Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • bm sashe na 22 p. 25
  • Manzanni Sun Yi Wa’azi da Gaba Gaɗi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Manzanni Sun Yi Wa’azi da Gaba Gaɗi
  • Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Makamantan Littattafai
  • Yesu Ya Zabi Shawulu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Wadanda Suke Yin Mugun Abu Za Su Iya Canjawa Kuwa?
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • A Hanyar Zuwa Dimaska
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Yin “Biyayya ta Fi Hadaya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
bm sashe na 22 p. 25

Sashe 22

Manzanni Sun Yi Wa’azi da Gaba Gaɗi

Ikilisiyar Kirista ta ƙaru sosai duk da tsanantawa

KWANAKI goma bayan Yesu ya koma sama, almajiransa wajen 120 sun taru a wani gida a Urushalima a lokacin Idin Yahudawa na Fentakos 33 A.Z. Kwaram, sai ƙara kamar na hucin iska mai ƙarfi ya cika gidan. Ta hanyar mu’ujiza, sai almajiran suka soma yin magana a harsunan da ba su sani ba. Menene ya jawo waɗannan abubuwa masu ban mamaki? Allah ya ba almajiran ruhunsa mai tsarki.

A waje, akwai taron mutane domin baƙi sun zo daga ƙasashe masu yawa domin idin. Sun yi mamakin jin almajiran Yesu suna yin yarensu sarai. Sa’ad da yake bayyana abin da ya faru, Bitrus ya yi nuni ga annabcin annabi Joel da ya ce Allah zai “zuba” ruhunsa, wanda zai ba da kyauta na mu’ujiza ga waɗanda suka same shi. (Joel 2:28, 29) Wannan shaida mai girma ta ruhu mai tsarki ya bayyana sarai cewa wani canji na musamman ya auku: Tagomashin Allah ya bar Isra’ila kuma ya koma kan sabuwar ikilisiyar Kirista da aka kafa. A yanzu, waɗanda suke son su bauta wa Allah yadda yake so suna bukatan su zama mabiyan Kristi.

Amma, hamayya ta yi tsanani sosai, kuma maƙiya sun jefa manzannin cikin kurkuku. Amma, daddare, mala’ikan Jehobah ya buɗe ƙofofin kurkukun kuma ya gaya wa manzannin cewa su ci gaba da yin wa’azi. Washegari, sun ci gaba da yin hakan. Sun shiga cikin haikali kuma suka soma koyar da bishara game da Yesu. Masu hamayya da addininsu sun yi fushi sosai kuma suka umurce su su daina yin wa’azi. Da gaba gaɗi, manzannin sun mai da martani: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.”—Ayyukan Manzanni 5:28, 29.

Tsanantawar ta yaɗu. Wasu Yahudawa sun zargi almajiri Istifanus da yin saɓo kuma suka jefe shi da duwatsu har ya mutu. Wani matashi mai suna Shawulu ɗan birnin Tarsus ya shaida kisan kuma ya amince da shi. Daga nan ya tafi Dimashƙa don ya kama duk wani mabiyin Kristi. Yayin da Shawulu yake kan hanya, sai wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi kuma wata murya ta ce: “Shawulu, Shawulu, don me ka ke tsanantata?” Domin hasken ya kashe mashi ido, sai Shawulu ya ce: “Wanene kai?” Sai muryar ta ce: “Ni ne Yesu.”—Ayyukan Manzanni 9:4, 5.

Kwana uku bayan hakan, Yesu ya aika wani almajiri mai suna Hananiya ya warkar da makantar Shawulu. An yi wa Shawulu baftisma kuma ya soma yin wa’azi da gaba gaɗi game da Yesu. An san Shawulu da sunan nan manzo Bulus kuma ya zama mai ƙwazo a cikin ikilisiyar Kirista.

Almajiran Yesu suna yin wa’azin bisharar Mulkin Allah ne ga Yahudawa da ’yan Samariya kawai. Sai mala’ika ya bayyana ga Karniliyus, wani shugaban sojojin Roma, mai tsoron Allah, kuma ya gaya masa cewa ya aika a kira manzo Bitrus. Tare da wasu, Bitrus ya yi wa’azi ga Karniliyus da iyalinsa. Yayin da Bitrus yake magana, sai ruhu mai tsarki ya sauka a kan waɗannan ’yan Al’ummai masu bi, kuma manzon ya ba da umurni cewa a yi musu baftisma a cikin sunan Yesu. Hanyar samun rai na har abada ta buɗu ga dukan al’ummai. Ikilisiyar tana shirye ta yaɗa bisharar zuwa nesa da kuma dukan duniya.

—An ɗauko daga Ayyukan Manzanni 1:1-11:21.

◼ Menene ya faru a lokacin Idin Fentakos?

◼ Wane mataki ne maƙiya suka ɗauka game da wa’azin da almajiran Yesu suke yi?

◼ Ta yaya hanyar samun rai na har abada ta buɗu ga mutanen dukan al’ummai?

[Taswirai a shafi na 25]

Farawa

Fitowa

Levitikus

Littafin Lissafi

Kubawar Shari’a

Joshua

Alƙalawa

Ruth

1 Sama’ila

2 Sama’ila

1 Sarakuna

2 Sarakuna

1 Labarbaru

2 Labarbaru

Ezra

Nehemiya

Esther

Ayuba

Zabura

Misalai

Mai-Wa’azi

Waƙar Waƙoƙi

Ishaya

Irmiya

Makoki

Ezekiel

Daniyel

Hosiya

Joel

Amos

Obadiya

Yunana

Mikah

Nahum

Habakkuk

Zafaniya

Haggai

Zakariya

Malakai

Matta

Markus

Luka

Yohanna

Ayyukan Manzanni ●

Romawa

1 Korintiyawa

2 Korintiyawa

Galatiyawa

Afisawa

Filibiyawa

Kolosiyawa

1 Tasalonikawa

2 Tasalonikawa

1 Timotawus

2 Timotawus

Titus

Filimon

Ibraniyawa

Yaƙub

1 Bitrus

2 Bitrus

1 Yohanna

2 Yohanna

3 Yohanna

Wasiƙa ta Yahuda

Ru’ya ta Yohanna

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba