Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 8 p. 26-p. 27 par. 1
  • Ibrahim da Saratu Sun Yi Biyayya ga Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ibrahim da Saratu Sun Yi Biyayya ga Allah
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Ibrahim, Abokin Allah
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Jehobah Ya Kira Shi “Aminina”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Allah Ya Gwada Bangaskiyar Ibrahim
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Kana Jiran “Birnin Nan Wanda Yake da Tushe”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 8 p. 26-p. 27 par. 1
Ibrahim da Saratu sun kwashe kayansu za su bar kasar Ur

DARASI NA 8

Ibrahim da Saratu Sun Yi Biyayya ga Allah

Akwai wani birni mai suna Ur kuma wannan birnin bai da nisa daga Babel. Mutanen birnin ba sa bauta wa Jehobah. Amma akwai wani mutumi mai suna Ibrahim a birnin Ur da ke bauta wa Jehobah kaɗai.

Jehobah ya ce wa Ibrahim: ‘Ka fita daga ƙasarka da kuma mutanenka zuwa ƙasar da zan nuna maka.’ Sai Allah ya yi masa alkawari cewa: ‘Yaranka za su yi yawa sosai, kuma dukan mutanen duniya za su sami albarka saboda kai.’

Ko da yake Ibrahim bai san inda Jehobah ya ce ya je ba, amma ya nuna bangaskiya. Sai Ibrahim da matarsa Saratu da babansa Terah da kuma Lutu yaron ɗan’uwan Ibrahim suka kwashe kaya, suka soma tafiya mai nisa.

Shekarun Ibrahim 75 ne sa’ad da shi da iyalinsa suka isa inda Jehobah ya ce su je. Sunan ƙasar Kan’ana. Sai Allah ya yi wa Ibrahim alkawari cewa: ‘Zan ba yaranka duka wannan ƙasa da ta kewaye ka.’ Amma Ibrahim da Saratu sun tsufa kuma ba su da yara. To, ta yaya Jehobah zai cika wannan alkawarin?

Ibrahim da iyalinsa sun soma yin tafiya zuwa kasar Kan’ana

“Ta wurin bangaskiya ne Ibrahim ya yi biyayya ya kama hanya zuwa wata ƙasa wadda aka yi masa alkawari cewa zai karɓi gādonta. Shi kuwa ya kama hanya ko da bai san inda za shi ba.”​—Ibraniyawa 11:​8, Juyi Mai Fitar da Ma’ana

Tambayoyi: Mene ne Jehobah ya gaya wa Ibrahim ya yi? Wane alkawari ne Jehobah ya yi wa Ibrahim?

Farawa 11:29–12:9; Ayyukan Manzanni 7:​2-4; Galatiyawa 3:6; Ibraniyawa 11:8

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba