Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 2/15 pp. 13-15
  • An Sāka wa Gwauruwar Zarefat don Bangaskiyarta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • An Sāka wa Gwauruwar Zarefat don Bangaskiyarta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ILIYA YA GA GWAURUWA MAI BANGASKIYA
  • “KI FARA YI MANI ƊAN WAINA TUKUNA”
  • ‘KO KA ZO WURINA DOMIN KA KASHE ƊANA?’
  • “GA ƊANKI, YANA DA RAI”
  • Yaron Wata Gwauruwa Ya Tashi Daga Mutuwa
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Allahnsa Ya Ƙarfafa Shi
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Sami Ƙarfafawa Daga Wajen Allahnsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Yadda Za Mu Kasance da Ra’ayi Mai Kyau
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 2/15 pp. 13-15

An Sāka wa Gwauruwar Zarefat don Bangaskiyarta

WATA gwauruwa talaka ta rungumi ɗanta tilo. Abin ya ba ta mamaki. Ɗazun tana ɗauke da gawan ɗanta. Amma, yanzu matan ta kalli ɗanta da aka tayar daga mutuwa kuma ta yi murna cewa yaron yana da rai kuma yana mata murmushi. Baƙon da ya sauka a gidanta ya ce mata, “Ga ɗanki, yana da rai.”

Wannan tashi daga mutuwa ya auku ne shekaru 3,000 da suke shige. Za ka iya karanta labarin a littafin 1 Sarakuna sura ta 17. Sunan baƙon Iliya ne. Mahaifiyar yaron fa? Wata gwauruwa ce da ba a ambata sunanta ba. Tana zama a garin Zarefat. Tayar da ɗanta daga mutuwa da aka yi abu ne da ya ƙarfafa bangaskiyar sosai. Bari mu tattauna wasu abubuwan da suka faru a rayuwarta domin mu koyi wasu darussa masu kyau.

ILIYA YA GA GWAURUWA MAI BANGASKIYA

Jehobah ya ƙudura cewa za a jima ana yin fari a Isra’ila a zamanin mugun Sarki Ahab. Bayan da Iliya ya sanar da wannan saƙon, Allah ya ɓoye shi don kada Ahab ya gan shi kuma ya ciyar da shi ta wata hanya mai ban al’ajabi. Ya aika tsuntsaye su riƙa kai masa nama da gurasa don ya ci. Sai Jehobah ya ce wa Iliya: “Ka tashi, ka tafi Zarefat, ta Zidon, ka zauna can: ga shi, na umurci wata gwauruwa can ta yi kiwonka.”—1 Sar. 17:1-9.

Sa’ad da Iliya ya isa Zarefat, sai ya ga wata gwauruwa tana tara ice. Shin wannan matar ita ce wadda za ta ciyar da annabin? Ta yaya za ta ciyar da shi da yake ita matalauciya ce? Ko da Iliya ya yi shakka, hakan bai hana shi soma tattaunawa da matar ba. Ya ce mata: “Ina roƙonki, ki ɗauko mani ɗan ruwa a cikin gora, domin in sha.” Sa’ad da take ƙoƙarin kawo masa ruwa, sai ya ƙara da cewa: “Ina roƙonki ki kawo mani ɗan abinci.” (1 Sar. 17:10, 11) Ba wa wannan baƙon ruwa ba matsala ba ce, amma ba shi abinci abu mai wuya ne a gare ta.

Matar ta ce: “Ta ce, Na rantse da Ubangiji, Allahnka mai-rai, ba ni da ko ɗan gutsure, sai dai tāfin gāri cikin tukunya, da mai kaɗan a cikin kurtu: ga shi kuwa, ina tara yan ice, domin in shiga in shirya domin ni da ɗana, mu ci, mu mutu.” (1 Sar. 17:12) Mene ne za mu koya daga wannan tattaunawar?

Gwauruwar ta gane cewa Iliya bawan Allah ne. Mun gane hakan daga furucinta sa’ad da ta ce: “Na rantse da Ubangiji, Allahnka mai-rai.” Kamar dai tana da masaniya game da Allah na Isra’ila, amma ita ba mai bauta masa ba ne. Tana zama ne a Zarefat, wani gari da ke ƙarƙashin birnin Zidon. Da alama cewa mazauna Zarefat masu bauta wa Baal ne. Duk da haka, akwai abin kirki da Jehobah ya gani a zuciyar wannan gwauruwar.

Ko da yake gwauruwar ta yi zama a tsakanin masu bauta wa gumaka, ta kasance da bangaskiya. Za mu iya koyon darasi daga misalinta.

Ba dukan mazaunan Zarefat da suke bauta wa Baal ba ne suka gama ɓacewa. Jehobah ya aika Iliya zuwa wurin wannan gwauruwar kuma hakan ya nuna cewa Jehobah yana lura da mutane masu zuciyar kirki da ba su soma bauta masa ba. Hakika, “a cikin kowace al’umma, wanda yake tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gare shi.”—A. M. 10:35.

Mutane nawa ne a yankinku suke kamar wannan gwauruwar Zarefat? Ko da yake suna zama ne tsakanin masu bin addinin ƙarya, wataƙila suna neman abin da zai sa su kyautata ibadarsu. Wataƙila suna ji game da Jehobah, amma ba su san shi sosai ba. Idan an taimaka musu, za su soma bauta ta gaskiya. Shin kana nema da kuma taimakon irin waɗannan mutanen?

“KI FARA YI MANI ƊAN WAINA TUKUNA”

Ka yi la’akari sosai da abin da Iliya ya gaya wa gwauruwar ta yi. Ta riga ta gaya masa cewa bayan ta dafa abincin da ya rage kuma ta ci tare da ɗanta, sai su mutu. Duk da haka, mene ne Iliya ya ce? “Kada ki ji tsoro; je ki, ki yi abin da kin faɗi; amma ki fara yi mani ɗan waina tukuna, ki kawo mani ita, daga baya ki yi wa kanki da ɗanki. Gama haka nan Ubangiji ya faɗi, Allah na Isra’ila, Tukunyar gāri ba za ta sare ba, kurtun mai kuma ba za ya sare ba, har ran da Ubangiji ya aiko da ruwa bisa ƙasa.”—1 Sar. 17:11-14.

Ka yi tunanin abin wasu za su ce: In ba ka abincina na ƙarshe? Ai hakan ba zai yiwu ba. Amma gwauruwar ba ta ji haka ba. Duk da cewa ba ta san Jehobah sosai ba, ta gaskata da abin da Iliya ya ce kuma ta bi umurninsa. Hakika wannan abin da ya faru ya gwada bangaskiyarta sosai, kuma ta yanke shawarar da ta nuna cewa tana da basira!

Allah bai yi watsi da wannan gwauruwar ba. Jehobah ya ci gaba da tanadar mata da abinci har ita da Iliya da kuma ɗanta sun sami abinci muddar farin. Hakika, “tukunyar hatsi ba ta shace ba, tulun mai kuma ba ya sare ba, bisa ga maganar Ubangiji da ya faɗi ta bakin Iliya.” (1 Sar. 17:16; 18:1) Da a ce matar bata ji maganar Iliya ba, da gurasar da ta yi da ɗan hatsin ya zama abincinta na ƙarshe. A maimakon haka, ta kasance da bangaskiya kuma ta dogara da Jehobah, ta ba wa Iliya abinci ya ci tukuna.

Wani darasi da za mu koya a nan shi ne Allah yana saka wa waɗanda suka gaskata da shi. Sa’ad da ka fuskanci gwaji kuma ka kasance da bangaskiya, Jehobah zai taimake ka. Zai tanadar maka da bukatunka kuma zai kāre ka. Ƙari ga haka, zai zama Amininka don ya taimake ka ka jure wa gwaji.—Fit. 3:13-15.

A shekara ta 1898, wani talifi a Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta koyar da wannan darasi: “Tun da matar ta kasance da bangaskiya har ta bi umurnin Iliya, hakan ya nuna cewa ta cancanci taimakon Jehobah ta hannun annabin; da ba ta gaskata da abin da annabin ya faɗa ba, da wata gwauruwa dabam za ta yi hakan. Hakan ma yake a yau. A wasu lokuta, Jehobah yakan bari a gwada bangaskiyarmu. Idan muka kasance da bangaskiya, za mu sami lada amma idan ba mu yi hakan ba, ba za mu sami ladar ba.”

Sa’ad da muna fuskantar wani gwaji na musamman, ya kamata mu nemi ja-gorar da Jehobah yake tanadarwa a cikin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu. Bayan haka, sai mu bi shawarar Jehobah ko da yin hakan yana da wuya. Jehobah zai albarkace mu sosai idan muka bi wannan shawarar mai hikima: “Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka, kada ka jingina ga naka fahimi: A cikin dukan al’amuranka ka shaida shi, shi kuma za ya daidaita hanyoyinka.”—Mis. 3:5, 6.

‘KO KA ZO WURINA DOMIN KA KASHE ƊANA?’

Wata aukuwa za ta sake gwada bangaskiyar gwauruwar. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Bayan wannan, sai ɗan macen, uwargida, ya yi ciwo; cutarsa kuwa ta yi zafi, har ba a rage lumfashi a cikinsa ba.” Matar ta soma tunanin dalilin da ya sa hakan ya faru, cike da baƙin ciki, sai ta ce wa Iliya: “Ina ruwana da kai, ya kai mutumin Allah? ko ka zo wurina domin ka tone mani zunubina, ka kashe ɗana kuma?” (1 Sar. 17:17, 18) Mene ne waɗannan kalaman suke nufi?

Shin matar ta tuna da wani zunubin da ta yi a dā da yake damunta ne? Shin ta yi tunanin cewa Allah ne ya kashe ɗanta kuma annabi Iliya ne Allah ya aiko ya yi hakan? Littafi Mai Tsarki bai ce haka ba, amma mun san cewa gwauruwar ba ta ce Allah ya yi mata rashin adalci ba.

Babu shakka, Iliya ya yi mamaki cewa ɗan gwauruwar ya mutu kuma ta yi tunani cewa shi ne ya jawo mutuwar. Sa’ad da Iliya ya ɗauki gawan yaron zuwa ɗakin da ke saman bene, sai ya soma roƙon Allah, yana cewa: “Ya Ubangiji Allahna, ko ka jawo masifa bisa gwauruwar nan kuma, wadda ni ke zaune a wurinta, ka kashe ɗanta?” Wannan abin ya dami Iliya don yana ganin cewa mutuwar yaron za ta ɓata sunan Allah don matar tana da kirki kuma ta karɓe shi da hannu bibbiyu. Saboda haka, Iliya ya roƙi Allah, yana cewa: “Ya Ubangiji Allahna, ina roƙonka, ka bar ran yaron nan ya sāke shiga cikinsa.”—1 Sar. 17:20, 21.

“GA ƊANKI, YANA DA RAI”

Jehobah ya ji addu’ar Iliya. Gwauruwar ta biya bukatar annabinsa kuma ta nuna bangaskiya. Kamar dai Allah ya ƙyale cutar ta yi sanadin mutuwar yaron don ya san cewa zai ta da yaron daga mutuwa. Wannan tashin matattu shi ne na farko da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki kuma ya sa miliyoyin mutane da suka rayu daga baya sun kasance da bege. Sa’ad da Iliya ya yi addu’a, sai Jehobah ya ta da yaron. Ka yi tunanin irin murna da gwauruwar ta yi sa’ad da Iliya ya ce mata: “Ga ɗanki, yana da rai.” Daga baya sai ta gaya wa Iliya cewa: “Yanzu na sani kai mutumin Allah ne; maganar Ubangiji kuwa a bakinka gaskiya ne.”—1 Sar. 17:22-24.

Ba a ƙara ambata wani abu game da wannan matar a littafin 1 Sarakuna sura 17 ba. Amma da yake Yesu ya yabe ta, wataƙila ta ci gaba da bauta wa Jehobah. (Luk 4:25, 26) Labarin wannan gwauruwar ya koya mana cewa Allah yana saka wa waɗanda suke yi wa bayinsa alheri. (Mat. 25:34-40) Ya nuna cewa Jehobah yana biya wa amintattunsa bukatu, ko da a mawuyacin yanayi ma. (Mat. 6:25-34) Ƙari ga haka, labarin ya nuna cewa Jehobah yana da iko kuma yana marmarin ta da waɗanda suka mutu. (A. M. 24:15) Babu shakka, waɗannan dalilai ne masu kyau na tuna da gwauruwar Zarefat.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba