Gabatarwar Sashe na 6
Sa’ad da Isra’ilawa suka isa Ƙasar Alkawari, mazauni ne ya zama wurin da za su riƙa bauta wa Jehobah. Firistoci ne suke koya musu dokar Allah, alƙalai kuma ne suke musu ja-gorancin. Wannan sashen ya nuna yadda abin da mutum ya yi yake shafen mutane. Kowane mutum a cikinsu yana bukatar ya kasance da aminci ga Jehobah da kuma ɗan’uwansa. Ka ambata yadda halayen Deborah da Naomi da Joshua da Hannatu da ’yar Jephthah da kuma Sama’ila suka shafi mutane a zamaninsu. Ka nanata yadda Rahab da Ruth da Jael da kuma Gibeyonawa suka haɗa kai da Isra’ilawa don sun san cewa Allah yana tare da su duk da cewa su ba Isra’ilawa ba ne.