Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 6/1 pp. 3-7
  • Ka Yabi Jehovah Don Ayyukansa Masu Girma!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yabi Jehovah Don Ayyukansa Masu Girma!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Sanar da Ayyukan Jehovah da Suka Isa Yabo!
  • ‘Ku Yabi Jah!’
  • Ayyuka da ke Haɗe da Madawwamin Ƙudurin Allah
  • Dubbai Suna Rugawa Zuwa Sujjada ta Gaskiya
  • Matasa Ku Yabi Jehobah!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Mu Yabi Jehobah Allahnmu!
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
  • Mu Yabi Jehobah
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
  • Darussa Daga Littafin Zabura na Biyar
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 6/1 pp. 3-7

Ka Yabi Jehovah Don Ayyukansa Masu Girma!

“Raina yana girmama Ubangiji . . . gama shi da shi ke mai-iko ya yi al’amura masu-girma gareni.”—Luka 1:46-49.

1. Domin waɗanne ayyuka masu girma ya dace mu yabi Jehovah?

JEHOVAH ya cancanci a yabe shi domin ayyukansa masu girma. Lokacin da annabi Musa ya ba da cikakken labari na ceton Isra’ila daga ƙasar Masar, ya ce: “Naku idanu sun ga dukan manyan ayyuka na Ubangiji.” (Kubawar Shari’a 11:1-7) Hakanan ma, lokacin da mala’ika Jibrailu ya sanar da budurwa Maryamu game da haihuwar Yesu da ke zuwa, ta ce: “Raina yana girmama Ubangiji . . . gama shi da shi ke mai-iko ya yi al’amura masu-girma gareni.” (Luka 1:46-49) Mu Shaidun Jehovah, muna yabonsa don irin waɗannan ayyuka masu girma, kamar su ’yantar da Isra’ilawa daga bauta a ƙasar Masar da kuma haihuwar Ɗansa da yake ƙauna ta mu’ujiza.

2. (a) Menene “madawwamin nufi” na Allah yake nufi ga mutane masu biyayya? (b) Menene Yohanna ya gani a tsibirin Batmusa?

2 Ayyuka masu girma da yawa na Jehovah game da “madawwamin nufi” nasa ne ya albarkaci mutane masu biyayya ta wurin Almasihu da sarautar Mulkinsa. (Afisawa 3:8-13) Wannan nufi na tasowa da kaɗan da kaɗan lokacin da aka bar tsoho manzo Yohanna ya ga a cikin ru’ya ƙofa a buɗe cikin sama. Ya ji murya mai kama da ta ƙaho ta ce: “Ka hau daganan, in nuna maka al’amuran da za su faru dole gaban nan.” (Ru’ya ta Yohanna 4:1) Yayin da gwamnatin Roma ta ƙore shi zuwa tsibirin Batmusa “sabili da maganar Allah da shaidar Yesu,” Yohanna ya karɓi “ru’ya ta Yesu Kristi.” Abin da manzon ya gani kuma ya ji ya bayyana abubuwa da yawa game da madawwamin nufin Allah, da haka ya yi tanadin wayewa a ruhaniya da kuma ƙarfafa a kan lokaci ga dukan Kiristoci na gaskiya.—Ru’ya ta Yohanna 1:1, 9, 10.

3. Su wa suke wakiltan dattawa 24 da Yohanna ya gani cikin ru’ya?

3 Ta wannan ƙofa da take buɗe a sama, Yohanna ya ga dattawa 24, da aka ɗora a kan kursiyi aka yi musu rawani kamar sarakuna. Sun fāɗi a gaban Allah suka ce: “Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Waɗannan dattawa suna wakiltan dukan shafaffu Kiristoci da aka tashe su zuwa matsayi na ɗaukaka da Allah ya yi musu alkawari. Sun motsa sun yabi Jehovah domin ayyukansa masu girma na halitta. Mu ma mun yi mamakin tabbacin “ikonsa madawwami da allahntakarsa.” (Romawa 1:20) Yayin da muke ƙara koyo game da Jehovah, muna da ƙarin dalilin yaba masa don ayyukansa masu girma.

Ka Sanar da Ayyukan Jehovah da Suka Isa Yabo!

4, 5. Ka ba da misalan yadda Dauda ya yabi Jehovah.

4 Dauda mai Zabura ya yabi Allah domin ayyukansa masu girma. Alal misali, Dauda ya rera: “Ku raira yabo ga Ubangiji, wanda ya ke zaune cikin Sihiyona: ku bada labarin ayyukansa a wurin al’ummai. Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai; ka dubi ƙasƙancin da ni ke sha a hannun maƙiyana, kai da ka ke ɗaukakata daga ƙofofin mutuwa; domin in bayyana dukan yabonka; a cikin ƙofofin ɗiyar Sihiyona.” (Zabura 9:11, 13, 14) Bayan ya ba ɗansa Sulemanu zanen ginin haikali, Dauda ya albarkaci Allah kuma ya yaba masa , yana cewa: “Girma, da iko, da ɗaukaka, da nasara, da sarauta, naka ne; ya Ubangiji . . . Mulki naka ne, ya Ubangiji, ka ɗaukaka kuma bisa kan komi. . . . Yanzu fa, ya Allahnmu, muna gode maka, muna yabon sunanka mai-daraja.”—1 Labarbaru 29:10-13.

5 Nassosi sun yi gayya a kai a kai—hakika, sun aririce mu—mu yabi Allah, yadda Dauda ya yi. Littafin Zabura na ɗauke da furcin yabo masu yawa ga Allah, kusan rabin waɗannan waƙoƙi an ce daga Dauda ne. A kai a kai yana yabo da kuma godiya wa Jehovah. (Zabura 69:30) Bugu da ƙari, tun farko, waƙoƙi da Allah ya hure na Dauda da na wasu an yi amfani da su a yabon Jehovah.

6. Ta yaya Zabura hurariya ta kasance da amfani gare mu?

6 Zabura lalle tana da amfani ga masu bauta wa Jehovah! Yayin da muke so mu gode wa Allah domin dukan ayyukansa masu girma dominmu, za mu iya tuna kalmomi masu kyau da ke cikin Zabura. Alal misali, yayin da muka farka kowacce rana, za mu iya motsawa mu yi furci irin wannan: “Yin godiya ga Ubangiji yana da kyau, da rairawar yabbai ga sunanka, ya Maɗaukaki: a bayyana rahamarka da safe, amincinka kuma kowane dare, . . . gama bisa ga aikinka ka faranta zuciyata, ya Ubangiji: zan yi sowa domin ayyukan hannuwanka.” (Zabura 92:1-4) Yayin da muka sha kan wata tangarɗa ga ci gabanmu a ruhaniya, za mu so mu furta farin cikinmu da godiya cikin addu’a, kamar yadda mai Zabura ya yi lokacin da ya rera: “Ku zo, mu raira ga Ubangiji: mu yi sowa ga fa na cetonmu. Mu zo gabansa da godiya, mu yi sowa gareshi da waƙoƙi.”—Zabura 95:1, 2.

7. (a) Menene abin lura musamman cikin waƙoƙi da yawa da Kiristoci suke rerawa? (b) Menene dalili ɗaya na zuwa taro da wuri kuma mu zauna har ƙarshe?

7 Sau da yawa muna ta da muryarmu mu rera waƙoƙin yabo ga Jehovah a taron ikilisiya, manyan taro, da taron gunduma. A bayyane yake cewa da yawa cikin waɗannan kalmomin da aka hure ne daga littafin Zabura. Muna farin ciki da muke da tarin waƙoƙi na yabo mai daɗaɗa zuciya ga Jehovah a zamanin yau! Rera waƙar yabo ga Allah shi ne dalili ɗaya mai kyau da ya sa za mu zo taro da wuri kuma mu zauna har ƙarshe, da haka za mu haɗu da ’yan’uwa masu bi wajen yabon Jehovah da waƙa da kuma addu’a.

‘Ku Yabi Jah!’

8. Menene ma’anar kalmar nan “Hallelujah,” kuma yaya ake amfani da ita koyaushe?

8 Yabon Jehovah ya fito daga kalmar nan “Hallelujah,” furcin Ibrananci ne da kusan koyaushe ana juya ta ‘ku yabi Jah.’ Alal misali, a Zabura 135:1-3, mun samu wannan gayyar mai daɗaɗawa, mai ƙarfi: “Hallelujah! Ku yabi sunan Ubangiji, ku yi yabonsa, ku bayin Ubangiji: ku da ke tsayawa cikin gidan Ubangiji, cikin farfajiyan gidan Allahnmu. Ku yabi Ubangiji; gama Ubangiji nagari ne: ku raira yabbai ga sunansa; gama yana da daɗi.”

9. Menene ke motsa mu mu yabi Jehovah?

9 Yayin da muke bimbini a kan ayyuka na halitta masu ban al’ajabi na Allah da dukan ayyukansa dominmu, godiya daga zuciya tana motsa mu mu yabe shi. Yayin da muka yi tunani a kan abubuwan mu’ujiza da Jehovah ya yi domin mutanensa a lokacin dā, zukatanmu na motsa mu mu yabe shi. Lokacin da muke bimbini a kan alkawura na abubuwa masu girma da Jehovah zai yi har ila yau, neman hanyoyi da za mu furta yabo da godiya ne muke yi.

10, 11. Yaya rai da muke da shi yake ba mu dalilin yabon Allah?

10 Rai da muke da shi yana ba mu ƙaƙƙarfan dalili na yabon Jah. Dauda ya rera: “Zan yi godiya gareka [Jehovah] gama ƙirata abin ban tsoro ce, abin al’ajabi ce kuwa: ayyukanka suna da ban al’ajabi; wannan ma raina ya sani sarai.” (Zabura 139:14) Hakika, ‘ƙirarmu abin ban tsoro ce’ kuma muna da kyauta mai tamani irinsu gani, ji, da tunani. Saboda haka, bai kamata mu yi rayuwa yadda za mu yabi Mahaliccinmu ba? Bulus ya yi irin wannan tunani lokacin da ya rubuta: “Ko kuna ci fa, ko kuna sha, ko kuwa iyakar abin da ku ke yi, a yi duka domin a girmama Allah.”—1 Korinthiyawa 10:31.

11 Za mu yi dukan abubuwa domin mu girmama Jehovah idan muna ƙaunarsa da gaske. Yesu ya ce babbar doka ita ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka, da dukan ƙarfinka.” (Markus 12:30; Kubawar Shari’a 6:5) Babu shakka ya kamata mu ƙaunaci Jehovah kuma mu yabe shi Mahaliccinmu kuma Mai Ba da “kowacce kyakkyawar baiwa da kowacce cikakkiyar kyauta.” (Yaƙub 1:17; Ishaya 51:13; Ayukan Manzanni 17:28) Ballantana ma, tunaninmu, ruhaniyarmu, da ƙarfinmu—duka ingancinmu da iyawarmu—sun zo daga Jehovah ne. Da yake shi ne Mahaliccinmu, ya cancanci mu ƙaunace shi kuma mu yabe shi.

12. Yaya ka ke ji game da ayyukan Jehovah masu girma da kuma kalmomin Zabura 40:5?

12 Ayyuka masu girma na Jehovah suna ba mu dalilai masu yawa da za mu yi ƙaunarsa kuma mu yabe shi! Dauda ya rera: “Ya Ubangiji Allahna, ayyuka masu-ban al’ajabi, waɗanda ka yi, suna dayawa, duk da tunaninka waɗanda sun nufo wajenmu: ba su lissaftuwa a gabanka; ko da ni ke so in bayyana su in bada labarinsu, sun fi gaban lissafi.” (Zabura 40:5) Dauda bai iya faɗin dukan ayyuka masu ban al’ajabi na Jehovah ba, ko mu ma ba za mu iya ba. Bari koyaushe mu yabi Allah lokacin da aka jawo hankalinmu ga wani cikin ayyukansa masu girma.

Ayyuka da ke Haɗe da Madawwamin Ƙudurin Allah

13. Yaya begenmu ya haɗa da ayyukan Allah masu girma?

13 Begenmu don gaba nan ya haɗa da ayyuka masu girma da suka isa yabo da ke haɗe da madawwamin ƙuduri na Allah. Bayan tawaye a Adnin, Jehovah ya yi annabci na farko da ke cike da bege. Da yake yanka wa maciji hukunci, Allah ya ce: “Tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma: shi za ya ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje duddugensa.” (Farawa 3:15) Bege cikin Ɗan macen da aka yi alkawarinsa ya kasance a zuciyar mutane masu aminci bayan Jehovah ya yi abu mai girma wajen ceton Nuhu da iyalinsa lokacin Rigyawa ta dukan duniya da ta share muguwar duniya. (2 Bitrus 2:5) Alkawura na annabci ga irin waɗannan mutane masu aminci kamar su Ibrahim da Dauda sun ba da ƙarin fahimi ga abin da Jehovah zai cim ma ta wannan Ɗa.—Farawa 22:15-18; 2 Samu’ila 7:12.

14. Menene misali mafi girma na ayyukan Jehovah masu girma domin mutane?

14 Nuni mafi girma da Jehovah ya yi shi mai yin ayyuka masu girma domin mutane ya faru ne lokacin da ya ba da Ɗansa makaɗaici—Ɗa na alkawari, Yesu Kristi—hadayar fansa. (Yohanna 3:16; Ayukan Manzanni 2:29-36) Fansa ta ba da dalilin sulhunta da Allah. (Matta 20:28; Romawa 5:11) Jehovah ya kawo mutane na farko da ya sulhunta da su cikin ikilisiyar Kirista, wadda aka kafa a Fentakos na shekara ta 33 A.Z. Da taimakon ruhu mai tsarki, suka yi wa’azi a ko’ina, suna nuna yadda mutuwar Yesu da tashinsa daga matattu ya buɗe hanya don mutane masu biyayya su samu madawwamin albarka a ƙarƙashin sarautar Mulkin Allah a sama.

15. Ta yaya Jehovah ya aikata abubuwa a hanya ta ban al’ajabi a zamaninmu?

15 A zamaninmu, Jehovah ya aikata abubuwa a hanya ta ban al’ajabi ya tattara shafaffun Kiristoci na ƙarshe. An riƙe iska na halaka don ya ƙyale a hatimce raguwar 144,000 waɗanda za su yi sarauta da Kristi a sama. (Ru’ya ta Yohanna 7:1-4; 20:6) Allah ya tabbata cewa an ceci shafaffu Kiristoci daga bauta ta ruhaniya na “Babila Babba,” daular addinin ƙarya ta duniya. (Ru’ya ta Yohanna 17:1-5) Wannan ceto a shekara ta 1919 da tsarewa ta Allah da suke gani tun lokacin ya bai wa raguwar shafaffu dama su yi menene? Don su haskaka wajen ba da shaida na ƙarshe kafin Jehovah ya kawo ƙarshen mugun tsarin abubuwa na Shaiɗan a “babban tsananin” da ke zuwa da sauri.—Matta 24:21; Daniel 12:3; Ru’ya ta Yohanna 7:14.

16. Menene ke faruwa domin aikin wa’azi na Mulki na zamanin yau da ake yi a dukan duniya?

16 Shaidun Jehovah shafaffu da ƙwazo sun ja-gabanci aikin wa’azi na Mulkin a dukan duniya. Sakamakonsa, “waɗansu tumaki” da suke ƙaruwa suna zama masu bauta wa Jehovah yanzu. (Yohanna 10:16) Muna farin ciki cewa har ila yau mutane masu tawali’u na duniya suna da zarafi su haɗu da mu wajen yabon Jehovah. Waɗanda suka amsa gayyatar su “zo” suna cikin layin samun ceto a babban tsananin, da begen za su yi yabon Jehovah duk fil azal.—Ru’ya ta Yohanna 22:17.

Dubbai Suna Rugawa Zuwa Sujjada ta Gaskiya

17. (a) Yaya Jehovah yake ayyuka masu girma game da aikinmu na wa’azi? (b) Ta yaya Zechariah 8:23 ke cika?

17 Jehovah yanzu yana ayyuka masu girma waɗanda suka isa yabo game da aikinmu na wa’azi. (Markus 13:10) A shekarun baya bayan nan, ya ‘buɗe kofa mai faɗi ta aiki.’ (1 Korinthiyawa 16:9) Wannan ya sa ta yiwu a sanar da bishara a duk yankuna masu faɗi inda magabtan gaskiya a dā sun hana. Mutane da yawa da a dā suna zama cikin duhu na ruhaniya yanzu suna na’am ga gayyatar su bauta wa Jehovah. Suna cika waɗannan kalmomi na annabci: “Hakanan Ubangiji mai-runduna ya faɗi; a cikin waɗannan kwanaki mutum goma daga cikin dukan harsunan al’ummai za su kama ƙafar wanda shi ke Ba-yahudi, su ce, Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.” (Zechariah 8:23) Waɗannan ‘mutane’ Yahudawa na ruhaniya ne, raguwar shafaffu Kiristoci na zamanin yau. Da yake goma na nufin cika irin ta duniya, “mutum goma” “taro mai-girma,” ne da aka kawo su su yi cuɗanya da “Isra’ila ta Allah,” da suka haɗu suka zama “garke ɗaya.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10; Galatiyawa 6:16) Abin farin ciki ne mu ga mutane da yawa yanzu suna bauta tare su masu bauta wa Jehovah Allah!

18, 19. Waɗanne tabbaci ne ke akwai cewa Jehovah ya albarkaci aikin wa’azinmu?

18 Ya burge mu cewa dubbai—kai, ɗarurruwan dubbai—suna karɓan sujjada ta gaskiya a ƙasashe da a dā addinin ƙarya ne ke mallakar su da kamar mutane ba za su taɓa karɓan bishara ba. Ka duba Yearbook of Jehovah’s Witnesses na shekarar nan, ka lura da ƙasashe da yanzu suna ba da rahoton wa’azi daga 100,000 zuwa kusan 1,000,000 na masu shelar Mulki. Wannan tabbaci ne mai ƙarfi cewa Jehovah ya albarkaci aikin wa’azi na Mulkin.—Misalai 10:22.

19 Mu mutanen Jehovah, muna yabon kuma gode wa Ubanmu na sama da ya ba mu manufa ta gaske a rayuwa, aiki mai lada cikin hidimarsa, da kuma abu mai kyau a nan gaba. Muna begen cikar dukan alkawura na Allah da kuma aniyyar mu ‘tsaya cikin ƙaunar Allah, mai kaiwa ga rai madawwami.’ (Yahuda 20, 21) Muna murna ganin cewa taro mai girma da suke yabon Allah yanzu adadinsu ya kai 6,000,000! Tare da albarkar Jehovah, raguwar shafaffu tare da abokan tarayyarsu waɗansu tumaki an shirya su cikin ikilisiyoyi 91,000 a ƙasashe 235. Ta wurin ƙoƙarin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” ana ciyar da dukanmu sosai a ruhaniya. (Matta 24:45) Ƙungiya ta tsarin Allah mai ci gaba da kula cikin ƙauna suna gudanar da tsarin aikin Mulkin ta rassa 110 na Shaidun Jehovah. Muna godiya cewa Jehovah ya motsa zukatan mutanensa su ‘girmama shi da wadatarsu.’ (Misalai 3:9, 10) Sakamakon wannan, aikinmu na wa’azi na duniya duka ya ci gaba, da gine-gine don buga littattafai, gidajen Bethel da na ’yan wa’azi a ƙasashen waje, kuma ana gina Majami’un Mulki, Majami’un Babban Taro yadda bukata ta kama.

20. Yaya ya kamata bimbini a kan ayyuka masu girma na Jehovah da suka isa yabo su taɓa mu?

20 Ba zai yiwu ba mu ambata dukan ayyuka masu girma da suka isa yabo na Ubanmu na sama. Amma wani mai zuciyar kirki zai iya ya ƙi bin taro masu yabon Jehovah? Ko kaɗan! Saboda haka, bari dukan masu ƙaunar Allah su yi yabo da farin ciki: “Hallelujah! Ku yabi Ubangiji daga sammai: Ku yi yabonsa a wurare maɗaukaka. Ku yi yabonsa, ya ku dukan mala’ikunsa: . . . Samari da ’yan mata; tsofaffi da yara: bari su yabi sunan Ubangiji; gama sunansa kaɗai maɗaukaki ne: darajatasa tana bisa kan duniya da sama.” (Zabura 148:1, 2, 12, 13) I, yanzu kuma har abada, bari mu yabi Jehovah don ayyukansa masu girma!

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene wasu ayyuka na Jehovah da suka isa yabo?

• Me ya sa ka motsa ka yabi Jehovah?

• Yaya begenmu ke haɗe da ayyuka masu girma na Allah?

• Yaya Jehovah yake ayyuka da suka isa yabo game da aikin wa’azi na Mulki?

[Hoto a shafi na 4]

Kana saka baki wajen rera waƙoƙin yabo ga Jehovah da dukan zuciyarka?

[Hotuna a shafi na 7]

Muna farin ciki cewa har ila akwai zarafi don mutane masu tawali’u su haɗu da mu wajen yabon Jehovah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba