Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • yc darasi na 2 pp. 6-7
  • Yadda Rifkatu Ta Sa Jehobah Farin Ciki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Rifkatu Ta Sa Jehobah Farin Ciki
  • Ku Koyar da Yaranku
  • Makamantan Littattafai
  • Rifkatu Tana Son Ta Faranta Ran Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • “Zan Tafi”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Ishaku Ya Auri Matar Kirki
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Tagwaye Da Suka Bambanta
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Ku Koyar da Yaranku
yc darasi na 2 pp. 6-7
Eliezer, Rifkatu, da bayin Ibrahim, da kuma rakuma goma, suna tafiya mai nisa zuwa Kan’ana

DARASI NA 2

Yadda Rifkatu Ta Sa Jehobah Farin Ciki

Rifkatu mace ce da take ƙaunar Jehobah. Sunan mijinta Ishaƙu. Shi ma yana ƙaunar Jehobah. Ta yaya Rifkatu da Ishaƙu suka haɗu? Mene ne ta yi da ya nuna cewa tana so ta sa Jehobah farin ciki? Bari mu koya game da Ishaƙu, mijin Rifkatu tukun.

Ibrahim da Saratu ne iyayen Ishaƙu. Suna da zama ne a ƙasar Kan’ana, kuma mutanen ƙasar ba sa bauta wa Jehobah. Amma, Ibrahim yana so ɗansa ya auri mace da take bauta wa Jehobah. Saboda haka, wataƙila bawansa Eliezer ne ya aika ya nemo wa Ishaƙu mata a wani birni mai suna Haran. Wasu dangin Ibrahim suna da zama a wannan birnin.

Rifkatu tana zuba wa rakuman Eliezer ruwa don su sha

Rifkatu ta yarda ta yi aiki tukuru don ta debo wa rakuman ruwa

Eliezer ya yi tafiyar ne tare da wasu bayin Ibrahim. Tafiyar tana da nisa sosai, kuma sun tafi da raƙuma guda goma da ke ɗauke da abinci da tsaraba. Ta yaya Eliezer zai san macen da ya kamata ya zaɓa wa Ishaƙu? Sa’ad da Eliezer da sauran bayin suka isa birnin Haran, sai suka tsaya a bakin wata rijiya. Me ya sa? Domin Eliezer ya san cewa ba da daɗewa ba, mutane za su zo ɗibar ruwa. Sai ya yi addu’a ga Jehobah cewa: ‘Duk macen da na ce ta ba ni ruwa kuma ta yarda ta ba ni da raƙumana ruwa, to zan san cewa ita ce macen da ka zaɓa.’

Ana nan sai wata budurwa mai suna Rifkatu ta zo bakin rijiyar. Littafi Mai Tsarki ya ce ita kyakkyawa ce. Eliezer ya roƙe ta ruwa, sai ta ce: ‘Hakika, zan ba ka ruwa sa’an nan zan je in ɗiba ma raƙumanka ruwa su ma su sha.’ Ka yi tunanin yadda Rifkatu take ta ɗebo ruwa daga rijiyar domin raƙuma suna shan ruwa sosai. Ka ga yadda take aiki sosai a wannan hoton?— Eliezer ya yi mamakin yadda Jehobah ya amsa addu’arsa.

Eliezer ya ba Rifkatu abubuwa da yawa masu kyau, sai Rifkatu ta kai shi da sauran bayin gidansu. Eliezer ya gaya wa mutanenta abin da ya sa Ibrahim ya aiko shi da kuma yadda Jehobah ya amsa addu’arsa. Iyalin Rifkatu sun yi farin ciki domin Ishaƙu zai aure ta.

Rifkatu ta bi Eliezer zuwa Kan’ana kuma Ishaƙu ya aure ta

Amma kana ganin Rifkatu za ta so ta auri Ishaƙu?— Rifkatu ta san cewa Jehobah ne ya aiko Eliezer, shi ya sa a lokacin da iyalinta suka tambaye ta ko tana so ta tafi ƙasar Kan’ana don ta zama matar Ishaƙu, ta ce: ‘E, ina so in tafi.’ Ba tare da ɓata lokaci ba ta bi Eliezer. Ishaƙu ya aure ta sa’ad da aka kawo ta ƙasar Kan’ana.

Jehobah ya yi wa Rifkatu albarka domin ta yi abin da ya yake so. Daga cikin iyalinta ne aka haifi Yesu shekaru da yawa bayan zamaninta. Idan ka bi misalin Rifkatu kuma ka sa Jehobah farin ciki, Jehobah zai yi maka albarka.

KARANTA NASSOSIN NAN

  • Farawa 12:4, 5; 24:1-58, 67

TAMBAYOYI:

  • Wace ce Rifkatu?

  • Me ya sa Ibrahim ba ya so Ishaƙu ya yi aure daga ƙasar Kan’ana?

  • Ta yaya Eliezer ya san ko Rifkatu ce macen da ya kamata Ishaƙu ya aura?

  • Mene ne ya kamata mu yi don mu zama kamar Rifkatu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba