Yadda Za Mu Kasance da Ra’ayi Mai Kyau
“Ko da mutum za ya yi shekaru da yawa, bari shi ji daɗinsu duka.”—M. WA. 11:8.
1. Waɗanne abubuwa ne Jehobah yake tanadar mana da ke sa mu farin ciki?
JEHOBAH yana so mu yi farin ciki kuma yana mana albarka don mu yi hakan. Shi ya halicce mu, saboda haka, za mu iya yin amfani da rayuwarmu don bauta masa, domin shi ne yake jawo mu ga bauta ta gaskiya. (Zab. 144:15; Yoh. 6:44) Jehobah yana ƙaunarmu sosai kuma yana taimaka mana mu ci gaba da bauta masa. (Irm. 31:3; 2 Kor. 4:16) Muna jin daɗin kwanciyar hankali da haɗin kai da ’yan’uwa masu ƙauna da tunasarwa a kai a kai kuma hakan yana nuna cewa Jehobah yana ƙaunarmu. Ƙari ga hakan, muna da begen yin rayuwa har abada.
2. Mene ne wasu bayin Jehobah suke fama da shi?
2 Duk da dukan waɗannan albarkar da Jehobah ya yi mana, wasu bayin Jehobah suna baƙin ciki. Suna iya ji cewa Jehobah ba ya daraja su da kuma hidimarsu. Mutanen da suke da irin wannan ra’ayin za su iya ji cewa more “shekaru da yawa” wasiƙar jaki ce. Sun ji cewa babu wani batun jin daɗi a rayuwa.—M. Wa. 11:8.
3. Mene ne zai iya sa mu baƙin ciki?
3 Rashin lafiya ko taƙaici ko kuma tsufa zai iya sa wasu ’yan’uwa baƙin ciki. (Zab. 71:9; Mis. 13:12; M. Wa. 7:7) Bugu da ƙari, dole ne kowane Kirista ya fahimci cewa zuciya tana da rikici kuma tana iya sa mu ji cewa ba ma faranta wa Jehobah rai ko da muna yin abu mai kyau. (Irm. 17:9; 1 Yoh. 3:20) Shaiɗan yana yaɗa ƙarya game da bayin Allah kuma waɗanda suke koyi da Shaiɗan za su iya sa mu kasance da irin ra’ayin Eliphaz marar bangaskiya wanda ya ce ba mu da daraja a gaban Jehobah. Hakan ƙarya ce a zamanin Ayuba da kuma a yau.—Ayu. 4:18, 19.
4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
4 Jehobah ya bayyana a cikin Kalmarsa dalla-dalla cewa zai kasance tare da waɗanda suke fama da baƙin ciki. (Zab. 23:4) Wata hanya da yake kasance tare da mu ita ce ta Kalmarsa. Littafi Mai Tsarki yana da iko daga ‘Allah don rushe makamai masu ƙarfi.’ Hakan yana nufin cewa zai iya canja ra’ayi marar kyau da muke da shi game da kanmu. (2 Kor. 10:4, 5, Littafi Mai Tsarki) Yanzu, bari mu tattauna yadda Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu kasance da ra’ayi mai kyau. Za ka iya amfana daga hakan kuma zai iya sa ka ƙarfafa wasu.
KA YI AMFANI DA KALMAR ALLAH DON KASANCE DA RA’AYI MAI KYAU
5. Mene ne zai iya taimaka mana mu kasance da ra’ayi mai kyau?
5 Manzo Bulus ya kwatanta wasu abubuwa da za su iya taimaka mana mu kasance da ra’ayi mai kyau. Ya aririce ’yan’uwa da ke ikilisiyar Korinti cewa: “Ku gwada kanku ko kuna cikin imani.” (2 Kor. 3:5) “Imani” da aka ambata a wannan ayar tana nufin koyarwa Littafi Mai Tsarki. Ba za mu iya cewa za mu bi wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki ba kuma mu yi watsi da wasu ba.—Yaƙ. 2:10, 11.
6. Me ya sa ya kamata mu gwada kanmu ko muna cikin imani? (Ka duba hoton da ke shafi na 12.)
6 Za ka iya yin jinkirin gwada kanka, musamman ma idan kana ji cewa za ka kasa. Amma, yadda Jehobah yake ɗaukanmu ya fi yadda muke ɗaukan kanmu domin ya fi mu hikima. (Isha. 55:8, 9) Yana binciken mu ba domin ya yi mana sūka ba, amma don ya ga halayenmu masu kyau kuma ya taimaka mana. Idan ka yi amfani da Kalmar Allah domin ka gwada kanka “ko kana cikin imani,” za ka san yadda Jehobah yake ji game da kai. Hakan zai sa ka san cewa kana da daraja sosai a gaban Jehobah kuma zai haskaka rayuwarka.
7. Ta yaya za mu amfana daga misalan amintattun mutane da aka ambata Littafi Mai Tsarki?
7 Hanya mafi kyau na yin wannan gwajin ita ce ta wajen yin bimbini a kan misalan amintattu da aka ambata a Littafi Mai Tsarki. Ka gwada yanayinka da nasu, kuma ka ga yadda za ka aikata da a ce kai ne ka sami kanka a yanayinsu. Bari mu yi la’akari da misalai uku da suka nuna yadda za ka iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki don gwada ko kana “cikin imani,” kuma ta yin hakan, za ka kasance da ra’ayin mai kyau.
GWAURUWA MATALAUCIYA
8, 9. (a) Wane irin yanayi ne gwauruwar take ciki? (b) Mene ne wataƙila ya sa gwauruwar baƙin ciki?
8 Yesu ya lura da wata gwauruwa matalauciya a haikalin da ke Urushalima. Misalinta zai iya taimaka mana mu kasance da ra’ayi mai kyau duk da kasawarmu. (Karanta Luka 21:1-4.) Ka yi la’akari da yanayinta. Na farko, maigidanta ya rasu kuma limamai a lokacin suna hadama kuma suna damfarar gwauraye, maimakon su taimaka musu. (Luk 20:47) Saboda tsabar talaucinta, ta ba da gudummawar kuɗin da leburori za su samu a cikin mintoci 15.
9 Ka yi tunanin yadda gwauruwar ta ji yayin da ta shiga cikin haikalin riƙe da anini biyu. Wataƙila ta yi baƙin ciki domin da a ce maigidanta na da rai, da ta ba da gudummawar da ta fi hakan. Ko kuwa ƙila ta ji kunya domin gudummawar da wasu suke bayarwa ya fi nata. Ko da ta ji hakan, amma ta ba da gudummawa don tallafa wa bauta ta gaskiya.
10. Ta yaya Yesu ya nuna cewa Allah ya daraja gwauruwar?
10 Yesu ya ce Jehobah ya daraja gwauruwar da kuma gudummawarta. Ya ce abin da gwauruwar “ta zuba ciki ya fi nasu [mawadatan] duka.” Ko da yake za a haɗa kyautarta da na wasu mutane, amma Yesu ya yaba mata. Waɗanda za su ƙirga kuɗin da aka saka cikin asusun ba za su san yadda Jehobah ya daraja wannan anini biyun da kuma gwauruwar ba. Amma duk da haka, yadda Jehobah ya ɗauke ta ne ya fi muhimmanci, ba yadda wasu suke ɗaukan ta ba ko kuma yadda ta ɗauki kanta. Zai dace ka yi amfani da wannan labarin don ka gwada ko kana cikin gaskiya.
11. Wane darasi ne za ka iya koya daga labarin gwauruwar?
11 Yanayinka zai iya shafan abin da za ka ba Jehobah. Saboda tsufa ko kuma ciwo, wasu mutane ba za su iya yin wa’azi na sa’o’i da yawa ba. Shin ya kamata su raina ɗan sa’o’in da suke bayarwa? Ko da kai matashi ne ko kuma kana da koshin lafiya, za ka iya ji cewa sa’o’in da kake yi kana wa’azi ƙalilan ne idan an haɗa su da waɗanda sauran bayin Jehobah a faɗin duniya suke bayarwa kowace shekara. Labarin gwauruwar ya koya mana cewa Jehobah yana daraja ƙoƙarin da muke yi a hidimarsa, musamman ma idan muna fuskantar mawuyacin yanayi. Ka yi la’akari da hidimarka a shekarun da suka shige. Shin akwai ranar da ka takura wa kanka sosai don ka fita wa’azi ko na sa’a guda? Idan haka ne, ta tabbata cewa ya daraja ƙoƙarin da ka yi a wannan lokacin. Hakan ya nuna cewa kana “cikin imani” domin ka yi koyi da gwauruwar kuma ka yi iya ƙoƙarinka a hidimar Jehobah.
“KA KARƁI RAINA”
12-14. (a) Ta yaya baƙin ciki ya shafi Iliya? (b) Me ya sa Iliya ya yi baƙin ciki?
12 Annabi Iliya amintaccen bawan Jehobah ne kuma yana da bangaskiya sosai. Amma akwai wani lokaci da ya yi baƙin ciki sosai har ya roƙi Jehobah ya kashe shi, ya ce: “Ya isa; yanzu, ya Ubangiji, ka karɓi raina.” (1 Sar. 19:4) Mutanen da ba su taɓa samun kansu a irin yanayin Iliya ba za su iya yin tunani cewa addu’arsa “rashin hankali” ne. (Ayu. 6:3) Amma Iliya bai yi rashin hankali a furucinsa ba. Ka lura cewa Jehobah bai tsauta masa domin kalamansa ba, amma ya taimake shi.
13 Me ya sa Iliya ya ji hakan? Jim kaɗan kafin wannan lokacin, Iliya ya yi wata mu’ujiza da ta nuna cewa Jehobah Allah ne na gaskiya kuma a sakamako, aka kashe annabawan Baal guda 450. (1 Sar. 18:37-40) Wataƙila Iliya ya yi tsammani cewa bayin Allah za su komo ga bauta ta gaskiya, amma hakan bai yiwu ba. Muguwar Sarauniya Jezebel ta aika wa Iliya saƙo cewa za ta kashe shi. Hakan ya sa hankalin Iliya ya tashi har ya yi gudu zuwa cikin daji a ƙetaren Yahuda.—1 Sar. 19:2-4.
14 Sa’ad da Iliya yake cikin daji shi kaɗai, ya yi baƙin ciki sosai kuma ji kamar aikin banza kawai yake yi. Sai ya ce wa Jehobah: “Ban fi ubannina kyau ba.” Mene ne hakan yake nufi? Yana nufin cewa ba shi da amfani kamar turɓaya ko kuma ƙasusuwan ubanninsa da suka mutu. A ganinsa, ba shi da daraja a gaban Jehobah ko kuma mutane.
15. Ta yaya Jehobah ya tabbatar wa Iliya cewa yana daraja shi?
15 Amma ba haka Allah Maɗaukaki ya ɗauki Iliya ba. Iliya yana da daraja ga Jehobah kuma Jehobah ya aiko da mala’ika domin ya ƙarfafa shi. Jehobah ya kuma tanadar masa da abinci da ruwa domin ya sami ƙarfin yin tafiya na kwana 40 zuwa Dutsen Horeb. Bugu da ƙari, Jehobah ya yi wa Iliya gyara sa’ad da ya yi tsammani cewa babu wani Ba’isra’ile da ke bauta wa Jehobah. Bayan haka, Jehobah ya sake ba Iliya wasu ayyuka kuma ya karɓe su da hannu bibbiyu. Jehobah ya taimaki Iliya kuma a sakamako, ya koma baƙin aikinsa a matsayin annabi cike da ƙwazo.—1 Sar. 19:5-8, 15-19.
16. A waɗanne hanyoyi ne Jehobah ya taɓa taimaka maka?
16 Labarin Iliya zai iya taimaka maka ka gwada ko kana cikin imani kuma ka kasance da ra’ayi mai kyau. Da farko, ka yi tunanin hanyoyi da Jehobah ya taimaka maka. Shin wani dattijo ko Kirista da ya manyanta ya taɓa ƙarfafa ka? (Gal. 6:2) Shin Littafi Mai Tsarki da littattafanmu da kuma taro sun taimaka maka ka san cewa Jehobah yana kula da kai? A nan gaba, idan ka sake amfana daga ɗaya cikin waɗannan tanadodi, ka tuna cewa Jehobah ne ya yi hakan kuma ka yi masa godiya cikin addu’a.—Zab. 121:1, 2.
17. Mene ne Jehobah ya fi so a bayinsa?
17 Na biyu, ka tuna cewa ra’ayi marar kyau zai iya ruɗar da mutum. Yadda Jehobah ya ɗauke mu ne ya fi muhimmanci. (Karanta Romawa 14:4.) Jehobah yana daraja ibadarmu da amincinmu kuma ba ya yin hakan domin mun cim ma wani abu na musamman. Wataƙila abubuwan da ka cim ma a hidimar Jehobah ya wuce yadda kake tunani, kamar yadda ya faru da Iliya. Mai yiwuwa, ka taɓa taimaka wa wasu a cikin ikilisiya da kuma sa’ad da kake wa’azi saboda ƙwazonka, amma ba ka san da hakan ba.
18. Mene ne aikin da Jehobah ya ba ka yake nunawa?
18 Na ƙarshe, ka ɗauki kowane aikin da Jehobah ya ba ka a matsayin tabbaci cewa yana tare da kai. (Irm. 20:11) Kamar Iliya, za ka iya yin baƙin ciki domin ba ka iya cim ma wani abu ba ko kuma ba ka cim ma wani maƙasudanka ba. Amma duk da haka, ba za a iya haɗa gatan da kake da shi da kome ba. Wane gata ke nan? Gatan da kake da shi a matsayin Mashaidin Jehobah da kuma na yin wa’azi. Ka kasance da aminci ga Jehobah. Idan ka yi haka, Yesu ya ce za ka “yi farin ciki tare da ubangijinka.”—Mat. 25:23, LMT.
ADDU’AR “FAKIRI”
19. Wane irin yanayi ne marubucin zabura ta 102 ya fuskanta?
19 Marubucin Zabura ta 102 ya sami kansa cikin tsaka mai wuya. Ya yi baƙin ciki ko wahala sosai domin bai san yadda zai sami mafita ba. Kalamansa sun kuma nuna cewa bai iya jimrewa da matsalolinsa ba. (Zab. 102:3, 4, 6, 11) Ya kammala cewa Jehobah yana so ya yashe shi.—Zab. 102:10.
20. Ta yaya addu’a za ta iya taimaka wa mutumin da ke fama da ra’ayi marar kyau?
20 Duk da haka, marubucin zaburar ya ci gaba da yabon Jehobah. (Karanta Zabura 102:19-21.) Zabura ta 102 ta nuna cewa waɗanda suke “cikin imani” za su iya fuskantar yanayi mai wuya kuma su kasa tattara hankalinsu. Marubucin zaburar ya ji kamar “ƙaramin tsuntsu (gwara) wanda ta ke bisa bene ita kaɗai,” wato kamar matsaloli kawai yake da shi. (Zab. 102:7) Idan ka taɓa jin haka, ka yi addu’a ga Jehobah kamar yadda marubucin zaburar ya yi. Addu’arka za ta iya taimaka maka ka magance ra’ayi marar kyau. Jehobah ya yi alkawari cewa zai ‘ji addu’ar masu-talauci, ba zai rena addu’arsu ba.’ (Zab. 102:17) Ka amince da wannan alkawarin.
21. Ta yaya mutumin da ke fama da ra’ayi marar kyau zai iya magance hakan?
21 Zabura ta 102 ta kuma nuna yadda za mu daɗa kasance da ra’ayi mai kyau. Marubucin zaburar ya fi mai da hankali ga dangantakarsa da Jehobah. (Zab. 102:12, 27) Ya samu ƙarfafa don sanin cewa Jehobah zai taimaka wa bayinsa sa’ad da suke cikin matsala. Saboda haka, idan matsaloli suka hana ka yin hidimar Jehobah sosai, ka yi addu’a game da batun. Ka roƙi Jehobah ya taimake ka ka sami sauƙi daga matsalar kuma ya sa “’yan Adam su labarta sunan Ubangiji.”—Zab. 102:20, 21.
22. Ta yaya kowanenmu zai iya sa Jehobah farin ciki?
22 Hakika, za mu iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki don gwada ko muna “cikin imani” kuma Jehobah yana daraja mu. Gaskiya ne cewa ba za mu iya magance dukan baƙin cikin da muguwar duniyar Shaiɗan take haddasawa ba. Amma, kowanenmu zai iya faranta wa Jehobah rai kuma ya samu rai na har abada idan mun kasance da aminci a hidimarsa.—Mat. 24:13.