WAƘA TA 75
‘Ga Ni! Ka Aike Ni’
(Ishaya 6:8)
- 1. A yau yawancin mutane - Suna ɓata sunan Allah. - Wasu sun ce Shi mugu ne, - Wasu sun musunci Allah! - Wa zai je ya gaya masu? - Wa zai yabi sunan Allah? - (AMSHI NA 1) - ‘Ya Allah, aike ni! Zan je! - Zan yabi sunanka sosai. - Gata mafi girma ce Allah. - Ga ni, aike ni! Zan je!’ 
- 2. Sun ce Allah na jinkiri - Kuma ba su tsoron Allah. - Suna bauta wa gumaka, - Sun mai da Kaisar Allahnsu. - Wa zai gargaɗi mugaye - Don Armageddon ya kusa? - (AMSHI NA 2) - ‘Ya Allah, aike ni! Zan je! - Zan yi shela babu tsoro. - Gata mafi girma ce Allah. - Ga ni, aike ni! Zan je!’ 
- 3. Masu adalci na kuka - Domin mugunta ta ƙaru. - Suna ta neman gaskiya - Da za ta kwantar da ransu. - Wa zai je ya ƙarfafa su - Domin su bauta wa Allah? - (AMSHI NA 3) - ‘Ya Allah, aike ni! Zan je! - Zan koya musu Kalmarka. - Gata mafi girma ce Allah. - Ga ni, aike ni! Zan je!’ 
(Ka kuma duba Zab. 10:4; Ezek. 9:4.)