Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 36 p. 88-p. 89 par. 1
  • Alkawarin da Jephthah Ya Yi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Alkawarin da Jephthah Ya Yi
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Alkawarin Jephthah
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ta Sa Babanta da Jehobah Farin Ciki
    Ku Koyar da Yaranku
  • Allah da Kuma Abokanta Sun Ƙaunace Ta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Allah Yana Albarkar Wadanda Suka Kasance da Aminci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 36 p. 88-p. 89 par. 1
Jephthah ya yayyaga rigarsa sa’ad da ya ga ʼyarsa ta fito ta marabce shi

DARASI NA 36

Alkawarin da Jephthah Ya Yi

Isra’ilawa sun sake barin Jehobah kuma suka soma bauta wa allolin ƙarya. Waɗannan allolin ƙaryan ba su taimaki Isra’ilawa ba a lokacin da Ammoniyawa suka yaƙe su. Isra’ilawan sun yi shekaru da yawa suna shan wahala. Daga baya, sai suka ce wa Jehobah: ‘Mun yi zunubi. Muna roƙonka ka ceci mu daga abokan gabanmu.’ Sai Isra’ilawan suka halaka dukan gumakansu kuma suka dawo suna bauta wa Jehobah. Jehobah bai yi farin ciki don wahalar da suke sha ba.

Sai Jehobah ya zaɓi Jephthah ya ja-goranci Isra’ilawa don su yaƙi Ammoniyawa. Ya ce wa Jehobah: ‘Idan ka taimake mu muka ci yaƙin nan, na yi maka alkawari cewa idan na koma gida, zan ba ka duk mutumin da ya fara fitowa daga gidana don ya yi mini maraba.’ Jehobah ya amsa addu’ar Jephthah kuma ya ci yaƙin.

Sa’ad da Jephthah ya dawo gida, sai ’ya guda ɗaya kawai da yake da ita ta fito don ta yi masa maraba. Ta fito tana kiɗi kuma tana rawa. To me Jephthah zai yi? Ya tuna da alkawarinsa kuma ya ce: ‘Kash ’yata! Kin sa ni baƙin ciki. Na yi wa Jehobah alkawari kuma don in cika alkawarin, za ki je ki yi hidima a mazauninsa a Shiloh.’ Sai ta ce masa: ‘Baba, tun da ka riga ka yi wa Jehobah alkawari, dole ka cika alkawarin. Abin da nake so shi ne ka ba ni wata biyu in ɗan kasance tare da ƙawayena a kan dutse. Bayan haka, zan tafi.’ ’Yar Jephthah ta yi hidima a mazauni har ƙarshen rayuwarta. Abokanta sukan kai mata ziyara kowace shekara a Shiloh.

Kawayen ʼyar Jephthah sun ziyarce ta a mazauni

“Duk wanda ya fi son mamarsa ko babansa fiye da ni, bai isa ya zama nawa ba.”​—Matta 10:​37, Juyi Mai Fitar da Ma’ana

Tambayoyi: Wane alkawari ne Jephthah ya yi? Yaya ’yar Jephthah ta ji don alkawarin da babanta ya yi?

Alƙalawa 10:6–11:11; 11:​29-40; 1 Sama’ila 12:​10, 11

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba