WAƘA TA 122
Mu Tsaya Daram, Babu Tsoro!
Hoto
1. Mutane suna wahala sosai,
Suna tsoron abin da zai faru.
Mu yi gaba gaɗi, babu tsoro,
Mu bauta wa Jehobah.
(AMSHI)
Mu riƙa dagewa fa,
Mu ƙi halin duniya.
Mu riƙe aminci
Don mu sami ceto.
2. Shaiɗan na jarraba mu koyaushe,
Amma ba za mu shiga tarkon ba.
In muna yin ayyukan nagarta,
Za mu yi ƙarfin hali.
(AMSHI)
Mu riƙa dagewa fa,
Mu ƙi halin duniya.
Mu riƙe aminci
Don mu sami ceto.
3. Mu riƙa bauta wa Maɗaukaki.
Mu riƙa yin wa’azi koyaushe.
Mu yi shi ban da tsoron mutane,
Mulkin Allah ya kusa.
(AMSHI)
Mu riƙa dagewa fa,
Mu ƙi halin duniya.
Mu riƙe aminci
Don mu sami ceto.
(Ka kuma duba Luk. 21:9; 1 Bit. 4:7.)