Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 7/1 pp. 13-18
  • Matasa Ku Yabi Jehobah!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matasa Ku Yabi Jehobah!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Za Ku Yabi Jehobah?
  • Yadda Wasu Matasa Suka Yabi Jehobah
  • Ta Yaya Za Ku Yabi Jehobah?
  • Yaushe ya Kamata Ku Soma Yabon Jehobah?
  • Mu Yabi Sunan Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Yabi Jehovah Don Ayyukansa Masu Girma!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Mu Yabi Jehobah Allahnmu!
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 7/1 pp. 13-18

Matasa Ku Yabi Jehobah!

“Ku yabi Ubangiji daga duniya, . . . ku samari da ’yan mata!”—ZABURA 148:7, 12.

1, 2. (a) Yara da yawa sun san an hana su waɗanne abubuwa? (b) Me ya sa ba shi da kyau yara su yi abubuwa da iyayensu suka hana su yi?

YARA sau da yawa sun san abin da ba a son su yi. Yawancinsu za su gaya maka shekara nawa za su kai kafin a yarda su ketare titi da kansu, ko su shiga barci ko kuma lokacin da za su soma tuƙi. Wani lokaci, yaro zai ji cewa abubuwa da yawa da yake son ya yi, ana ce masa, “Ka jira sai ka yi girma.”

2 Matasa, iyayenku suna ji ya fi kyau su yi irin wannan hani, wataƙila don su kāre ku. Kun sani kuma cewa yana faranta wa Jehobah rai idan kuka yi wa iyayenku biyayya. (Kolosiyawa 3:20) Kuna jin cewa ba ku soma ainihin rayuwa ba tukuna don waɗannan hani? Ana hana ku dukan abubuwa masu muhimmanci har sai kun yi girma ne? Wannan ba gaskiya ba ne! Da akwai aiki da ake yi yau da ya fi kowane zarafi da kake jira muhimmanci. Ana barin matasa su yi wannan aikin kuwa? Allah Mai Iko Duka ne da kansa yake gayyatarku ku yi hakan!

3. Jehobah ya gayyaci matasa su sa hannu a wane aiki na musamman, waɗanne tambayoyi za mu bincika yanzu?

3 Wane aiki ne muke maganarsa? Ku lura da kalmomin ayar jigonmu na wannan talifin: “Ku yabi Ubangiji daga duniya, . . . ku samari da ’yan mata! Ku yabe shi, ku tsofaffi da yara!” (Zabura 148:7, 12) Kana da gata da ya fi girma: Za ka iya yabon Jehobah. Da yake kai matashi ne kana farin cikin sa hannu a wannan aikin kuwa? Matasa da yawa suna yin haka. Don a ga abin da ya sa ya dace a ji hakan, bari mu bincika tambayoyi uku. Ta farko, me ya sa ya kamata ku yabi Jehobah? Ta biyu, ta yaya za ku yabe shi da kyau? Ta uku, yaushe ne ya kamata a soma yabon Jehobah?

Me Ya Sa Za Ku Yabi Jehobah?

4, 5. (a) In ji Zabura 148, muna cikin wane yanayi mai ban al’ajabi? (b) Ta yaya halittu da ba sa magana ko tunani har ila suke yabon Jehobah?

4 Domin Jehobah Mahalicci ne, dalili na musamman ke nan da ya sa za a yabe shi. Zabura ta 148 ta taimaka mana mu mai da hankali ga wannan gaskiyar. Alal misali: Idan ka sadu da rukunin mutane da suke waƙa mai daɗi da ke motsawa, yaya za ka ji? A ce waƙar na ɗauke da kalmomi da ka sani gaskiya ne, ana rera abubuwa da ka sani suna da muhimmanci, da ke sa mutum farin ciki, kuma da ban ƙarfafa? Za ka so ka koyi kalmomin kuma ka soma rerawa? Yawancinmu za mu yi hakan. Zabura ta 148 ta nuna kana cikin irin wannan yanayi amma wanda ya fi kyau. Wannan zabura ta kwatanta taro mai girma cewa dukansu suna yabon Jehobah cikin haɗin kai. Yayin da kake karanta wannan zabura, za ka lura da wani abin ban mamaki. Menene wannan?

5 Masu yabo da yawa da aka kwatanta a Zabura ta 148 ba sa magana ko kuma tunani. Alal misali, mun karanta cewa rana, wata, taurari, dusar ƙanƙara, iska, duwatsu, da tuddai suna yabon Jehobah. Ta yaya waɗannan halittu marasa rai suke hakan? (Ayoyi 3, 8, 9) Hakika, yadda itatuwa, halittun cikin teku, da dabbobi suke yi. (Ayoyi 7, 9, 10) Ka taɓa kallon faɗuwar rana ko kuwa sha huɗun wata tana tafiya a sararin samaniya, shin ka yi dariyar farin ciki da kake kallon dabbobi suna wasa ko kuwa ka yi mamaki game da wani tsarin ƙasa da ka gani? Idan haka ne ka “ji” waƙar yabo daga halittu. Dukan abubuwa da Jehobah ya yi suna tuna mana cewa shi ne Mahalicci maɗaukaki, babu wani a dukan sararin samaniya da yake da iko, hikima, ko yana da ƙauna kamar shi.—Romawa 1:20; Wahayin Yahaya 4:11.

6, 7. (a) Zabura ta 148 ta kwatanta waɗanne halittu masu basira da suke yabon Jehobah? (b) Me ya sa za mu motsa mu yabi Jehobah? Ka ba da misali.

6 Zabura ta 148 ta kuma kwatanta halittu masu basira cewa suna yabon Jehobah. Aya ta 2 ta ce “rundunan” Jehobah, wato mala’iku suna yabon Allah. A cikin aya ta 11 an gayyaci ’yan adam masu iko da rinjaya, kamar su sarakuna da hukumomi su haɗu a yabon. Idan mala’iku masu iko suna farin ciki wajen yabon Jehobah, ba ɗan adam da zai ce yana da muhimmanci ainun da ba zai yabi Jehobah ba. A ayoyi 12 da 13 an gayyace ku matasa ku yabi Jehobah. Kuna son ku yi hakan ne?

7 Ka yi la’akari da wannan misali. Idan kana da wani aboki na kusa da yake da wani iyawa na ban mamaki—wataƙila wasanni, fasaha, ko kuma kiɗa—ba za ka yi maganarsa ba ga iyalinka da wasu abokai? Babu shakka. Koyon dukan abin da Jehobah ya yi zai iya shafanmu hakan. Alal misali, Zabura 19:1, 2 sun ce sararin samaniya na “shelar ɗaukakarsa.” Idan mu ma muka yi tunani game da abubuwa masu ban mamaki da Jehobah ya yi, ba za mu iya daina gaya wa mutane game da Allahnmu ba.

8, 9. Don waɗanne dalilai ne Jehobah yake son mu yabe shi?

8 Wani dalili na musamman da ya sa za mu yabi Jehobah shi ne cewa yana son mu yi haka. Me ya sa? Shin domin yana bukatar yabo daga ’yan adam ne? A’a. Muna bukatar yabo wani lokaci, amma Jehobah ya fi mu sosai. (Ishaya 55:8) Ba ya shakkar kansa ko kuma halayensa. (Ishaya 45:5) Duk da haka, yana son mu yabe shi kuma yana farin ciki idan muka yi hakan. Me ya sa? Ga dalilai biyu. Na farko, ya san muna bukatar mu yabe shi. Ya halicce mu da bukata na ruhaniya, bukatar mu yi bauta. (Matiyu 5:3) Jehobah yana farin ciki sosai idan ya ga muna biyan wannan bukata, yadda iyayenku suke farin ciki idan suka ga kana cin abinci mai kyau.—Yahaya 4:34.

9 Na biyu, Jehobah ya san cewa mutane suna bukatar su ji muna yabonsa. Manzo Bulus ya rubuta waɗannan kalmomi ga saurayi Timoti: “Ka kula da kanka da kuma koyarwarka. Ka nace da haka, domin ta yin haka za ka ceci kanka da masu sauraronka.” (1 Timoti 4:16) Hakika, sa’ad da ka koya wa mutane game da Jehobah Allah, kana yabonsa, su ma za su san Jehobah. Irin wannan sani zai iya sa su sami ceto na har abada!—Yahaya 17:3.

10. Me ya sa muke motsawa mu yabi Allahnmu?

10 Har ila da wani dalili na yabon Jehobah. Ka tuna misalin abokinka da ya gwaninta. Idan ka ji wasu suna faɗan ƙarya game da shi, suna ɓata sunansa, ba za ka ƙuduri aniya ka goyi bayansa ba? Ana tsegunta Jehobah ko’ina a wannan duniya. (Yahaya 8:44; Wahayin Yahaya 12:9) Saboda haka waɗanda suke ƙaunarsa sun motsa su faɗi gaskiya game da shi, suna ƙaryata ƙaryar da ake yaɗawa. Za ku so ku nuna ƙaunarku da godiyarku ga Jehobah kuma ku nuna cewa kuna son ya zama Sarkinku maimakon babban magabcinsa Shaiɗan? Za ku yi hakan ta yabon Jehobah. Tambaya ta gaba ita ce, to, ta yaya.

Yadda Wasu Matasa Suka Yabi Jehobah

11. Waɗanne misalan Littafi Mai Tsarki suka nuna cewa yara za su iya yabon Jehobah da kyau?

11 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa sau da yawa matasa suna yabon Jehobah da kyau. Alal misali, da akwai yarinya Ba’isra’iliya da Assuriyawa suka kama bauta. Ta yi wa uwargidanta wa’azi da gaba gaɗi game da Elisha annabin Jehobah. Kalmominta sun sa aka yi mu’ujiza, kuma aka ba da shaida ƙwarai. (2 Sarakuna 5:1-17) Yesu da yake yaro ya yi wa’azi da gaba gaɗi. Cikin dukan abubuwa da ya yi da yake yaro, Jehobah ya zaɓi a rubuta ɗaya kawai cikin Nassosi, wato lokacin da yake ɗan shekara 12, Yesu da gaba gaɗi ya yi wa shugabanan addinai tambaya cikin haikali a Urushalima kuma ya ba su mamaki da yadda ya fahimci hanyoyin Jehobah.—Luka 2:46-49.

12, 13. (a) Menene Yesu ya yi a haikali jim kaɗan kafin mutuwarsa, ta yaya ya shafi mutanen da ke wurin? (b) Yaya Yesu ya ji game da yabo da ’yan yara suka furta?

12 Da ya zama mutum, Yesu ya kuma hure yara su yabi Jehobah. Alal misali, ’yan kwanaki kafin mutuwarsa, Yesu ya ba da lokaci sosai cikin haikali a Urushalima. A wajen ya yi “abubuwan al’ajabi” in ji Littafi Mai Tsarki. Ya kori waɗanda suka mai da wannan wuri mai tsarki kogon ’yan fashi. Ya kuma warkar da makafi da guragu. Duk wanda ke wajen, musamman shugabannan addinai ya kamata su motsa su yabi Jehobah da Ɗansa, Almasihu. Amma, abin baƙin ciki mutane da yawa a wannan zamani ba su furta irin wannan yabo ba. Sun san cewa Allah ne ya aiki Yesu, amma suna jin tsoron shugabannan addinai. Amma da wani rukuni da suka yi magana da gaba gaɗi. Ka san ko su waye ne? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da manyan firistoci da malaman Attaura suka ga abubuwan al’ajabi da [Yesu] ya yi, har yara suna sowa a Haikalin suna cewa, ‘Hosanna ga ɗan Dawuda!’ sai suka ji haushi. Suka ce masa [Yesu], ‘Kana jin abin da waɗannan ke faɗa?’ ”—Matiyu 21:15, 16; Yahaya 12:42.

13 Waɗannan firistocin suna tsammani cewa Yesu zai sa yaran su daina yabonsa. Ya yi hakan kuwa? Ina! Yesu ya amsa ma firistocin: “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa, ‘Kai ne ka shiryar da ’yan yara da masu shan mama su yabe ka’?” Hakika, Yesu da Ubansa sun yi farin ciki da yabon ’yan yaran. Waɗannan yara suna yin dukan abin da ya kamata manyan su yi. A zuciyarsu na yara, dukan abubuwan a bayane suke. Sun ga wannan mutum ya yi abubuwa na ban al’ajabi, ya yi magana da gaba gaɗi da bangaskiya, yana ƙaunar Allah da mutanensa sosai. Da’awarsa cewa shi—“ɗan Dawuda” ne da aka yi alkawarinsa, wato Almasihu gaskiya ne. An albarkace yaran don bangaskiyarsu, da yake suna da gatar cika annabci.—Zabura 8:2.

14. Ta yaya kyauta da matasa suke da shi abubuwa ne masu amfani wajen yabon Allah?

14 Menene za mu iya koya daga irin waɗannan misalai? Yara za su iya yabon Jehobah da kyau. Sau da yawa suna iya fahimtar gaskiya sarai kuma da sauƙi, suna furta bangaskiyarsu da ƙwazo da himma. Suna da kyauta da aka ambata a Karin Magana 20:29: “Ƙarfin samari abin darajantawa ne.” Hakika, matasa suna da ƙarfi da kuzari—abubuwa masu amfani wajen yabon Jehobah. Ta yaya za ku yi amfani da wannan kyauta da kyau?

Ta Yaya Za Ku Yabi Jehobah?

15. Don ka yabi Jehobah da kyau, wane muradi ake bukata?

15 Yabo mai ba da ’ya’ya na somawa daga zuciya. Ba za ka iya yabon Jehobah da kyau ba idan kana yi ne domin wasu suna son ka yi hakan. Ka tuna cewa, umurni da ya fi shi ne wannan: “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.” (Matiyu 22:37) Ka san Jehobah ta wurin nazarin Kalmarsa da kanka? Sakamakon wannan shi ne za ka ƙaunaci Jehobah. Hanyar da ta dace na nuna wannan ƙauna ita ce ta yabonsa. Idan muradinka mai kyau ne za ka kasance a shirye ka yabi Jehobah sosai.

16, 17. Ta yaya hali yake taimako wajen yabon Jehobah? Ka ba da misali.

16 Kafin ka yi tunanin abin da za ka faɗa, ka yi tunanin yadda za ka aikata. Idan wannan yarinya Ba’isra’iliya ta zamanin Elisha mai reni ce, marar ladabi, ko kuma ba ta faɗan gaskiya, ca kuke Suriyawa da suka kama ta za su saurari abin da ta ce game da annabin Jehobah? Wataƙila ba za su saurara ba. Hakanan ma, mutane za su fi sauraronka idan suka ga kai mai ladabi ne, kana faɗan gaskiya, kuma halinka mai kyau ne. (Romawa 2:21) Ga misali.

17 Wata yarinya ’yar shekara 11 a Fatugal ta fuskanci tsanantawa a makaranta ta yi bukukuwa da suka taka lamirinta da aka koyar da Littafi Mai Tsarki. Ta bayyana wa malamarta cikin ladabi abin da ya sa ba za ta yi ba, amma malamar ta yi mata ba’a. Da shigewar lokaci malamar ta yi ƙoƙari sau da yawa ta kunyatar da ita, tana yi wa addininta ba’a. Amma, yarinyar ta ci gaba da yi mata ladabi. Wasu shekaru bayan haka, wannan matashiya tana hidimar majagaba ta kullum. A wani taron gunduma, tana kallon waɗanda suke baftisma sai ta gane ɗaya cikinsu. Malamarta ce ta dā! Bayan sun rungumi juna cikin farin ciki, wannan matar ta gaya wa matashiyar ba ta manta da halinta na kirki ba. Wata Mashaidiya ta sadu da ita, kuma malamar ta yi magana game da halin ɗalibarta ta dā. Ta haka, aka soma nazarin Littafi Mai Tsarki da ita, kuma wannan matar ta amince da gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Hakika, halinka zai zama hanya mai kyau na yabon Jehobah!

18. Menene matashi zai iya yi idan yana iske shi da wuya ya soma taɗi game da Littafi Mai Tsarki da kuma Jehobah Allah?

18 Kana iske shi da wuya wani lokaci ka soma taɗi game da imaninka a makaranta? Ba kai kaɗai ba ne ke jin hakan. Amma za ka iya shirya yanayi da wasu za su yi maka tambaya game da imaninka. Alal misali, idan bisa doka ya dace kuma ana hakan, ka kai littattafai da ke bisa Littafi Mai Tsarki makaranta kana karantawa lokacin cin abinci na rana ko wani lokacin da aka yarda a yi hakan. Abokan makaranta za su iya tambayarka abin da kake karantawa. Ta wajen amsa musu da kuma gaya musu abin da ka ji daɗin karantawa a talifin ko kuma a littafin da ke hannunka, za ka ga cewa kun soma taɗi. Ka tuna ka yi tambayoyi don ka san abin da abokanka na makaranta suka yi imani a kai. Ka saurara da kyau, kuma ka gaya musu abin da ka koya daga Littafi Mai Tsarki. Wannan yana sa su farin ciki kuma yana taimakon mutane da yawa su san Jehobah.

19. Ta yaya matasa za su daɗa kyautata hidimarsu ta kofa kofa?

19 Hidimar kofa kofa ce hanya mafi kyau na yabon Jehobah. Idan ba ka soma yin wa’azi ba, me ya sa ba za ka kafa wannan makasudi ba? Idan kana yin hidima, da ƙarin makasudai da za ka kafa wa kanka. Alal misali, maimakon kana faɗan abu ɗaya a kowace kofa, ka nemi hanyoyi ka kyautata hidimarka, ka tambayi iyayenka da wasu ’yan’uwa da suka ƙware shawarwari masu kyau. Ka koyi yadda za ka fi amfani da Littafi Mai Tsarki, yadda ake komawa ziyara da zai ba da ’ya’ya, ko kuma yadda ake soma nazarin Littafi Mai Tsarki. (1 Timoti 4:15) Idan kana yabon Jehobah hakan, za ka kyautata hidimarka kuma za ka ƙara jin daɗinta.

Yaushe ya Kamata Ku Soma Yabon Jehobah?

20. Me ya sa bai kamata matasa su ji sun yi ƙanƙanta ainun wajen yabon Jehobah ba?

20 Cikin tambayoyi uku da ke cikin wannan talifin, wannan na ƙarshen ne ya fi sauƙi. Ka lura da amsar Littafi Mai Tsarki na kai tsaye: “Ka tuna da Mahaliccinka a kwanakin samartakarka.” (Mai Hadishi 12:1) Hakika, yanzu ne lokacin da za ka soma yabon Jehobah. Babu wuya za ka ce: “Ni yaro ne ba zan iya yabon Jehobah ba. Ban san kome ba. Zan jira sai na yi girma.” Ba kai ba ne na farko da ya ji hakan. Alal misali, Irmiya sa’ad da yake matashi ya gaya wa Jehobah: “Ya Ubangiji Allah! Ban san abin da zan faɗa ba, gama ni yaro ne.” Jehobah ya tabbatar masa cewa kada ya ji tsoro. (Irmiya 1:6, 7) Hakanan ma, ba mu da dalilin jin tsoro sa’ad da muke yabon Jehobah. Ba abin da zai same mu da Jehobah ba zai iya kawar da shi ba.—Zabura 118:6.

21, 22. Me ya sa aka kamanta matasa masu yabon Jehobah da raɓa, me ya sa wannan kwatanci da ban ƙarfafa?

21 Muna ariritarku matasa: Kada ku yi jinkirin yabon Jehobah! Yanzu da kuke matasa ne lokacin da ya fi kyau da za ku yi aiki mafi muhimmanci da ake yi a duniya a yau. Idan ku ka yi hakan, za ku kasance cikin abu mai ban al’ajabi, wato iyalin waɗanda suke yabon Jehobah. Jehobah yana farin ciki cewa kuna cikin wannan iyalin. Ku lura da wannan hurarrun kalmomi da mai zabura ya furta ga Jehobah: “A ranar da za ka yi yaƙi da maƙiyanka, jama’arka za su kawo maka gudunmawa don kansu. Kamar yadda raɓa take da sassafe, haka samarinka za su zo wurinka a tsarkakan tsaunuka.”—Zabura 110:3.

22 Raɓa da ke ƙyalli da safe na sa wuri ya yi kyau, ko ba haka ba? Suna da ban wartsakewa, suna walƙiya, kuma sun fi gaban ƙirgawa. Haka ne Jehobah yake ɗaukan ku matasa da kuke yabonsa a waɗannan kwanaki masu wuya ƙwarai. Hakika, Jehobah yana farin ciki idan kuka zaɓi ku yabe shi. (Karin Magana 27:11) Saboda haka, matasa, ku yi iyakar ƙoƙarinku ku yabi Jehobah!

Yaya Za Ka Amsa?

• Don waɗanne dalilai masu muhimmanci za mu yabi Jehobah?

• Waɗanne misalai na Littafi Mai Tsarki suka nuna cewa matasa za su iya yabon Jehobah da kyau?

• Ta yaya matasa za su iya yabon Jehobah a yau?

• Yaushe ya kamata matasa su soma yabon Jehobah, kuma me ya sa?

[Hotuna a shafi na 15]

Idan abokinka yana da gwani ne na musamman, ba za ka gaya wa mutane game da shi ba?

[Hoto a shafi na 17]

Abokan makaranta za su so su san imaninka

[Hoto a shafi na 18]

Idan kana son ka kyautata hidimarka, ka tambayi Mashaidi da ya ƙware don shawarwari masu kyau

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba