Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 92 p. 214-p. 215 par. 1
  • Yesu Ya Je Wajen Masu Kama Kifi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yesu Ya Je Wajen Masu Kama Kifi
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Ya Shawo Kan Tsoro da Kuma Shakka
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Yaƙi Tsoro da Kuma Shakka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 92 p. 214-p. 215 par. 1
Yesu yana magana da mabiyansa yayin da suke gasa kifi a wuta

DARASI NA 92

Yesu Ya Je Wajen Masu Kama Kifi

Bayan Yesu ya bayyana ga manzanninsa, sai Bitrus ya tafi kamun kifi a Tekun Galili. Toma da Yaƙub da Yohanna da wasu almajirai sun bi shi. Sun kwana suna neman kifi, amma ba su kama ko ɗaya ba.

Washegari da sassafe, sai suka ga wani mutum yana tsaye a gefen tekun. Sai ya tambaye su: ‘Kun kama kifi kuwa?’ Suka ce masa: “A’a!” Mutumin ya ce: “Ku jefa taru ga hannun dama na jirgin.” Sa’ad da suka yi haka, sai tarunsu ya cika da kifi har ba su iya ciro shi daga kogin ba. Yohanna ya gane cewa Yesu ne. Ya ce: “Ubangiji ne!” Nan da nan, sai Bitrus ya yi tsalle cikin ruwa kuma ya yi iyo zuwa bakin tekun. Sauran almajiran kuma suka zo a jirgin ruwa.

Sa’ad da suka isa bakin tekun, sai suka ga ana gasa gurasa da kifi. Yesu ya gaya musu su kawo wasu daga cikin kifin da suka kama don su gasa. Bayan haka, sai ya ce: ‘Ku zo ku ci abinci.’

Bitrus ya je wurin Yesu a bakin teku, sauran manzanninsa kuma sun zo a kwale-kwale

Bayan sun gama ci, sai Yesu ya tambayi Bitrus: ‘Kana ƙauna ta fiye da sana’ar kama kifi?’ Bitrus ya ce: ‘E Ubangiji, ka san ina ƙaunar ka.’ Yesu ya ce: ‘To, ka ciyar da ’ya’yan tumakina.’ Yesu ya sake tambayar sa: ‘Bitrus, kana ƙauna ta?’ Bitrus ya ce: ‘Ubangiji ka san ina ƙaunar ka.’ Yesu ya ce: “Ka zama makiyayin tumakina.” Da Yesu ya sake yi wa Bitrus tambayar a ƙaro na uku, sai Bitrus ya soma baƙin ciki. Ya ce: ‘Ubangiji, ka san kome. Ka san ina ƙaunar ka.’ Yesu ya ce masa: “Ka yi kiwon ’yan tumakina.” Sai ya ce wa Bitrus: ‘Ka ci gaba da bi na.’

“[Yesu] ya ce musu, ‘Ku bi ni, zan mai da ku masuntan mutane.’ Nan da nan sai suka watsar da tarunansu, suka bi shi.”​—Matta 4:​19, 20, Littafi Mai Tsarki

Tambayoyi: Wace mu’ujiza ce Yesu ya yi wa masu kamun kifi? Me ya sa Yesu ya yi wa Bitrus wannan tambayar sau uku: ‘Kana ƙauna ta?’

Yohanna 21:​1-19, 25; Ayyukan Manzanni 1:​1-3

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba