Ku Koyar Da Yaranku
Rifkatu Tana Son Ta Faranta Ran Jehobah
RIFKATU sanannen suna ne a wurare da yawa a yau. Ka san wadda take da irin wannan sunan kuwa?—a Rifkatu wata mata ce mai muhimmanci a cikin littafin da aka fi sani a dukan duniya, wato, Littafi Mai Tsarki. Menene ka sani game da ita?— Ya kamata mu so sanin Rifkatu domin misalinta zai iya taimaka mana mu bauta wa Allah na gaskiya, Jehobah.
Rifkatu ita ce mace ta biyu wadda aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki da ta zama mai bauta wa Jehobah. Ka san ko wace mata ce na farko?— Saratu ce, matar Ibrahim. Sa’ad da ta tsufa, Saratu ta haifi Ishaƙu—ɗanta tilo. Yanzu, bari mu ga yadda Rifkatu ta yarda ta yi abin da Jehobah yake so da kuma yadda ta saɗu da Ishaƙu.
Shekaru sittin sun wuce tun lokacin da Allah ya ce wa Ibrahim da Saratu su fita daga ƙasar Haran zuwa ƙasar Ka’anan. Sa’ad da Ibrahim da Saratu suka tsufa sosai, Allah ya yi musu alkawarin ɗa wanda za a kira Ishaƙu. Kamar yadda ka sani, iyayen Ishaƙu suna ƙaunarsa sosai. Sa’ad da Saratu ta mutu a ’yar shekara 127, ɗanta, Ishaƙu, ya riga ya girma sosai kuma ya yi baƙin cikin yin rashin mahaifiyarsa sosai. Ibrahim ba ya son Ishaƙu ya auri mace daga Ka’anan domin waɗannan mutanen ba sa bauta wa Jehobah. Saboda haka, ya aiki bawansa, wataƙila Eliezer, ya zaɓar wa Ishaƙu mata daga cikin iyalin Ibrahim a ƙasar Haran, ƙasa mai nisa fiye da mil ɗari biyar!—Farawa 12:4, 5; 15:2; 17:17, 19; 23:1.
Da sannu sannu Eliezer, tare da raƙuma goma da suke ɗauke da kaya da tsarabar amarya, suka isa ƙasar Haran tare da wasu bayin Ibrahim. Sun tsaya a bakin wata rijiya domin Eliezer ya san cewa da rana, mutane sukan zo ɗibar ruwan da dabbobinsu da kuma iyalinsu za su sha. Yanzu sai Eliezer ya yi addu’a cewa wadda zai zaɓa ta zama matar Ishaƙu ta zama wacce za ta amince da bukatar ruwan da zai yi, ta wajen cewa: “Sha, in ba raƙumanka kuma su sha.”
Ainihin abin da ya faru kenan! Rifkatu ta isa bakin rijiyar kuma “kyakkyawa ce ƙwarai.” Sa’ad da Eliezer ya nemi ruwan sha, ta ce: “Zan ɗiba wa raƙumanka kuma.” Sa’ad da take gudu “ta ɓulɓule ruwan tulunta cikin kwango, ta sāke tafiya rijiyan a guje domin ta ɗiba ruwa,” Eliezer ya kalle ta ‘da mamaki.’ Ka yi tunani! Don ta ƙosar da raƙuma goma masu ƙishirwa, Rifkatu tana bukatan ta ɗebo aƙalla galan 250 na ruwa!
Eliezer ya ba Rifkatu kyauta masu kyau, kuma ya samu labari cewa ita ’yar Bethuel ce, dangin Ibrahim. Rifkatu ta gayyaci Eliezer da abokansa zuwa gidansu don su ‘sauka a gidansu.’ Sai ta ruga gida don ta gaya musu game da baƙin da Ibrahim ya aika tun daga ƙasar Ka’anan don su ziyarce su.
Sa’ad da ɗan’uwan Rifkatu, Laban, ya ga tsaraba masu tsada da aka ba ’yar’uwarsa kuma ya san ko wanene Eliezer, ya marabce shi cikin ɗaki. Amma Eliezer ya ce: “Ba ni ci, sai na iyar da saƙona tukuna.” Sai ya bayyana dalilin da ya sa Ibrahim ya aiko shi. Bethuel, da matarsa, da kuma Laban sun yi farin ciki sosai kuma sun amince da auren.
Bayan sun ci abinci, Eliezer da waɗanda suke tare da shi suka kwana a wurin. Washegari, Eliezer ya ce: “Ku sallame ni in tafi wurin ubangidana.” Amma mahaifiyar Rifkatu da ɗan’uwanta suna son su zauna aƙalla kwanaki “goma.” Sa’ad da aka tambayi Rifkatu ko za ta bi su ba tare da ɓata lokaci ba, ta amsa, ‘zan tafi.’ Kuma nan da nan ta tafi tare da Eliezer. Sa’ad da suka isa wurin, ta zama matar Ishaƙu.—Farawa 24:1-58, 67.
Kana tsammanin cewa yana da sauƙi Rifkatu ta bar iyalinta da ƙawayenta kuma ta tafi wuri mai nisa, da sanin cewa wataƙila ba za ta sake ganinsu ba?— A’a, bai kasance da sauƙi ba. Amma dai, an albarkaci Rifkatu domin ta amince ta yi abin da Jehobah yake so. Ta zama ɗaya daga cikin kakannin Mai-Cetonmu, Yesu Kristi. Za a albarkace mu idan kamar ita, mun yarda mu yi abin da ke faranta wa Jehobah rai.—Romawa 9:7-10.
[Hasiya]
a Idan kana karanta wa yaro, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata ka ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa.
TAMBAYOYI:
▪ Wacece Rifkatu, kuma a ina ne Eliezer ya saɗu da ita?
▪ Me ya sa Ibrahim baya so Ishaƙu ya auri ’yar Ka’aniyawa?
▪ Yaya Rifkatu ta nuna cewa za ta zama matar kirki?
▪ Menene za mu iya yi don mu zama kamar Rifkatu?