WAƘA TA 59
Mu Yabi Jehobah
Hoto
(Zabura 146:2)
1. Mu yabi Jah,
Mu yi waƙa!
Ya nuna mana alheri sosai.
A koyaushe,
Mu yabe shi
Don ƙaunarsa da kuma ikonsa.
Mu yabe shi, mu yi wa’azi ma.
2. Mu yabi Jah,
Yana son mu,
Yana biyan dukan bukatunmu.
Yana kula
Da bayinsa.
Ruhunsa yana taimaka mana.
Za mu bauta wa Jehobah kullum.
3. Mu yabi Jah
Mai adalci,
Mu dogara ga Jehobah Allah.
Zai magance;
Matsaloli,
Za mu more albarkar Mulkinsa.
Ku zo mu ci gaba da yabon sa!
(Ka kuma duba Zab. 94:18, 19; 145:21; 147:1; 150:2; A. M. 17:25.)