Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 4/1 pp. 11-12
  • Allah da Kuma Abokanta Sun Ƙaunace Ta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Allah da Kuma Abokanta Sun Ƙaunace Ta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Ta Sa Babanta da Jehobah Farin Ciki
    Ku Koyar da Yaranku
  • Alkawarin Jephthah
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Allah Yana Albarkar Wadanda Suka Kasance da Aminci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Alkawarin da Jephthah Ya Yi
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 4/1 pp. 11-12

Ku Koyar Da Yaranku

Allah da Kuma Abokanta Sun Ƙaunace Ta

BABU wanda ya san sunanta a yau. An san ta ne kawai da sunan mahaifinta, Jephthah. Bari mu bincika Littafi Mai Tsarki don mu koya game da mutanen nan biyu. Za mu ga cewa Allah da kuma ƙawayen ɗiyar Jephthah suna ƙaunarta sosai.

Za mu iya karanta labarin Jephthah da ɗiyarsa a cikin Littafi Mai Tsarki a Alƙalawa sura ta 11. Tun da Jephthah bawan Allah ne mai aminci, babu shakka yana tattauna Nassosi a kai a kai da ɗiyarsa.

Jephthah ya rayu ne kafin mutanen Allah, Isra’ilawa, suka ce suna son sarki ɗan Adam ya sarauce su. Jephthah mutumi ne mai ƙarfi wanda ya ƙware wajen yin yaƙi. Saboda haka, Isra’ilawa suka roƙe shi ya ja-gorance su su yaƙi Ammoniyawa, wata ƙasa maƙwabciyarsu da ta daɗe tana yaƙi da Isra’ilawa.

Jephthah yana son Allah ya taimake shi don ya yi nasara bisa Ammoniyawa, saboda haka, ya yi wani alkawari. Jephthah ya ce idan Jehobah ya ba shi nasara, zai ba Jehobah duk wanda ya fara fitowa daga gidansa ya tarbe shi sa’ad da ya dawo gida. Har mutumin ya ko ta mutu zai ko za ta ci gaba da yin bauta a mazaunin Allah, inda mutanen suke bauta wa Allah a zamanin. Ka san mutumin da ya fara fitowa?—a

Hakika, ɗiyar Jehpthah ce! Jephthah ya yi baƙin ciki sosai. Ɗiyarsa ke nan tilo. Amma ya riga ya yi alkawari ga Jehobah kuma dole ne ya cika shi. Nan da nan, ɗiyarsa ta ce: “Ubana, kā buɗe bakinka ga Ubangiji; sai ka yi mani bisa ga abin da ya fito daga cikin bakinka.” Sai ta ce a ƙyale ta ta tafi kan duwatsu har tsawon watanni biyu domin ta yi makoki. Me ya jawo baƙin cikin? Domin idan ta cika wa’adin mahaifinta, ba za ta iya yin aure kuma ta haihu ba. Duk da haka, ba ta ɗauki sha’awoyinta a matsayin abin da ya fi muhimmanci ba. Tana son ta yi biyayya ga mahaifinta kuma ta nuna aminci ga Jehobah. Kana tunanin cewa Jehobah da mahaifinta sun yi farin ciki?—

Saboda haka, Jephthah ya ƙyale ɗiyarsa tare da abokanta su yi tafiya har tsawon watanni biyu. Sa’ad da ta dawo, mahaifinta ya cika wa’adin da ya yi ta wajen tura ta mazaunin Allah a Shiloh ta ci gaba da hidima a can har tsawon rayuwarta. A kowace shekara, ’yan matan Isra’ila suna zuwa Shiloh kuma su ƙarfafa ɗiyar Jephthah.

Ka san ƙananan yaran da suke biyayya ga iyayensu kuma suna ƙaunar Jehobah?—Yana da kyau ka san yaran sosai kuma ka zama abokinsu. Idan ka yi koyi da ɗiyar Jephthah kuma ka nuna biyayya da aminci, za ka samu abokan kirki. Za ka faranta ran iyayenka, kuma Jehobah zai ƙaunace ka.

Ka karanta

Kubawar Shari’a 6:4-6

Alƙalawa 11:30-40

1 Korintiyawa 7:37, 38

a cikin naka Littafi Mai Tsarki

[Hasiya]

a Idan kana karatun ne da yaro, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata ka ƙarfafa shi ya faɗi ra’ayinsa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba