Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 48 p. 116-p. 117 par. 1
  • Yaron Wata Gwauruwa Ya Tashi Daga Mutuwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yaron Wata Gwauruwa Ya Tashi Daga Mutuwa
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • An Sāka wa Gwauruwar Zarefat don Bangaskiyarta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Allahnsa Ya Ƙarfafa Shi
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Sami Ƙarfafawa Daga Wajen Allahnsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Taba Jin Kadaici da Tsoro?
    Ku Koyar da Yaranku
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 48 p. 116-p. 117 par. 1
Iliya ya kira wata gwauruwa da take tattara itace

DARASI NA 48

Yaron Wata Gwauruwa Ya Tashi Daga Mutuwa

Tukunyar fulawa da kuma māi

Sa’ad da ba a yi ruwan sama a ƙasar ba, Jehobah ya ce wa Iliya: ‘Ka je Zarefat. Akwai wata mata a wurin da za ta ba ka abinci.’ Iliya ya ga wata mata a bakin ƙofar birnin tana tattara itace. Sai ya ce ta ba shi ruwa ya sha. Da ta je kawo masa ruwa, sai Iliya ya ƙara ce mata: ‘Don Allah ki kawo mini gurasa.’ Amma gwauruwar ta ce: ‘Ba ni da wata gurasa da zan iya ba ka. Fulawa da māi da zai ishe ni da kuma ɗana ne kawai nake da shi.’ Sai Iliya ya ce mata: ‘Jehobah ya yi alkawari cewa idan kika yi mini gurasa, fulawarki da mānki ba za su ƙare ba har sai an soma ruwan sama.’

Sai gwauruwar ta je gida kuma ta yi wa annabin Jehobah gurasa. Kamar yadda Jehobah ya yi alkawari, wannan gwauruwar da ɗanta ba su rasa abinci ba a lokacin da ba a yi ruwan sama ba. Fulawarta da mānta ba su ƙare ba.

Amma wani mummunan abu ya faru. Yaron gwauruwar ya yi rashin lafiya kuma ya mutu. Sai ta roƙi Iliya ya taimaka mata. Iliya ya karɓi yaron daga hannunta kuma ya kai shi wani ɗaki a saman gidanta. Ya ajiye shi a kan gado kuma ya yi addu’a: ‘Ya Jehobah, ina roƙonka ka tayar da yaron nan daga mutuwa.’ Ka san dalilin da ya sa tayar da wannan yaron zai zama abu na musamman? Domin a lokacin, babu wanda aka taɓa tayar daga mutuwa. Kuma wannan gwauruwar da yaronta ba Isra’ilawa ba ne.

Jehobah ya tayar da yaron daga mutuwa! Sai Iliya ya ce wa gwauruwar: ‘Ki ga, ɗanki yana da rai.’ Ta yi farin ciki sosai kuma ta ce wa Iliya: ‘Babu shakka, kai mutumin Allah ne. Na san da hakan domin abin da Jehobah ya gaya maka kawai kake faɗa.’

Iliya ya kawo wa gwauruwar danta

“Ku dubi dai hankaki! Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba su da taska ko rumbu, amma kuwa Allah yana cishe su. Sau nawa martabarku ta ninka ta tsuntsaye!”​—Luka 12:​24, Littafi Mai Tsarki

Tambayoyi: Ta yaya gwauruwar da ke birnin Zarefat ta nuna cewa ta dogara ga Jehobah? Ta yaya muka san cewa Iliya annabin Allah ne da gaske?

1 Sarakuna 17:​8-24; Luka 4:​25, 26

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba