Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w16 Fabrairu pp. 3-8
  • Jehobah Ya Kira Shi “Aminina”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ya Kira Shi “Aminina”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • TA YAYA IBRAHIM YA ZAMA ABOKIN ALLAH?
  • YADDA IBRAHIM YA CI GABA DA KYAUTATA DANGANTAKARSA DA ALLAH
  • DANGANTAKA DA KE KAWO ALBARKA
  • Allah Ya Gwada Bangaskiyar Ibrahim
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • An Gwada Bangaskiyarsa
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Ibrahim da Saratu Sun Yi Biyayya ga Allah
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Kana Jiran “Birnin Nan Wanda Yake da Tushe”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
w16 Fabrairu pp. 3-8
Ibrahim da Ishaku suna hawan wani dutse

Jehobah Ya Kira Shi “Aminina”

“Amma kai, Isra’ila bawana, Yaƙub wanda na zaɓa, zuriyar Ibrahim aminina.”—ISHAYA 41:8.

WAƘOƘI: 91, 22

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya sanin Jehobah da kuma abubuwan da ya yi suka ƙarfafa bangaskiyar Ibrahim?

  • Mene ne Ibrahim ya yi don ya ƙarfafa dangantakarsa da Allah?

  • Ta yaya za ka iya yin koyi da Ibrahim wajen ƙulla dangantaka da Jehobah?

1, 2. (a) Ta yaya muka san cewa ‘yan Adam za su iya zama abokan Allah? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

DAGA ranar da aka haife mu har zuwa ranar mutuwarmu, muna bukatar a nuna mana ƙauna. ‘Yan Adam suna bukatar dangantaka ta kud da kud da kuma abokai na ƙwarai, ba irin soyayya da ke tsakanin na miji da ta mace kawai ba. Amma muna bukata ƙauna daga wurin Jehobah. Mutane da yawa ba su gaskata cewa ‘yan Adam za su iya ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah ba domin shi ne Allah Maɗaukakin Sarki kuma ba a ganin sa. Amma mu mun gaskata da hakan!

2 Labaran Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa ‘yan’ Adam za su iya ƙulla dangantaka ta kud da kud da Allah. Ya kamata mu yi koyi da misalinsu. Me ya sa? Domin ƙulla dangantaka da Allah shi ne maƙasudin mafi muhimmanci da ya kamata mu kafa a rayuwarmu. Bari mu yi la’akari da misalin Ibrahim. (Karanta Yaƙub 2:23.) Ta yaya ya zama abokin Allah? Ibrahim ya kasance da bangaskiya sosai kuma hakan ya sa ya ƙulla dangantaka da Allah. Shi ya sa aka san da shi a matsayin “uban masu-bada gaskiya duka.” (Romawa 4:11) Yayin da kake bincika misalinsa, ka tambayi kanka, ‘Ta yaya zan yi koyi da bangaskiyar da Ibrahim ya nuna, kuma ta yaya zan ƙarfafa dangantakata da Jehobah?’

TA YAYA IBRAHIM YA ZAMA ABOKIN ALLAH?

3, 4. (a) Ka kwatanta abin da ya zama gwajin bangaskiya mafi girma da Ibrahim ya taɓa fuskanta. (b) Me ya sa Ibrahim ya kasance a shirye ya yi amfani da Ishaƙu a matsayin hadaya?

3 Ka yi tunanin Ibrahim sa’ad da yake wajen shekara 125 yayin da yake haurawa kan dutse a hankali.[1] (Ka duba ƙarin bayani.) Ɗansa Ishaƙu yana bin sa a baya. Shekararsa ne 25 a lokacin. Ishaƙu yana ɗauke da damin itace, mahaifinsa kuma yana ɗauke da wuƙa da abubuwan da zai yi amfani da su wajen kunna wuta. Mai yiwuwa wannan ita ce tafiya mafi wuya da Ibrahim ya yi a rayuwarsa. Amma ba saboda tsufa ba. Yana da sauran ƙarfinsa. Ya ji nauyin tafiyar ne don Jehobah ya gaya masa ya ba da ɗansa hadaya!​—⁠Farawa 22:​1-8.

4 Mai yiwuwa wannan shi ne gwajin bangaskiya mafi girma da Ibrahim ya taɓa fuskata. Wasu mutane sun ce Allah ya yi mugunta da ya umurci Ibrahim ya ba da ɗansa hadaya a gare shi. Wasu kuma sun ce Ibrahim ya amince ya yi hakan da yardar rai ne don ba ya ƙaunar ɗansa. Mutanen da suke wannan maganar ba su da bangaskiya kuma ba su san abin da ainihin bangaskiya ta ƙunsa ba. Ƙari ga haka, ba su san yadda take tasiri a rayuwar mutum ba. (1 Korintiyawa 2:​14-16) Ba wai Ibrahim ya yi biyayya ga Allah ba tare da yin tunani ba, amma ya yi hakan ne don yana da bangaskiya ta ƙwarai. Ya san cewa Jehobah ba zai gaya masa ya yi abin da zai ɓata rayuwarsa har abada ba. Ibrahim ya san cewa idan ya yi biyayya, Jehobah zai albarkace shi da kuma ɗansa ƙaunatacce. Mene ne Ibrahim yake bukata don ya kasance da irin wannan bangaskiya? Yana bukata ya san Jehobah da kuma shaida abubuwan da ya yi.

5. Ta yaya Ibrahim ya soma sanin Jehobah kuma ta yaya wannan ilimin ya shafe shi?

5 Sanin Jehobah. Ibrahim ya girma a wani birni da ake kira Ur. Mutanen da ke wajen suna bauta wa gumaka, har da mahaifinsa. (Joshua 24:⁠2) Tun da haka ne, ta yaya Ibrahim ya koya game da Jehobah? Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ɗan Nuhu, wato Shem dangin Ibrahim ne kuma ya yi rayuwa har zuwa lokacin da Ibrahim ya kai shekara 150. Shem mutum mai bangaskiya ne sosai kuma wataƙila ya gaya wa danginsa game da Jehobah. Ko da yake ba mu san abin da ya faru ba, amma zai iya yiwu cewa daga Shem ne Ibrahim ya soma sanin Jehobah. Wannan ilimin ya sa Ibrahim ya soma ƙaunar Jehobah kuma ya taimaka masa ya kasance da bangaskiya.

6, 7. Ta yaya abubuwan da Ibrahim ya fuskanta suka ƙarfafa bangaskiyarsa?

6 Shaida abin da Jehobah ya yi. Ta yaya Ibrahim ya shaida abubuwan da suka ƙara ƙarfafa bangaskiyarsa ga Jehobah? Wasu suna cewa tunani ne yake sa mutum ya kasance da ra’ayin yin wani abu, ra’ayin kuma yana sa mutum ya ɗauki mataki. Sanin Jehobah da Ibrahim ya yi, ya motsa zuciyarsa ya girmama “Ubangiji, Allah maɗaukaki, mai-sama da ƙasa.” (Farawa 14:22) Littafi Mai Tsarki ya kira irin wannan ban girma ‘tsoro mai-ibada,’ wato tsoron Allah. (Ibraniyawa 5:⁠7) Muna bukata mu kasance da tsoron Allah idan muna so mu ƙulla dangantaka ta kud da kud da shi. (Zabura 25:14) Wannan halin ne ya motsa Ibrahim ya yi biyayya ga Allah.

7 Allah ya gaya wa Ibrahim da Saratu su bar birnin Ur kuma su tafi ƙasar da ba su taɓa zuwa ba. Su ba ƙananan yara ba ne kuma za su riƙa zama a cikin tanti har ƙarshen rayuwarsu. Ko da yake Ibrahim ya san cewa yin hakan yana tattare da haɗarurruka da dama, ya yi biyayya ga Jehobah. Saboda haka, Jehobah ya albarkace shi kuma ya kāre shi. Alal misali, matarsa Saratu kyakkyawa ce. Sa’ad da aka ƙwace ta daga hannunsa kuma aka kusan kashe shi, Jehobah ya kāre Ibrahim da Saratu ta hanyar mu’ujiza fiye da sau ɗaya. (Farawa 12:​10-20; 20:​2-7, 10-12, 17, 18) Waɗannan abubuwa da suka faru ya ƙarfafa bangaskiyar Ibrahim sosai.

8. Ta yaya sanin Jehobah da kuma shaida abubuwan da ya yi za su ƙarfafa dangantakarmu da shi?

8 Shin za mu iya ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah? Ƙwarai kuwa! Kamar Ibrahim, muna bukata mu koya game da Jehobah. Amma, mu ma za mu sami abubuwan da muke bukata mu sani game da Jehobah da kuma ayyukansa suna cikin Littafi Mai Tsarki. A yau, abubuwan da za su taimaka mana mu san Jehobah a yau, sun fi na Ibrahim. (Daniyel 12:4; Romawa 11:33) Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da dukan abubuwan da muke so mu sani game da “Mai-sama da ƙasa.” Abin da muka koya yana sa mu ƙaunaci Jehobah kuma mu daraja shi sosai. Da yake muna ƙaunar Jehobah da kuma daraja shi, hakan zai motsa mu mu yi masa biyayya. Sa’ad da muka yi hakan, zai kāre mu kuma zai yi mana albarka. Hakan zai sa mu ƙware kuma zai ƙarfafa bangaskiyarmu. Ta hakan, muna shaida taimakonsa. Idan muka bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu, rayuwarmu za ta kasance da gamsuwa da kwanciyar hankali kuma za mu yi farin ciki. (Zabura 34:8; Misalai 10:22) Yayin da muke ƙara koya game da Jehobah kuma muka daɗa ƙware, hakan zai sa mu ƙara kusantar sa.

YADDA IBRAHIM YA CI GABA DA KYAUTATA DANGANTAKARSA DA ALLAH

9, 10. (a) Mene ne zai iya ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin mutane biyu? (b) Mene ne ya nuna cewa Ibrahim ya ɗauki dangantakarsa da Allah da tamani kuma ya kyautata ta?

9 Za a iya ƙwatanta dangantaka ta kud da kud da abu mai tamani, saboda haka, muna bukatar mu ƙarfafa dangantar a “kullayaumi.” (Karanta Misalai 17:17.) Dangantaka ta kud da kud ba kamar tangaran da ake amfani da shi don ado ba ne. Yana kamar fure mai kyau da yake bukatar ban ruwa da kuma kulawa don ya girma. Ibrahim ya ɗauki dangantakarsa da Jehobah da tamani kuma ya ci gaba da kyautata ta. Ta yaya ya yi hakan?

10 Ibrahim ya ci gaba da yin biyayya ga Allah kuma bai daina kasancewa da tsoron Allah ba. Alal misali, a lokacin da ya yi tafiya zuwa ƙasar Kan’ana tare da iyalinsa da kuma bayinsa, ya ci gaba da bin umurnin Jehobah a dukan shawarwarin da ya yi. Shekara ɗaya kafin a haifi Ishaƙu, wato sa’ad da Ibrahim yake shekara 99, Jehobah ya gaya masa cewa ya yi wa dukan mazajen gidansa kaciya. Shin Ibrahim ya yi shakkar Jehobah ne ko kuma ya nemi wani uzuri don ya ƙi bin umurnin da Jehobah ya ba shi? A’a, amma ya dogara ga Jehobah kuma ya yi biyayya ‘a ranar.’​—⁠Farawa 17:​10-14, 23.

11. Me ya sa Ibrahim ya damu game da birnin Saduma da Gwamarata, kuma ta yaya Jehobah ya taimaka masa?

11 Da yake Ibrahim yana yi wa Jehobah biyayya a ko yaushe, har ma a ƙananan abubuwa, hakan ya ƙara ƙarfafa dangantakarsu. Hakan ya sa ya ji kamar zai iya yi wa Jehobah magana a kan kowane abu kuma ya nemi taimakonsa sa’ad da yake fama da tambayoyi da yawa. Alal misali, Ibrahim ya damu sa’ad da Jehobah ya gaya masa cewa zai halaka birnin Saduma da Gwamarata. Me ya sa? Ya ji tsoro cewa za a halaka mugayen mutane tare da mutanen kirki. Wataƙila ya damu da danginsa Lutu da iyalinsa waɗanda suke zama a birnin Saduma. Ibrahim ya dogara ga Jehobah “Mai-shari’an dukan duniya” saboda haka, ya bayyana masa damuwarsa. Jehobah ya bi da amininsa cikin haƙuri kuma ya nuna masa cewa shi mai jin ƙai ne. Jehobah ya bayyana cewa kafin ya yi hukunci, yana biɗan mutanen kirki kuma ya cece su.​—⁠Farawa 18:​22-33.

12, 13. (a) Ta yaya sanin Jehobah da kuma shaida abubuwan da ya yi ya taimaka wa Ibrahim daga baya? (b) Mene ne ya nuna cewa Ibrahim ya ba da gaskiya ga Jehobah?

12 Sanin Jehobah da kuma ganin yadda ya taimaka masa ya sa Ibrahim ya kyautata dangantakarsa da Jehobah. Shi ya sa a lokacin da Jehobah ya gaya masa ya yi hadayar ɗansa, ya san cewa Jehobah mai haƙuri ne, mai jin kai da kuma aminci a kowane lokaci. Ƙari ga haka, yana kāre mutanensa. Ibrahim yana da tabbaci cewa Jehobah bai canja ya zama mugu nan take ba. Me ya sa muka ce haka?

13 Kafin ya bar bayinsa, Ibrahim ya ce: ‘Ku zauna daganan tare da jāki, da ni da saurayin za mu tafi can; mu yi sujada, kāna mu komo wurinku.’ (Farawa 22:⁠5) Mene ne Ibrahim yake nufin da hakan? Sa’ad da ya ce za su dawo tare da Ishaƙu, ya yi ƙarya ne tun da ya san cewa zai yi hadayar sa? A’a. Littafi Mai Tsarki ya ce, Ibrahim ya san cewa Jehobah zai iya ta da Ishaƙu daga mutuwa. (Karanta Ibraniyawa 11:19.) Ibrahim ya san cewa ta ikon Jehobah ne shi da matarsa Saratu suka haifi ɗa duk da cewa sun tsufa. (Ibraniyawa 11:​11, 12, 18) Saboda haka, ya tabbata cewa ba abin da Jehobah ba zai iya yi ba. Ibrahim bai san abin da zai faru a ranar ba. Amma ya kasance da bangaskiya cewa ko da ɗansa ya mutu, Jehobah zai ta da shi domin dukan alkawuran Allah su cika. Shi ya sa ake kiran Ibrahim “uban masu-bada gaskiya duka.”

Ibrahim ya kasance da bangaskiya cewa ko da ɗansa ya mutu, Jehobah zai ta da shi domin dukan alkawuran Allah su cika

14. Wane ƙalubale ne kake fuskanta yayin da kake bauta wa Jehobah, kuma ta yaya misalin Ibrahim zai taimake ka?

14 Ko da yake, Jehobah bai ce mu yi hadayar ‘ya’yanmu a yau ba, amma yana so mu yi masa biyayya. A wani lokaci, ba za mu iya fahimtar dalilin da ya sa Jehobah ya ba da wasu umurni ba. A wani lokaci kuma, bin wasu dokokin da ya bayar yana mana wuya. Shin ka taɓa jin hakan? Ga wasu, yin wa’azi yana yi musu wuya sosai. Wataƙila suna jin kunya da kuma nauyin yin magana da mutanen da ba su saba da su ba. Wasu kuma suna tsoron kasancewa dabam a makarantarsu ko kuma a wuraren aikinsu. (Fitowa 23:2; 1 Tasalonikawa 2:⁠2) Sa’ad da aka gaya maka ka yi wani abu da yake da wuya, ka tuna bangaskiyar Ibrahim da kuma gaba gaɗin da ya kasance da shi. Idan muka yi bimbini a kan misalin waɗannan amintattun mutanen, hakan zai motsa mu mu yi koyi da su kuma mu ƙara kusantar babban Abokinmu, Jehobah.​—⁠Ibraniyawa 12:​1, 2.

Ibrahim da Saratu suna yin hadaya; Ibrahim ya rike wuka yana shirye ya mika Ishaku a matsayin hadaya; Ibrahim yana ja-gorar ibada a iyalinsa

YADDA IBRAHIM YA ƘULLA DANGANTAKA TA KUD DA KUD DA JEHOBAH

SA’AD DA SUKE ZAMA A BIRNIN UR

  • Ibrahim da Saratu sun koyi abubuwa game da Jehobah kuma suka soma bauta masa

  • Ibrahim ya bi umurnin Allah kuma ya bar birnin Ur

SA’AD DA SUKE YIN TAFIYA ZUWA ƘASAR KAN’ANA

  • Jehobah ya kāre Ibrahim da Saratu sa’ad da suke kan tafiya

RAYUWA A ƘASAR KAN’ANA

  • Ibrahim ya bi umurnin Allah kuma ya yi wa dukan mazajen gidansa kaciya

  • Jehobah ya yi haƙuri da Ibrahim sa’ad da ya nuna damuwarsa game da Saduma

  • Jehobah ya sa Ibrahim da Saratu su haifi ɗa

  • Ibrahim ya nuna bangaskiya kuma ya kasance a shirye ya yi hadaya da ɗansa

  • Ibrahim ya mutu da “kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa”

DANGANTAKA DA KE KAWO ALBARKA

15. Me ya sa muke da tabbaci cewa Ibrahim bai yi da na sanin cewa ya yi biyayya ga Jehobah ba?

15 Shin Ibrahim ya yi da-na-sani cewa ya bi umurnin Jehobah ne? Littafi Mai Tsarki ya ce Ibrahim “ya kuwa rasu cikin kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa.” (Farawa 25:​8, Littafi Mai Tsarki) Ko a lokacin da yake shekara 175, Ibrahim zai iya yin tunanin shekaru da yawa da ya yi a duniya kuma ya gamsu da hakan. Me ya sa? Domin ya ɗauki dangantakarsa da Jehobah da muhimmanci sosai. Ko da yake, Littafi Mai Tsarki ya ce Ibrahim “tsoho ne mai shekaru masu yawa,” da ya ji daɗin rayuwa, hakan ba ya nufin cewa ba shi da burin yin rayuwa a nan gaba.

16. Waɗanne abubuwan farin ciki ne Ibrahim zai iya shaidawa a al’janna?

16 Littafi Mai Tsarki ya ce Ibrahim “yana tsumayen birnin da ke da tussa, wanda mai-sifansa da mai-aikinsa Allah ne.” (Ibraniyawa 11:10) Ibrahim yana da tabbaci cewa wata rana zai ga wannan birnin, wato zai yi rayuwa a Mulkin Allah sa’ad da ya soma sarauta a duniya. Hakika, Ibrahim zai gāji Mulkin! Ka yi tunanin farin ciki da Ibrahim zai yi sa’ad da duniya ta zama aljanna kuma hakan zai sa ya ci gaba da ƙarfafa dangantakarsa da Jehobah. Zai yi farin cikin sanin cewa misalin bangaskiya da ya kafa ya taimaka wa mutanen Allah shekaru dubbai da suka biyo baya. A aljanna, zai gane cewa yadda Jehobah ya mai da masa Ishaƙu yana wakiltar wani abu mai muhimmanci sosai. (Ibraniyawa 11:19) Ƙari ga haka, zai koyi cewa yadda ya ji sa’ad da yake shirin yin hadayar ɗansa Ishaƙu ya taimaka wa miliyoyin amintattun mutane su fahimci yadda Jehobah ya ji sa’ad da yake ba da Ɗansa Yesu Kristi a matsayin hadaya ga ‘yan Adam. (Yohanna 3:16) Misalin da Ibrahim ya kafa ya taimaka mana mu nuna godiyarmu ga hadayar fansa. Babu wanda ya taɓa nuna irin wannan ƙaunar!

17. Mene ne ka ƙudura anniyar yi kuma me za mu tattauna a talifi na gaba?

17 Bari dukan mu mu ƙudura anniyar yin koyi da bangaskiyar Ibrahim. Kamar Ibrahim, muna bukatar mu san Jehobah da kuma shaida abubuwan da ya yi a madadinmu. Yayin da muka ci gaba da koyo game da Jehobah da kuma yi masa biyayya, za mu ga yadda za mu shaida albarkarsa da kuma kāriyarsa. (Karanta Ibraniyawa 6:​10-12.) Bari mu ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah har abada! A talifi na gaba, za mu tattauna wasu misalai na amintattun mutane guda uku da suka ƙulla dangantaka ta kud da kud da Allah.

^ [1] (sakin layi na 3) A dā, ana kiran Ibrahim da Saratu Abram da Saraya. Amma a wannan talifin, za mu yi amfani da sunayen da Jehobah ya ba su daga baya.

Ba wai Ibrahim ya yi biyayya ga Allah ba tare da yin tunani ba

Abota tana kamar fure mai kyau da take bukatar ban ruwa da kuma kulawa don ya girma

MA’ANAR WASU KALMOMI

  • Idan muna so mu zama abokin Allah, muna bukatar mu san shi sosai. Yayin da muke koya game da shi, za mu soma ƙaunar sa kuma mu daraja shi. Hakan zai motsa mu mu dogara a gare shi kuma mu yi masa biyayya. Idan muka ci gaba da ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah, abotarmu da shi za ta dawwama

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba