WAƘA TA 22
Ya Allah, Ka Kawo Mulkinka!
(Ru’ya ta Yohanna 11:15; 12:10)
- 1. Jehobah, ba ka da farko, - Ba ka da ma ƙarshe. - Yesu ne ka ba Mulkinka, - Yana yin nufinka. - Ka riga ka kafa Mulkin, - Jin daɗi zai zo duniya. - (AMSHI) - Allah mun gode ma, - Domin ka kafa Mulkinka. - Ɗanka shi ne Sarki. - Mun ƙosa “Mulkinka ya zo!” 
- 2. Mala’iku suna waƙa, - Suna rera yabo. - Akwai salama a sammai - Don an kori Shaiɗan. - Ka riga ka kafa Mulkin, - Jin daɗi zai zo duniya. - (AMSHI) - Allah mun gode ma, - Domin ka kafa Mulkinka. - Ɗanka shi ne Sarki. - Mun ƙosa “Mulkinka ya zo!” 
- 3. An kusan halaka Shaiɗan, - Yana fushi sosai. - Amma za mu sami ’yanci, - Duk da masifarsa. - Ka riga ka kafa Mulkin, - Jin daɗi zai zo duniya. - (AMSHI) - Allah mun gode ma, - Domin ka kafa Mulkinka. - Ɗanka shi ne Sarki. - Mun ƙosa “Mulkinka ya zo!” 
(Ka kuma duba Dan. 2:34, 35; 2 Kor. 4:18.)