Sarauta ga Wasu, Albarka ga Yawanci
TUN a zamanin manzanni, Allah ya fara zaɓa daga tsakanin mutane ɗan adadi ƙalilan na Kiristoci masu aminci su zama ’ya’yansa. Canji da waɗannan za su fuskanta cikakke ne sosai har da kalmar Allah ta kwatanta shi da maya haihuwa. Dalilin wannan maya haihuwar shi ne ya shirya waɗannan bayin Allah da aka sake haifarsu su zama sarakuna a samaniya. (2 Timothawus 2:12) Domin su yi wannan sarauta, aka tashe su daga matattu zuwa rayuwa a samaniya. (Romawa 6:3-5) A samaniya, “suna kuwa mulki bisa duniya” tare da Kristi.—Ru’ya ta Yohanna 5:10; 11:15.
Duk da haka, kalmar Allah ta ce, ban da waɗanda aka sake haifarsu, wasu ma za su sami ceto na har abada. A cikin Littafi Mai Tsarki (a cikin Nassosin Ibraniyawa da kuma Nassosin Hellenanci na Kiristoci), an faɗi cewa Allah yana da niyar ceton rukuni biyu na mutane, ɗan ƙaramin rukunin da za su rayu a samaniya da kuma babban rukuni da za su rayu a duniya. Alal misali, ka lura da abin da manzo Yohanna ya rubuta wa ’yan’uwa masu bi da aka sake haifarsu. Ya yi magana game da Yesu: “shi ne kuwa fansar zunubanmu; ba kuwa ta namu kaɗai ba, amma ta duniya duka kuma.”—1 Yohanna 2:2.
Hakazalika, manzo Bulus ya rubuta: “Gama begen talikai [babban rukuni] yana sauraron bayyanuwar ’ya—yan Allah [ƙaramin rukuni].” (Romawa 8:19-21) Ta yaya za a fahimci wannan kalamai na manzo Yohanna da kuma Bitrus? A wannan hanyar: Waɗanda aka sake haifarsu za su kasance cikin gwamnatin samaniya. Menene manufar haka? Domin su kawo amfani na dindindin ga miliyoyin mutane, talakawan gwamnatin Allah waɗanda za su rayu a nan duniya. Saboda haka, Yesu ya koyar da almajiransa su yi addu’a: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.”—Matta 6:10.
Wannan gaskiya game da ceto da aka ba rukuni biyu an same ta cikin Nassosi na Ibraniyawa. Alal misali, ka lura cewa Jehobah ya gaya wa kakan Yesu Ibrahim: “Cikin zuriyarka [ɗan ƙaramin rukunin] kuma dukan al’umman duniya [babban rukuni] za su sami albarka.” (Farawa 22:18) Hakika, za a albarkaci dukan al’ummai ta wajen “zuriyar” Ibrahim.
Wanene wannan “zuriya”? Yesu Kristi ne, da kuma waɗanda aka sake haifarsu, waɗanda Allah ya mayar da su ’ya’yansa. Manzo Bulus ya yi bayani: “Idan kuma na Kristi ne, zuriyar Ibrahim ku ke kuma.” (Galatiyawa 3:16, 29) To wace albarka ce mutanen dukan al’ummai za su samu ta wajen wannan “zuriyar”? Gatar komawa ga tagomashin Allah da kuma samun rai madawwami a aljanna a duniya. Mai zabura Dauda ya annabta: “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zabura 37:29; Ishaya 45:18; Ru’ya ta Yohanna 21:1-5.
Hakika, sarauta a samaniya an keɓe ta saboda mutane ƙalilan, amma albarkar mulkin samaniya, wato rai madawwami a duniya, da kuma dukan albarkatansa ga mutane ne da yawa. Bari kai da iyalinka ku kasance cikin waɗanda za su sami albarka da Mulkin Allah zai kawo.
[Hotunan da ke shafi na 12]
Miliyoyin mutane za su sami albarkar rai madawwami a nan duniya. Za ka kasance cikinsu?