Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 21 p. 54-p. 55 par. 1
  • Annoba ta Goma

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Annoba ta Goma
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Musa Da Haruna Sun Je Wurin Fir’auna
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Annoba ta Daya Zuwa Uku
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Allah Ya Ceci ’Ya’yan Isra’ila
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • Mugun Sarki Yana Sarauta A Masar
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 21 p. 54-p. 55 par. 1
Wani dan Isra’ila yana yafa jini a bakin kofar gidansa

DARASI NA 21

Annoba ta Goma

Musa ya yi wa Fir’auna alkawari cewa ba zai sake zuwa wurinsa ba. Amma kafin ya tafi, ya gaya masa cewa: ‘Kowane ɗan fari na ʼyan Masar zai mutu da daren nan har da ɗan Fir’auna ma.’

Sai Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa su dafa wani irin abinci. Ya ce: ‘Ku yanka bunsuru ko rago mai shekara ɗaya kuma ku yafa jininsa a ƙofarku. Ku gasa naman kuma ku ci da burodin da ba a saka masa yisti ba. Ku saka riga da kuma takalmi kuma ku kasance da shiri don za ku tafi da daren nan.’ Babu shakka, Isra’ilawa sun yi murna sosai, ko ba haka ba?

Mala’ikan Jehobah ya shiga duka gidajen Masarawa da tsakar dare. Duk gidan da ba su yafa jini a ƙofarsu ba, ɗan farinsu ya rasu. Amma mala’ikan bai shiga gidajen da aka yafa jini a ƙofarsu ba. ʼYan farin Masarawa masu arziki da talakawa duk sun mutu. Amma babu ko ɗaya cikin ’ya’yan Isra’ilawa da ya mutu.

Yaron Fir’auna ma ya mutu. Nan da nan, sai Fir’auna ya gaya wa Musa da Haruna cewa: ‘Ku tashi, ku fita daga ƙasar nan. Ku tafi ku bauta wa Allahnku. Ku tafi da dukan dabbobinku!’

An shirya Isra’ilawa bisa iyali da ƙabila kuma sun fita daga ƙasar Masar ana farin wata. Akwai Isra’ilawa maza 600,000 da mata da kuma yara da yawa. Har ila, mutane da yawa da ba Isra’ilawa ba sun bi su don su bauta wa Jehobah. Yanzu, Isra’ilawa sun samu ’yanci!

A kowace shekara, Isra’ilawa suna yin biki don su riƙa tunawa da yadda Jehobah ya cece su. Ana kiran wannan bikin Idin Ƙetarewa.

Isra’ilawa sun fita daga kasar Masar

“Na tashe ka ka zama sarki da nufi cewa in nuna ikona ta wurinka, a kuma sanar da sunana cikin duniya duka.”​—Romawa 9:​17, Juyi Mai Fitar da Ma’ana

Tambayoyi: Wace annoba ce ta goma? Mene ne Isra’ilawa suka yi don su kāre kansu daga wannan annobar?

Fitowa 11:1–12:42; 13:​3-10

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba