WAƘA TA 9
Jehobah Ne Sarkinmu!
(Zabura 97:1)
- 1. Ku zo duk mu yabi Jehobah, - Don sammai sun nuna yawan ikonsa. - Mu rera waƙoƙin yabo ga Allahnmu, - Mu bayyana duk ayyukansa. - (AMSHI) - Ku mazaunan sama da na duniyar nan, - Mu yabi Jehobah Sarkinmu! - Ku mazaunan sama da na duniyar nan, - Mu yabi Jehobah Sarkinmu! 
- 2. Mu yi shelar ikon Jehobah, - Yana yin abubuwan al’ajabi. - Jehobah Sarki ne, ya cancanci yabo, - Za mu rusuna a gabansa. - (AMSHI) - Ku mazaunan sama da na duniyar nan, - Mu yabi Jehobah Sarkinmu! - Ku mazaunan sama da na duniyar nan, - Mu yabi Jehobah Sarkinmu! 
- 3. Mulkinsa ya soma a sama, - Yesu Kristi ne Sarki a Mulkinsa. - Dukan maƙiyan Allah - su yi fargaba, - Domin shi ya cancanci yabo. - (AMSHI) - Ku mazaunan sama da na duniyar nan, - Mu yabi Jehobah Sarkinmu! - Ku mazaunan sama da na duniyar nan, - Mu yabi Jehobah Sarkinmu! 
(Ka kuma duba 1 Laba. 16:9; Zab. 68:20; 97:6, 7.)