WAƘA TA 14
Mu Yabi Sabon Sarkinmu
Hoto
(Zabura 2:12)
1. Dubban mutane na zuwa
daga dukan al’umma.
Yesu ne ke tattara su
cikin ikilisiya.
Allah ya kafa Mulkinsa,
Mulkin zai kawo albarka.
Wannan bege ne mai tamani,
Yana sa mu farin ciki.
(AMSHI)
Mu yabi Jehobah, Har da Ɗansa Kristi,
Don shi ne Sarkin Sarakuna.
Ba mu da wani Sarki kamar sa,
Mu ɗaukaka sunansa.
2. Mu yabi Kristi Sarkinmu,
da waƙoƙin bakinmu.
Shi zai yi sarauta kuma
zai sa mu sami ceto.
Yesu zai kawo albarka,
Zai kuma cire mugunta.
Kristi zai tayar da matattu
Dukanmu za mu yi murna!
(AMSHI)
Mu yabi Jehobah, Har da Ɗansa Kristi,
Don shi ne Sarkin Sarakuna.
Ba mu da wani Sarki kamar sa,
Mu ɗaukaka sunansa.
(Ka kuma duba Zab. 2:6; 45:1; Isha. 9:6; Yoh. 6:40.)