WAƘA TA 15
Mu Yabi Ɗan Allah!
Hoto
(Ibraniyawa 1:6)
1. Mu Yabi Ɗan Allah,
Jehobah ya naɗa shi
Domin ya yi adalci,
Mu rayu har abada.
Zai ɗaukaka Jehobah,
Ya sa a san da shi.
Don yana son Jehobah
Da kuma Mulkinsa.
(AMSHI)
Mu yabi Ɗan Allah!
Kowa ya yabi Yesu.
Domin shi ne sarkinmu,
Kuma ya soma Mulki!
2. Mu yabi Ɗan Allah,
Ya mutu don mu rayu.
Ya sadaukar da ransa
Don a gafarta mana.
Abokan sarautarsa
Suna kan jiran sa.
Mulkin Yesu a sama
Zai ɗaukaka Allah.
(AMSHI)
Mu yabi Ɗan Allah!
Kowa ya yabi Yesu.
Domin shi ne sarkinmu,
Kuma ya soma Mulki!
(Ka kuma duba Zab. 2:6; 45:3, 4; R. Yoh. 19:8.)