?

[Akwati a shafi na 25]

Za mu iya lissafa tsawon “Wannan Tsara”?

Kalmar nan “tsara” a yawancin lokaci tana nufin mutane masu shekaru dabam dabam waɗanda suka rayu a wani lokaci ko yanayi. Alal misali Fitowa 1:6 ta ce: ‘Yusufu ya mutu, da dukan ’yan’uwansa, da dukan wannan tsara.’ Yusufu da ’yan’uwansa suna da shekaru dabam dabam, amma dukansu sun shaida abubuwan da suka faru a lokacinsu. Waɗanda suke cikin ‘wannan tsara’ sun haɗa da wasu a cikin ’yan’uwan Yusufu da suka girme shi. Kuma Yusufu ya riga wasu a cikinsu mutuwa. (Far. 50:24) Wasu kuma a cikin “wannan tsara,” kamar su Benyamin, an haife su ne bayan da aka haifi Yusufu kuma wataƙila sun rayu har bayan mutuwar Yusufu.

Saboda haka, sa’ad da aka yi amfani da kalmar nan “tsara” wajen yin nuni ga mutanen da suka rayu a wani lokaci na musamman, ba za a iya cewa ga iyakar lokacin ba amma dai tana da ƙarshe kuma ba zai ɗauki dogon lokaci ba. Saboda haka, ta wajen yin amfani da furcin nan “wannan tsara,” kamar yadda aka rubuta a Matta 24:34, Yesu bai ambata wani abin da zai taimaka wa almajiransa su san lokacin da “kwanaki na ƙarshe” zai ƙare ba. Maimakon haka, Yesu ya nanata cewa ba za su san “ranan nan da sa’an nan ba.”—2 Tim. 3:1; Mat. 24:36.

[Hoto a shafi na 22]

Bayan da aka naɗa shi Sarki a shekara ta 1914, an kwatanta cewa Yesu ya ci gaba da “yin nasara”

[Hoto a shafi na 24]

“Wannan tsara ba za ta shuɗe ba sai an cika waɗannan abu duka”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba