Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 93 p. 216-p. 217 par. 5
  • Yesu Ya Koma Sama

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yesu Ya Koma Sama
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • A Kan Dutsen Zaitun
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Yesu Ya Yi Wa’azi Game da Mulkin Allah
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • An Ta da Yesu Daga Matattu!
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
  • An Ba Mabiyan Yesu Ruhu Mai Tsarki
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 93 p. 216-p. 217 par. 5
Manzannin suna ganin sa’ad da Yesu yake komawa sama

DARASI NA 93

Yesu Ya Koma Sama

Yesu ya haɗu da almajiransa a Galili. Ya ba su wani aiki mai muhimmanci kuma ya ce: ‘Ku je ku yi wa dukan mutane a faɗin duniya wa’azi. Ku koya musu abubuwan da na koya muku kuma ku yi musu baftisma.’ Sai ya yi musu alkawari cewa: ‘Ku tuna, ina nan tare da ku a koyaushe.’

A cikin kwanaki 40 bayan an ta da Yesu daga mutuwa, ya bayyana ga mabiyansa a Galili da kuma Urushalima. Ya koya musu abubuwa masu muhimmanci kuma ya yi mu’ujizai da yawa. Sai ya haɗu da su a lokaci na ƙarshe a Dutsen Zaitun. Yesu ya ce: ‘Kada ku bar Urushalima. Ku jira alkawarin da Ubana ya yi.’

Almajiransa ba su san abin da yake nufi ba. Sai suka ce masa: ‘Za ka zama Sarkin Isra’ilawa ne yanzu?’ Yesu ya ce: ‘Lokacin da ya kamata na zama Sarki bai kai ba tukun. Ba da daɗewa ba, za a aiko muku da ruhu mai tsarki kuma za ku soma wa’azi game da ni. Ku je ku yi wa’azi a Urushalima da Yahuda da Samariya da kuma dukan duniya.’

Sai Yesu ya koma sama. Almajiransa sun duba sama ko za su gan shi amma ba su gan shi ba.

Almajiransa sun bar Dutsen Zaitun kuma suka tafi Urushalima. Suna yawan haɗuwa a wani babban ɗaki don su yi addu’a. Suna jiran Yesu ya gaya musu abin da za su yi.

“Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’an nan matuƙa za ta zo.”​—Matta 24:14

Tambayoyi: Wane aiki ne Yesu ya ba almajiransa? Mene ne ya faru a Dutsen Zaitun?

Matta 28:​16-20; Luka 24:​49-53; Yohanna 20:​30, 31; Ayyukan Manzanni 1:​2-14; 1 Korintiyawa 15:​3-6

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba