Maya Haihuwa—Menene Manufarta?
MUTANE da yawa sun gaskata cewa mutum yana bukatar a sake haifarsa kafin ya sami ceto na har abada. Amma ka lura da abin da Yesu da kansa ya ce game da manufar wannan maya haihuwa. Ya ce: “In ba a sāke haifar mutum ba, ba zai iya ganin Mulkin Allah ba.” (Yohanna 3:3) Saboda haka, mutum yana bukatar a sake haifarsa domin ya ga Mulkin Allah, ba domin ya sami ceto ba. ‘Amma,’ wasu za su ce, ‘waɗannan furcin biyu, ganin Mulki da kuma samun ceto, ba abu ɗaya suke nufi ba?’ A’a ba abu ɗaya suke nufi ba. Domin mu fahimci bambancin, bari mu fahimci ma’anar wannan furcin “Mulkin Allah.”
Mulki na nufin gwamnati. Saboda haka “Mulkin Allah” yana nufin “gwamnati ta Allah.” Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa Yesu Kristi, “ɗan mutum,” shi ne Sarkin Mulkin Allah kuma cewa Yesu yana da abokan sarauta. (Daniel 7:1, 13, 14; Matta 26:63, 64) Ƙari ga haka, wahayi da aka bai wa manzo Yohanna ya nuna cewa abokan sarautar Yesu an zaɓe su ne daga “cikin kowace kabila, da kowane harshe, da al’umma, da iri” “ kuma za su yi “mulki bisa duniya.” “ (Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 20:6) Kalmar Allah kuma ta nuna cewa waɗanda za su yi sarauta suna cikin “ƙaramin garke” na mutane 144, 000 “waɗanda aka fanshe su daga cikin duniya.”—Luka 12:32; Ru’ya ta Yohanna 14:1, 3.
Daga Ina ne Mulkin Allah zai yi sarauta? An kira “Mulkin Allah” kuma “Mulkin sama,” wanda ya nuna cewa Yesu da abokan sarautarsa za su yi sarauta ne daga samaniya. (Luka 8:10; Matta 13:11) Saboda haka, Mulkin Allah gwamnati cewa ta samaniya da ta ƙunshi Yesu Kristi da kuma rukunin abokan sarautarsa da aka zaɓa daga tsakanin ’yan adam.
To menene Yesu ya ke nufi sa’ad da ya ce sai an sake haifar mutum kafin ya “ga Mulkin Allah”? Abin da yake nufi shi ne dole ne a sake haifar mutum kafin ya yi sarauta da Kristi a samaniya. Saboda haka, manufar maya haihuwar ita ce ta shirya mutane kalilan domin sarauta a samaniya.
Mun riga mun ga cewa maya haihuwa tana da muhimmanci ƙwarai, Allah ne ya kafa ta, kuma ya shirya rukunin mutane domin sarauta a samaniya. Ta yaya maya haihuwar take faruwa?
[Bayanin da ke shafi na 7]
Manufar maya haihuwar ita ce ta shirya mutane kalilan domin sarauta a samaniya
[Hotunan da ke shafi na 7]
Yesu Kristi tare da rukunin mutane kalilan da aka zaɓa daga tsakanin ’yan adam su za su kasance Mulkin Allah