Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • rk sashe na 6 pp. 15-17
  • Mene ne Allah Ya Nufa ga Duniya?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Allah Ya Nufa ga Duniya?
  • Cikakken Imani Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa
  • Makamantan Littattafai
  • Minene Nufin Allah ga Duniya?
    Menene Allah Yake Bukata a Garemu?
  • A Ina Aljannar da ke Cikin Littafi Mai Tsarki Take?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Aljanna a Duniya, Gaskiya Ce ko Kage?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Mene Ne Nufin Allah ga Duniya?
    Albishiri Daga Allah!
Dubi Ƙari
Cikakken Imani Zai Sa Ka Yi Farin Ciki a Rayuwa
rk sashe na 6 pp. 15-17

SASHE NA 6

Mene ne Allah Ya Nufa ga Duniya?

ALLAH ya halicci duniya domin ta zama wurin zama mai kyau ga ’yan Adam. Kalmarsa ta ce: “Sammai na Ubangiji ne, amma ya ba da duniya ga ’yan Adam.”—Zabura 115:16.

Kafin ya halicci mutum na farko, Adamu, Allah ya zaɓi wani ƙaramin yanki a duniya mai suna Adnin kuma ya shuka kyakkyawar lambu. Nassosi sun faɗi cewa kogin Euphrates da Hiddekel sun fito ne daga Adnin.a Ana tunanin cewa Adnin ya kasance ne a yankin da ake kira a yau Turkiyya ta gabas. Hakika, lambun Adnin ya kasance ne a duniya!

Allah ya halicci Adamu kuma ya sanya shi a cikin lambun Adnin “domin shi aikace ta, shi tsare ta kuma.” (Farawa 2:15) Bayan haka, Allah ya halicci mata ya ba Adamu, wato, Hauwa’u. Allah ya ba ma’auratan doka: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya, ku mallake ta.” (Farawa 1:28) A bayyane yake cewa Allah ‘ya halicce [duniya] ba wofi ba, [amma] ya kamanta ta domin wurin zama.’—Ishaya 45:18.

Amma, Adamu da Hawa’u sun yi tawaye ga Allah ta wajen karya dokarsa da gangan. Saboda haka, Allah ya kore su daga lambun Adnin. An yi rashin Aljanna. Ɓarnar da zunubin Adamu ya jawo bai tsaya a nan ba kawai. Nassosin sun gaya mana: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.”—Romawa 5:12.

Jehobah ya watsar da nufinsa na assali kuwa, wato, duniya ta zama aljanna inda mutane masu farin ciki za su zauna a cikinta? A’a! Allah ya ce: “Maganata, wadda ta ke fitowa daga cikin bakina za ta zama: ba za ta koma wurina wofi ba, amma za ta cika abin da na nufa, za ta yi albarka kuma a cikin saƙona.” (Ishaya 55:11) Za a sake mai da duniya zuwa Aljanna!

Yaya rayuwa za ta kasance a cikin Aljanna? Ka yi la’akari da alkawuran da aka yi a cikin Nassin da ke shafuffuka biyu na gaba.

a Farawa 2:10-14 ta ce: “Kogi kuma ya fito daga cikin Adnin domin ya shayadda gona; daga can kuma ya rabu, ya zama kawuna huɗu. Sunan na farin Pishon ne . . . Sunan kogi na biyu kuma Gihon ne . . . Sunan kogi na uku kuma Hiddekel ne [ko Tigris]: shi ne wanda ke gudu gaban Assyria. Kogi na huɗu kuma Euphrates ne.” Babu wanda ya san inda koguna biyu na farko suke.

Yaya Za Ka Amsa?

  • Mene ne ainihin nufin Allah ga duniya da mutum?

  • Ta yaya muka san cewa Allah zai cika wannan nufin na sa?

Mutane a Aljanna

Aljanna a Duniya a Nan Gaba

Za a ta da matattu: “Dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma”—Yohanna 5:28, 29.

Babu tsufa, rashin lafiya, ko mutuwa: “Wanda ya ke zaune a ciki ba za ya ce, Ina ciwo ba.” (Ishaya 33:24) Allah “zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba” ba.—Ru’ya ta Yohanna 21:4.

Kyakkyawan abinci mai yawa: “Ƙasa tā bada anfaninta: Allah wanda shi ke Allahnmu, za ya albarkace mu.”—Zabura 67:6.

Gidaje masu kyau da aiki mai gamsarwa: “Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki . . . zaɓaɓuna kuma za su daɗe suna jin daɗin aikin hannuwansu.”—Ishaya 65:21, 22.

Za a kawar da yaƙi, aikata laifi, ko mugunta: Jehobah “ya sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya.” (Zabura 46:9) “Za a datse miyagu daga cikin ƙasan.”—Misalai 2:22.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba